DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu0️⃣9️⃣
Tunda asuba da suka had'u da Abeey d'in nasu a masallaci ya gaya masa yau zai tafi Abuja akwai abinda yake son yi na business d'in da yake yi amma bazai dad'e ba baifi yayi sati ba.Abeey d'in ya kalle shi yace "Ya admission d'in fa?"
Yace "Na makara saidai next year zanyi managing na cigaba da business d'ina kafin lokacin."
Shima yace "Ok amma dai tunda baka tafi ba sai ka nemo mata kayi aure tunda abun yazo a haka."
Kai kawai ya jinjina ya wuce yana mamakin iyayen sa duka duka fa ashirin da biyar yake yanzu amma sun bi sun damu kansu da wai sai yayi aure,shikam bai shiryawa wani aure yanzu ba kuma bazai yi ba kawai zai cigaba da amsa musu har lokacin da zai tafi ba kuma zai dawo ba sai ya gama kafin lokacin ya kusan talatin to sannan yasan ya shiryawa auren.
Yana shiga d'akin su ya tattara ragowar abinda bai had'a ba yayi wanka ya je yayi sallama da su Haj Asiya ya d'auki hanyar abuja yana jin kamar ya sauke wani nauyi a kansa ne.
✨✨✨
Safiyar litinin Turajo ya tashi da wani irin ciwon ciki Immileey duk ta rud'e tun suna yi su kad'ai a d'aki taga ya soma mimmiqewa ta fice da gudu tana kuka ta kira Yafendo,a tare suka dawo saidai tana kallon shi ta janye Immileey suka fito.Ta kalli Yafendo tace "Innah bacci yayi ne naga ya daina motsi."
Gyad'a mata kai kawai tayi tace tana tura ta d'akin ta "Shiga ki zauna kada kije ki tashe shi da kusur kusur baya son damu in yana bacci."
Kai ta gyad'a tana kallon fuskar Yafendo tana nazarinta ta dai lura taqi had'a ido da ita kuma kamar tana danne tashin hankalin da ke kwance kan fuskar ta.
Yafendo tayi saurin fita,b'angaren babban d'an gidan tayi tana kiran sa.
Ya fito daga d'aki yana cewa "Yafendo barka da safiya."
Da sauri ta ruqo hannun sa ba tare da tayi magana ba ta jashi d'akin su Immileey cikin rad'a tace "Duba shi Datti kamar fa bashi da rai."
A tsaye da yake ya soma maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un."
Ya juya ya kalli Yafendo ya sake kallon Turajo dake kwance samb'al dashi,yace cikin rad'ar shima "Saidai haquri Yafendo amma Turajo ya tafi."
Saurin toshe bakin ta tayi ta zauna zaman dirshen a wajen,hankalin ta in yayi million a wannan lokacin ya tashi,tunanin ta yama za ayi ne a fad'awa Immileey ta fahimta yarinya qarama zawarci ya same ta da qarancin shekaru.
Hirji kawai da hailala take maimaitawa ,Datti ya tsuguna gabanta yana d'an bubbuga kafad'ar ta sannan a hankali yace "Ya kamata a sanar dasu baba azo ai masa suttura tunda safiya ce za a kaishi da wuri."
Ta jinjina kai tana kallon yaron ta samb'al dashi a kwance hawaye sai bin kumatun ta suke tausayin Immileey da abinda yake cikin ta duk ya dame ta.
Datti ya fice yaje ya taso kawunnan sa da iyayen sa duk suka firfito,a hankali aka dinga komai,ita Immileey dake d'aki kawai sai ta tsinci kanta da mummunar fad'uwar gaba a kai akai ta dinga dubawa taga ko Yafendo ta dawo amma sai taga bata dawo ba,qarshe ne ta lura da kawunnan su Turajo suna fitowa d'aya bayan d'aya don haka ta tsaya tana kallon su ba a jima ba sai ga Baffa Adaamu da Liman sun shigo gidan kowannen su fuskar sa babu wani cikakken kuzari.
Kirjinta yayi wata wawuyar bugawa tace a fili "To ko ciwon yayi tsanani ne da har sai liman yayi masa addu'a?"
Can kuma saita girgiza kanta tace "To ai indai addu'a ce kad'ai Baba Jibrila ma ya iya shima malami ne,to ko dai mu...."
Da sauri ta damqe bakin ta kamar tayi sab'o sannan tace "Aa Turajo bazai mutu yanzu ba in sha Allahu."
Tana nan jikin window tana kallo bata sake jin qwaqqwaran motsin kirki ba,kusan mintuna talatin kakar su Turajo dake rigar kusa dasu da wasu mata sukayi sallama suka shigo kana kallon su kasan da matsala kakar tasu sai shab'ine take yi ta shige d'akin su sauran matan duk suka zazzauna a can daga gefe suka bubbuga taguma wasu a cikin su ma nata kuka saidai a hankali yanda ba wanda zaiji.
Take jikin Immileey ya fara rawa ra fara tunanin wani abun saidai bata son ta sawa zuciyar ta abinda ba haka ba don haka ta koma ta zauna ta takure ta cure waje d'aya tana jin yanda d'an cikinta keta sake wajen kwanciya saboda ta takure shi amma bata da niyyar motsawa balle ta sake zaman da tayi.
ZahraArkel ce!🥰