DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu0️⃣5️⃣
Satin bikin tun laraba suka soma bukukuwan su irin na fulani da wasanni harda su shad'i da Ajo don su basu yadda al'ada duk qanqantar ta shiyasa bikin ba qaramin burge su Jannah yayi ba musamman Amnah da ita a Ipad taita daukan bikin saboda kada ta bari wannan abubuwan su wuce ta.An gama biki lafiya aka d'aura aure ran lahadi bisa ga shawarar Alh Khamis saboda ya gayyaci abokanan sa yako san duk sai weekends suke da lokaci don haka dole sai weekend d'in za a saka.
Ranar aka kai ta da daddare duk cikin Gogel d'inne babu nisa tsakanin ta da gida in a babur ko mota zakaje amma in a qafa ne da er tazara don wata rigar ce daban tasu Turajon.
A ranar tayo gudu washegari aka maida ta shikenan biki ya qare,duk da haka su Jannah suna tare da su Fad'ima shiyasa sam basu ji garin ya ishe su ba.
Haka Mooha shi gabad'aya ma ba a ganin sa sai ta kama sun zo cin abinci ko neman wani abun a rutsa shi,daji suke shigewa da shanu wai sun tafi kiwo zakaji mamakin yanda Mooha ke sarrafa su kamar nasa duk sun saba dashi shanun basu masa tutsu ko gardama.
Lameen ne dai duk garin ya gundura don ana gobe d'aurin auren Alh Khamis yaga da gaske baida niyyar zuwa ya kira shi a waya yace wallahi ya bari aka yi d'aurin auren nan gobe babu shi a wajen zai sha mamakin abinda zai masa kuma wallahi sai yayi shekara a Gogel.
Aiko hankalin sa ya tashi don yasan mahaifin sa ba qaramin aikin sa bane ya cika abinda ya fad'a don haka a dole ya tattara a ranar ya tafi a niyyar sa kwana biyu zaiyi ya dawo saidai yana zuwa Alh Khamis yace ba inda zashi har sai zasu koma ai ko abun ya qona masa rai ba kad'an ba ya qaraci quncin sa ya haqura don ko Mummyn tasa wannan karon bata goyi bayansa ba.
Yana zaune da daddare yana danne danne a system d'insa yana had'a wasu documents na takardunsa,yanayin shirun da garin yayi da irin waqe waqen da yan matan keta yi a dandali ne ya soma d'an jansa a hankali ya rufe system d'in ya miqe ya zura wayar sa a aljihu ya fice.
Inda sautin ke fitowa ya tsinci kansa da bi a hankali har ya isa wajen ya zauna can gefe da su yana kallon yanda wajen yake tarwal kamar rana ba kamar wancen zuwan nasu ba da babu wannan qwayayen kuma babu wutar lantarki abun ya bashi mamaki.
Kowa abinda ke gabansa yake yi wasu zance suke da emmatan su wasu na gad'a da waqe waqen su wasu na saye da siyarwar su abun dai gwanin sha'awa.
Ya shagala sosai da kallon su yaji an watsa masa qasa a qafa a fusace ya d'aga kai yana kallon ta gabad'aya ta dibibice tayi barin gyad'ar da take saidawa gashi ta watsa masa qasa da fulatanci ta ke maimaita "Don Allah kayi haquri don Allah kayi haquri." Iyakacin abinda take iya fad'a kenan jikinta nata rawa.
Ya bud'e baki zaiyi masifa sai ga su Amnah da sauri ta isa wajen ta tana ce mata "Fad'ima b'ari kikayi fad'uwa kikayi?meya sameki?"
Ganin gabad'aya hankalin Fad'imar yana kan sa yasa ta juya tana kallon sa da mamaki tace "Lahhh Jaan L kaine ashe?fad'uwa tayi?kaga qawata ce fa sunanta Fad'ima." Ta fad'a tana jan hannun Fad'iman zuwa inda yake.
Itako dake duk a tsorace take da yanda taga ya d'aure sai tayi saurin janye hannun ta tana cewa "Na b'ata masa qafarsa."
Amnah ta kalli qafar tayi dariya tace "To ki bashi haquri zai haqura ai."
Da sauri yace "Ba sai ta bani ba qyale ta tunda qawar kice." Yana gama maganar ya juya da saurin daya bata mamaki.
Da kallo duk suka bishi Fad'ima ta sauke boyayyiyar ajiyar zuciya suka taya ta suka tsince b'arin da tayi suka tafi.
Shi ko gida ya wuce yana jin wani irin b'acin rai kamar ya cire qafar don tsabar takaici a fili yake mita "Mutane sai kace dabbobi shiyasa bazan tab'a son wad'annan gidadawan mutanen ba."
Amnah ta kalli Fad'ima suna tafiya tace "Yayana ne shine babban mu."
Fad'ima da har yanzun a tsorace take tace "Allah sarki ni nayi zaton Hamma Mooha ne kawai yayan ku."
Ta girgiza kai tace "Aa shine babba sai Hamma Mooha sai Sis Jannah saini."
Murmushi tayi tace "Kece Auta kenan."
Ta gyad'a kai cikin jin dadi tace "Eh."
Fad'ima itama ta gyad'a kai tace "Kinji dadi."
Daidai nan suka kawo qofar gidan inna Amina don haka sukayi sallama kowanne ya tafi gida sai kuma da safe.
ZahraArkel ce!🥰