Part 7

320 26 0
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu



0️⃣7️⃣
Zaman gidan miji yayiwa Immileey dadi ba kad'an ba,don iyaka iyawa surukanta basu rage ta da komai ba suna sonta sosai dake itama ta samu tarbiyya mai kyau tana musu biyayya yanda takewa su Innar ta shiyasa zaman nasu gwanin sha'awa.

Tun sassafe take fitowa ta share tsakar gidan tsaf dake sashen kowa daban ita nata dana surukanta ne don haka ba wanda zai ganta shiyasa ma ta zab'i fitowar sassafen amma bisa ga al'adar su amarya sai tayi shekara bata karb'i aikin gida ba.

Ita Immileey dama can bame son jiki bace tana son ayyuka irin na gida Goggo lari ta sabar mata sosai don haka tana yi kwana uku taji baza ta iya ba.

A ran na hud'u Innah Yafendo kamar yanda yaran ta ke kiranta sai ganin ta tayi ta gama shara,ta hauta da fad'an meyasa tayi ta dinga bata haquri cike da girmamawa da kunya don ita kanta tasan al'adar su ba a bari amarya tayi ayyukan gida wasu har sai ta haihu ko zata shekara goma bata haihu ba.

Ga b'angaren Turajo,sam baya nuna jin kunya akan soyayyar da yake mata bai qi ba ko gaban waye ya mata wasa da magana.

Duk da yanda matar fari ake jin kunyar ta haka nan mijin fari ba kasafai ma ake ganin shigar su d'aki a tare ba shi sam bai d'auka ba daman yasha fad'a shifa gaskiya baya son wannan d'abi'ar kuma bai ga wanda ya isa ya sashi yin ta ba,don haka yasha yazo ya tarar da Immileey da Innar sa sai kawai kaga yana kiran ta ko yana mata signal idan Yafendo taga haka sai ta miqe ta bar wajen haka matan gidan zasu taru suyi ta masa tsiya amma bakin sa sam baya mutuwa.

A haka matar kawun sa Ladingo ta tab'a tare Immileey kusan watanni biyu bayan auren ta tana tsince alkama Turajo ya kira ta taje bayan ta dawo tace da ita "Ke Immileey ki kiyayi bin namiji ku kenan bini bini kuna d'aka?me kuke yi?mu a zamanin mu kam yaushe ma zaka yarda ka had'a makwanci da namiji."

A'ilo da ke qarasowa tace "Madallah Ladingo kamar kin shiga zuciya ta wallahi, yarinyar nan kiyi zaqewa namiji da yace zo ki wani tashi zungwi zungwi ba ko kunyar idon Yafendo ki tafi kuma ba kunya ki sake dawo mana wataran kina gyara zani."

Immileey ta zazzaro ido ta dire farantin da take tsince alkamar tace cikin rawar murya "Wallahi duk sanda ya kirani aiki yake sani..."

Kan ta qarasa A'ilo tace "Qarya kike yanzu zaiyi wahala ma in aka duba ki baki samu ciki ba zaki mana qarya mu ne zaki mayar yara qananu yarinyar da mun riga mun sani tun washegarin gudu kika san namiji."

Immileey ta fashe da kuka tana shirin miqewa Ladingo tace "Kije ki dauki cikin kwankwason ki bai gama qwari ba kije ki nakasa ya auro wata kuma..."

Turajo ne ya cafe zancen cikin yin qasa da murya yanda ya tabbatar su kad'ai ne zasu ji yace "Ya ishe ku gaskiya ina sane daku ba tun yau ba kuke sa mana ido amma in tambaye ku dukkan ku wad'annan 'ya 'yan da kuke da su duk a ruwa kuka sha cikkunan su kome?ko ke Ladingo sanda aka kawo ki daga rigar ku kin kai Immileey ne?karfa kiga shekaru basu yawa lokacin nasan shekarar ki guda kika haifo Tasi'u bayan kinyi b'ari,kinga kenan idan abun kunya ne kece kika farayi Immileey dake tai koyi."

Ya juya wajen A'ilo yace "Ke kuma A'i kina buqatar na tuna miki kema abinda ya faru je?"

Da sauri A'ilo tace "Aa Allah baka haquri bari in tafi."

Ya girgiza kansa "Aa basai kin tafi ba ki tsaya amma ina mai sanar daku cewa duk wanda ya qara takura min mata ko ya samana ido wallahi bazai ji dad'i ba,don babu wata al'ada da ta isa ta hanani rufe ido naiwa duk wanda ya tab'a min mata rashin mutunci."

Ladingo dai bata samu damar tofa komai ba ta miqe ta gudu,A'ilo ma ba shiri ta bar wajen tana magana qasa qasa "To daga gyara kayan ka kuma sai tone tone taje taita yi Allah ya taimaka ta haifo goma ka a wata guda."

Ladingo ko maganar Turajo ba qaramin dukan ta tayi ba da a tunanin ta basu san komai ba tunda suna qanana ne komai ya faru ashe suna sane to kam ta daina shiga sabgar gidajen su kafin a samu mai qwaqwalo abinda aka dade da mantawa.

Ya kalle ta yace "Tashi ki tafi d'aki."

Ta miqe jiki ba qwari tana share hawaye ta wuce saida ta zauna bakin gadon ta na qarfe ta sake fashewa da kuka don ba abinda yafi tsaya mata irin wai tana bin namiji kuma wai kwankwason ta bai gama qwari ba,to mutanen da dana yanzu ba d'aya bane suke nufi kome?don Innar ta tasha fad'a mata cewa ita bata ma kaita ba aka mata aure kuma bata fi shekaru uku ba ta haifo d'anta na fari.

To kodai nata ne sukaga baida qwarin suke guje mata kada ta nakasa ko ta mutu?ta tuno qawar su Halime da ta rasu wancen shekarar ta tuna a lokacin tazo haihuwa ne kuma mutane da yawa suna cewa wai qwanqwason ta ne baiyi qwari ba shiyasa d'an ya maqala harta rasu abun fa gabad'aya ya dagule mata.

A haka Turajo ya same ta tana ta gursheqen kuka,ya kalle ta yana dariya yace "Ke kam anyi sokuwa Immileey yanzu nan kukan wannan maganar tasu kike yi har yanzu?to bari kiji na fad'a miki ita Ladingo asali d'iyar ta Jummai taso na aura naqi nace sai ke shine take son tsorata ki."

Murya na rawa tace "To kuma Halime data rasu wancen shekarar fa aka dinga fad'in abinda suka fad'a ni bana son na mutu."

Dariya yayi yace "Ba abinda zai same ki in sha Allahu sai alkhairi Ki kwantar da hankalin ki tunda bama wanda yace kina da ciki balle hankalin ki ya tashi idan kin samu ma Allah yasa mai albarka ne."

Ta jinjina kai a kunyace tana mamakin Turajon ta,duk da tasan yana shiga binne sosai amma sai taga wayewar sa da yawa,mutum ne mai fahimtar rayuwa da duk wanda yake tare dashi ga wayewa ko a yanayin shigar sa,shiga sa sauda dama idan ana zancen miji a tsakanin qawayen ta tun suna saurayi da budurwa qawayen kan ce mata "Ke kam Immileey ki godewa Allah kinyi miji na kere sa'a kowaccen mu nan ba wadda ta more kamar ke."

A lokacin saidai tayi murmushi kawai sai yanzu take fahimtar da gaske ne tayi miji na nunawa sa'a na fita kunya tun kuwa daga kan lefen ta."

Gaskiya nayi nayi in qara daga haka amma na gaji ayi manage da wannan kafin page na gaba.

ZahraArkel ce!🥰

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now