*°🔘°KILALLU°🔘°*
_{K'alubale gare ku y'an mata}_
*1441H/2020M.*
*JUMADAII/JAN.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*DR FAYEEX M. USMAN✍🏼*~VOTE&FOLLOW 4Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*Alhamdulillah!!!* *alhamdulillah!!!* *alhamdulillah!!!*
*Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijina buwayi gagara musali maiji* *maigani mak'agin sammai da k'assae Mai mulki ranar sakamako mahaliccina gareka nake mik'o godiya ta**Ya Ubangiji na Allah kayi salati da Sallama ga annabi MUHAMMAD S.AW da sahabbanshi da iyalinshi da Wanda sukai Imani da shi har izuwa ranar sakamako*
'''Tooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske''' '''Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka.
Inafata Ubangijina yabani ikon kammala''' '''wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.'''~Kusani comment d'inku shine k'warin gwiywata,Ina fatan labarina ya shigeku tare da ratsaku musamman Y'an uwa mata Allah yasa mufi k'arfin zuciyarmu Ameeen~
*SHAFI NA 1📑**__________📖* Sansanin yan kin arewa wato b'angaren mu kenan, Babu San Kai a magana ta Yan kine Wanda muke rik'o da Addini tare da k'ok'arin naiman ilimin Addini, to a yanzu dai Nigeria ta d'aya daga cikin k'asashen da suka samu ci baya matuk'a, Kuma Allah shaida ne waje da lugun k'asar akan rik'o da Addini da dokokin Allah muke , duba da yacce mukasa neman ilimi yazama gaba a rayuwar mu, to ko mai yasa k'asar mu rashin ci gaban??,to komadai me ne-ne da Allah muka dogara Kuma bazamu tab'a daina Alfahari da k'asar muba,Kuma muna addu'ar nai man sauk'i da agajin Ubangijinmu....
.... Wata matashiyar budurwace , a k'alla shekarun ta zasuyi shatara,tana da kyau mai sanyi, domin farace doguwa mai matsakaicin jiki ita ba lukutaba ita ba siririyaba a tak'aice Zan iya kiranta da San kowa k'in Wanda yarasa.Sanye take cikin dogon hijjab d'inta kalar fari Wanda har k'asa yake ja tsabar tsayinshi da Kuma girmanshi.
Hannunta rungume da littafin *BULUGUL* *MARAM*, da *SAHIHI MUSLIM* , da alama daga makaran ta take.
Kanta sunkuye Dan ko kusa Bata iya d'aga kanta gudun had'a ido da wani Dan wannan babban al'amarine gareta.
Gab take da k'arasawa gidan da zata daga bayanta taji yace.
" Umaima."... ya kirata cikin sanyin muryarshi.
Harzata shareshi sai Kuma taga rashin da cewar hakan, domin tasan Imam Babu kalar cizgi da wahalar da Bata bashiba , Amma kullum acikin bibiyarta yake, batako tsayawa ta saurareshi balle tanuna tasan da zamanshi, Amma ko kusa Imam baya gajiya danuna kulawarshi gareta hakan yasa taji nauyin shareshi Kuma a yaune tafara jin wannan yanayin.
Ganin Umaima ta tsaya sanadin kiranta ba k'aramin sanyaya ran Imam yayi ba domin koba a fad'a ba yaci wahala kafin samuwar haka, Dan idan ba b'atan lissafi yayi ba yau wata Tara da had'uwarsu,kusan kullum saiyaje gareta Kuma sai yayi Mata tallan soyayyarshi Amma Ina kamar anayiwa dala dun-dun ne.
Hakan yasa baiyi k'asa a gwiywa ba, ya k'arasa kusa da ita zuciyarshi na harbo mai, k'amshin nasara, idonshi fal k'walla yace.
" Umem menayi maki ne, maye Abin gudu a gareni , wanne aibu nakeda?,shin masoyinka zaizamo mak'iyin kane Umem?, Ko banza kalmar so nafurta agareki ya kamata nasamu wani kasho mai kyau,kalmar da bakiso Umem bazan tab'a daina fad'a maki itaba cewa inasonki so mai mugun k'arfin gaske Umem, soyayyar ita tazamo abincin cina tare da shana,kullum a tunaninki ki daure kana kijure Umem kibani Dama komai k'an-k'an tarta Umem wllhy bazakiyi Dana saniba domin Imam sanki yake so Kuma na gaskiya."... Shirun da yayi na nuna alamun gazawa tare da nuna yacce sonta yake cimai zuciya dare da Rana duba da yacce yasa hannu a santar zuciyarshi tare da cije lab'b'anshi.
YOU ARE READING
KILALLU. {Completed 04/2020.}
ActionTooooooooooo shidai wannan labari nawa ya farune a gaske Kuma lamarine Wanda yake faruwa a wannan rayuwa tamu mai Albarka. Inafata Ubangijina yabani ikon kammala wannan labari nawa lafiya, labari mai cike da darrusa mararsa iyaka.