〰〰〰
*BUTULU*
〰〰〰
Story...writing by
*Maryam Abdul*
Wattpad @maryamad856
💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*
We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all..
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃Wannan shafin nakune *'yan Da BAZARMU WRITERS ASS*
ALHMDULILLAH inagodiya ga Allah subhanahu wata'ala da yabani dama da iko na sake antayowa acikin wani sabon littafin nawa......ina roqarsa da gaban dama da ikin kammalashi kamar yadda nafara yabani ikon isar da saqon da nakeson isarwa.....ameen thumma ameen.*DAGA MARUBUCIYAR:-
*BIYAYYA**page...1-5*
*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
*******Fatima matace ga *Abdallah* Wanda a lokutan baya suka zauna cikin tsantsar so da 'kauna da kuma kulawa ta musamman a tsakaninmu. sa'banin yanzu da Sam babu wad'annan abubuwanba dalilin kwa ya samu asaline ga larurar da *Fatima* ke d'auke da ita, wato tana fama da matsalar mafitsara ne hakan yasa take yoyon fitsari ga kuma infection(sanyi) datake d'auke da shi tun bayan da ta haifi d'anta na biyu mai suna *Yusif*
'Ya'yansu biyu *Basma* itace 'yarsu ta farko sannan *Yusif* Wanda yace sunan daddyn su suna cemai *Abba*.sakamakon wannan larurar ne yasa *Abdallah* daina kulawa dasu, hakan yasa yayi mugun tsanar ta Sam baya zuwa inda take kullum cikin hantara da sangwama take Wanda hatta yaran abun ya shafesu.Dan Sam baya basu abinci baya lura da shansu da kuma tufafinsu tsawon shekara d'aya da rabi kenan.
Sautari Fatima kan nusar dashi illar abinda yake musu, koda ace ita bai kula da ita ba sufa? ai 'ya'yan sane, amma ba abinda yake biyo bayanta sai zagi da cin mutuncin tare da ba'ka'ken maganganu.
Wanda hakan yasa hatta d'akinsa da take sureviving aciki yanzu ya mata iyaka dashi, bata da 'yancin ta shigeshi ahalin yanzu ko wani Abu takeson yi bata da ikon yi a cikin gidan farin ciki da walwala sum mata fintunkau.
Baya ajjiye musu komi ma nau'ikan kayan abinci haka zalika ficikarsa baya bata Dan tai wasu bu'katun.
Dan da yafara bata kud'i akan tai maganin larurar tata amma yanzu ya daina a cewarsa wai" asara kawai takeyi tunda ba'a samun wani ci gaba"
Wannan dalilin ne yasa take fafutukar neman maganin dakanta da kuma gumin ta sai dai yanzu kud'i sun yanke mata bata da wata mafita akai yanzu saidai ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido.
*Na'ima* 'kawace agareta tana matu'kar Santa kuma tana taimaka mata sai duk da haka Fatima bata ta'ba gayamata halin datake cikeba, sai da taga bazata Iya jire 'kumcin da take sha'kaba yasa ta sanar mata.
Na'ima tayi mamaki sosai 'kwarai da taji abinda ta 'boye mata tsawon wannan lokutan. "lallai ba shakka Teemanta jarumace" (dayake haka take cemata *TEEMAH*)
A lokacin ne kuma Fatima ta nunawa Na'ima robar fitsarin da take anfani da ita Wanda Na'ima bata ta'ba sanin tana tare da ita ba duk tsawon wannan lokacin.
Sai da Fatima take sanar mata cewa" ai bata bari agani musamman ma ita Na'iman sabida bataso ta tayar mata da hankali"
Nan Na'ima tai tamata fad'a akan hakan, tare da nunamata illar zama da ciwon har tsawon wannan lokutan.
"Lallai ta lura badan komi *Abdallah* yakeson ta'ba sai Dan lafiyarta, lallai *d'an Adam BUTULU ne, kuma ba shakka zata shayar dashi giyar mammaki akan Teemahn ta" da wannan tunanin ta koma gida.
Nan take gayawa Hajiyarta halin da Teemahn nata take ciki, nan Hajiya tai ta al'ajabi, take suka kira Dr. Aysha suka sanar da ita halin datake ciki.(sister d'in hajiya ce, itace 'karamarsu a d'akin su)
Nan tace " Na'ima takaita gobe hospital d'in ta duba ta" takya kwa sukai alqawarin taimaka mata.
Washe gari kam Na'ima take har gida ta d'au Fatima suka nufi asibiti, koda Dr.Aysha ta dubata ta tsorata da yadda gaban Fatima ya lalace gaba d'aya infection ya lalatamata gaba, nan dai ta d'ora ta akan wasu magungunan.sai da suka tsaya a pharmacy suka sai magungunan sannan suka wuce gida.
Bayan Dr. Aysha ta musu alqawarin cewa" zata sanar da wani babban likita Dr. Auwal Dan dole su nemi tai makonsa" .sosai sukai farin ciki da hakan.
........
Bayan kwana uku da zuwansu asibitin cikin dare Yusif ya dinga firgita jikinsa na wani irin mazari da zafi bakinsa na kakkarwa sai kace mai aljanu, cikin wannan yanayin ne hankalina Fatima ya tashi Dan Abdallah baya gidan hakan yasata ta sunkutoshi tayi waje batare da ta bi takan Basma dake bacci ba.Titin tsit ba kowa ikon Allah wani mai adai-daita sahu ya tsaya nan ya temaka mata tare da kaita wani asibiti amma private ne, sanin cewa shine asibiti mafi kusa dasu (Alheri hospital).
Koda suka je nan take aka wuce dashi emergency wata nurse ce ta kira babban likitan dazai Iya amsarsa a wayarta, takya kwa yace"gashi nan" cikin abinda baifi sakwan biyar ba yazo wajen.
Nurse dince tai mai magana tare da cewa" Dr.Auwal yana emergency yaron"
"OK" kawai yace suka shige ciki.take yafara aikinsa sai dai duk Iya 'ko'karinsu nasan ceto yaron hakan bai samuba domin ta Allah itace dai-dai.
Ganin cewa" dare ne yasa Dr.Auwal 'kin sanar da su halin da ake cike Dan ya lura da uwar yaron hankalinta atashi yake, Dan shi atunaninsa har mai keknapep d'in babansa ne"
Sai washegari yashiga yimusu nasiha mai ratsa jiki da zuciya sananan ya sanar musu da halin da ake ciki na rashin yaron.
Nan fa hankalina Fatima ya matu'kar tashi sosai sai dai duk da hakan besa tayi kukan da aka halatta ayiwa mamaci ba domin kwa takya tafara anbaliyar ruwan hawaye.
Nan ta ro'ki Dr.Auwal akan tanaso suyiwa Yusif jana'iza domin ko taje dashi gida ubansa bazai ta'ba kallon suba.
Nan Dr.Auwal yace mata" sai dai ya d'aukesu suje ga Ammin sa domin kwa shi baida ma aure" nan ta yarda suka tafi harda mai kekenapep d'in.
Cikin mutuntawa Ammi ta kar'besu, koda yagayamata halin da take ciki ta tausayawa mata, nan aka shirya Yusif Dan kaishi gidansa na gaskiya.
Bacin an dawone da awa biyu tai nufi komawa , bayadda base ba ta Dan 'kara koda awa d'aya ne tace" a'a" Dr.Auwal yaso yakaita amma Sam shima ta'ki, bayadda suka Iya haka suka barta ta tafi tare da fatan Allah ya sakya had'asu kodan su tai maka mata domin ga dukkan alamubtana da bu'kata hakan.
Koda ta koma zaune yake a falo har ta wuce ta tsaya sanadiyar kiran sunan ta dayai.
Ya kalleta yace" yawon bin mazan naki har yayi 'karfi da bazaki Iya zuwa na wuni ba sai kin kwana?"
Fatima ta kalleshi tace" haba ya Abdalla wannan wani irin tambayace haka, atunani na ko wanine ya gayama haka akai na sai inda 'karfinka ya 'kare, ban ta'ba tunanin 'kiyayyar da kakemin tayi tsamari haka ba"
"Ya isa dalla kina tunanin duk abinda kike aikatawa bansani ba Dan haka zamanki agidan nan ya 'kare Dan baza azo a haifamin 'ya'yan zina ba agida, baza adinga juyemin abincin haram agidaba, Dan haka na baki nan da minti biyu ki fice min a gidan na gaya miki"
Ta kalleshi ciki da mamakin abinda yake fad'a, kamar bashine ya Abdalla taba mai sonta da tattalinta, inason yaje ne haka? Meyasa yake mata haka Dan kawai Allah ya jarabce ta da wad'annan cututtukan?
"Naji zan fitar ma a gida amma kasani Allah baya yafe ha'k'kinkin wani akan wani, sannan jarrabawace Allah yana yiwa Wanda ya ga dama kuma ai abin murna ne agareni tunda nasan ina kankarar zunubai ne, sannan kuma kasani 'kazafin da kamin sai Allah ya sai damu ranar gobe alqiyama, sannan kajirayi ranar *nadama*, daman ance *d'an adam BUTULU*"
Cikin tsawa yace" naji koma me zakice naji ni dai yanzu ki ficemin a gida kinji ko?"
Ba tare da ta tsaya d'aukar tsinki ko neman Basma ba ta fice daga gidan zuciyarta na mata suya Sam batajin dad'in kanta" Allah ka kawomin mafita ta fad'a aranta"
Editing is not allow.....📵
Vote
Comment
Like and
Share....*Miss Gentle ce.....*✍✍✍
YOU ARE READING
BUTULU.....
RandomQalubale daga wajen mijinta sabida wasu larurori datake fama dasu.......kubiyoni dai acikin wannan 'kayataccen labarin Dan jin ya zata kasance. Banyishi Dan cin zarafin wani ko wata ba...'kir'kirarran labarine....kada a juyaminshi...Dan Allah akiya...