DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu0️⃣4️⃣
Lameen kam yana shiga ya tadda su falon mahaifin su suna kallon wani american film yayi wajen Hajiya Asiya yana wani shagwab'ewa yace "Mamana shine baki neme niba?"Alhaji Khamis ya maqale dariyar sa yana kallon sa yace "God'od'o dakai kai ko kunya baka ji ba kace ta neme ka kaida zaka zo ka gaishe ta kamar yanda Muhammadu yayi ya nemi albarka kai saidai taje ta neme ka?"
Lameen yayi saurin kallon saitin Hajiya Asiya da take murmushi ya sauke b'oyayyiyar ajiyar zuciya kuma ya fahimci yayi sakarci amma duk da haka sai ya wani sake shagwab'ewa wannan karon harda kwantar da kansa kan cinyarta yana cewa "Mummy Kinga Abeey ko?tunda muka taho suke min abubuwa shida Mooha kiyi musu fad'a."
A wasance ta kalli Abeey d'in tace "Aa shiyasa mana ban ganshi ba na kuma tambaya aka qi gaya min gaskiya to nifa gaskiya a daina tab'a min lele na gaskiya."
Murmushi yayi yace "Uhm Su lele anji jiki yaya goto kenan."
Haka dai ya cigaba da tsokanar sa mummyn na tare masa har ya saki ransa kuma ya dawo ana hira sosai saida aka sake sako zancen auren Immileey sannan ya miqe yana jin wani iri yace "Na manta nacewa Jaan ta jira ni muje shan ice cream Allah yasa batayi fushi ba na tafi."
Ya tafi da gudun sa suka bishi da ido suna dariya.
Yana fita ya tadda ta baiwar Allah tana ta kallo yana fitowa ta miqe da sauri tana dariya tace "Jaan L muje na matsu inje."
Shafa kanta yayi yace "Muje Jaan A am sorry i kept u waiting."
"Its Okay." Ta fada tana yin gaba bata wani damu ba.
Haka suka fice sukaje wajen shan ice cream din ya siya musu sannan suka wuce wani d'an qaramin Super market ya kwaso mata kayan lashe lashe suka fito.
****
Biki ya rage sauran watan guda don haka Goggo Lari ta tattara ta ta kaita dangin ta inda zasu yi mata gyaran da akewa amaren fulani na sati biyu.Aiko tasha shi tasha madara da wankanta kamar ba gobe fatar nan kan cikar sati biyu tayi wani irin kyau ga sulb'i da qyalli da takeyi ita kanta har mamaki take yanda tayi kyau sosai.
Satin ta biyu ta dawo gida aka cigaba da shirin biki sosai ita da qawayen ta sannan shima Angon bangaren sa da abokanan sa.
Tun sauran sati Alh Khamis da Iyalansa inka cire Lameen da yaqi zuwa yace wai yana da abun yi ana gobe d'aurin auren zai je.
Mooha da Amnah kamar sunfi kowa farin cikin zuwan Jannah ce dai baza ka iya hasashen yanayin da take ciki ba lokaci guda.
Gidan su suka soma sauka sai yamma sannan Haj Asiya da Amnah suka ce zasuje gidan su amaryar Haj Asiya ta kalli Jannah tace "Zakije ko mu tafi."
Takai wajen 30secs kafin tace da qyar "Zanje."
Tsaki Haj Asiya tayi tace "Wallahi indai wannan halin zaki d'auka kece a wahale aikin banza kawai kina mace da zaki auri wani kike wannan isar banzar data wofi to ko shi da yake namiji ba riba zaici ba balle ke shashashar banza."
Tayi gaba abinta Amnah na riqe da hangbag d'inta ta bi bayanta itama Jannah tabi bayansu tana ta cin rai kamar wadda aka wa dukan tsiya.
Suna tafe suna kalle kalle duk da irin quncin da takeyi sai da taji garin yayi masifar burgeta nan da nan ba tare data sani bama ta soma sakin ranta har tana nunawa Amnah wasu abubuwa.
A qofar gidan suka ci karo da Rabi da Atika da Ladingo da Fad'ima qawayen Immileey zasu shiga gidan suma,Jannah ta bisu da kallon sha'awa duk d'in su basu sa'annin taba a tsakar gida suka tadda su Goggo Lari da qannen ta biyu suna ta kad'in man shanu suna ta fesa fulatancin nan da nan Haj Asiya dake tsatson su ce ita ma anan Gogel d'in take har aka mata aure ta shige cikin su kad'in ma bata manta yanda ake ba saidai yanzu baza ta iya da yawa ba kamar da saboda hutu da jin dad'i daya ratsa ta (Nidai nace tama yi qoqari data tuna din.)
Amnah data ga su Immileey zasu fita ta bisu da gudu tace "Khadija nima nazo mu tafi?"
Immileey ta juyo tana dariya don bata lura dasu ba tace "Taho mana ai ban gan ki bane?"
Amnah tace "Bari naje na tambayi Mummy inta barni."
Da sauri Immileey tace "Muje to in gaishe ta nima."
Tabi ta a baya taje ta gaishe da Haj Asiya kuma a sannan taga Jannah tace mata "Kema kizo muje to."
Jannah bisa ga mamakin Amnah da Mummy sai suka ga ta miqe tace "Muje."
Haka suka musu sallama suka fice suna ta hirar data shafe su suna ta shirme abin su amma a tunanin su hirace ta manya ta hankali.
Mummy ma haka suka yi ta hirar Yaushe gamo da Goggo Lari daga qarshe ma d'aki suka qule suka cigaba don dama tun suna yara aminai ne suma aure ne ya raba su don shi Khamis yana kano shiko Hafizu a Gogel yake.
A bangaren su Immileey zancen bikin suke da irin al'adun da ake a bukukuwa suma suna lissafa irin abubuwan da zasuyi.
Sosai Jannah ta sake cikin su ta zage ana ta lissafawa da ita don har ma tafi Amnah zagewa harda yiwa Immileey kwalliya irin ta binni da taga emmata sunayi tunda su ba yi suke ba sosai.
Aiko su Fad'ima suka dinga kod'a irin kyan da tayi har suna roqon ta ta koya musu don in an tashi bikin wata a cikin su ko su zasu bikin suyi irinta.
Jannah cike da jin dad'in yanda suke yaba mata tace duka zata koya musu amma sai bayan an gama biki saboda yanzun basa zama dukkan su suka amince da hakan.
ZahraArkel ce!🥰