DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu1️⃣0️⃣
A haka Yafendo da Innah kakar su Turajo suka shigo suka same ta bayan su su Ladingo ne da Jamila matar qanin baban su Turajo da Atika matar qannin baban nasu suma."Sannu kinjiii,Ubangiji ya dube ku ke da abinda ke cikin ki Allah kada ya wahalshe ku rashin miji an rasa bango ga shekaru qanana Allah ya dube ku kinjiii." Abinda wata da Immileey ke tsammanin qawar kakar su Turajo ce ta soma fad'a kenan.
Da kallo kawai ta bita don bata ji kwakwalwar ta ta karbi saqon ba.
Innah Aziza tayi saurin dakatar da matar data sake bude baki zata yi wata maganar tace "Don Allah Asabe jeki waje."
Babu musu matar ta fice tana jinjina tausayin er mitsitsiyar yarinyar data lura kidima tasa ko cikakken motsi bata yi.
Kafin su fara magana sai su Goggo Lari da matar yayyan Immileey sun shigo,Innah Aziza ta ce "Yawwa qaraso nan Lari."
Goggo Lari ta matsa tana kallon Immileey da idon ta ya soye kallon kowa take kamar bata fahimtar abinda ake yi,Goggo Lari ta tabbatar Immileey ta shiga babban tashin hankali ne don haka take yi duk sanda wani abu ya firgita ta a hankali ta matsa ta riqo hannun ta,sai a sannan Immileey ta kalle ta sosai tace "Innah." Cikin wani irin sauti mai kama da rad'a.
Goggo Lari tace "Khadijatu dinga maimaita Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un."
Kamar er koyo haka ta dinga maimaitawa da taimakon Goggo Lari,a hankali ta soma dawowa hayyacin ta daga firgitar da tayi,can ta kalli Yafendo tace "Innah meya samu Turajo."
Duk suka zuba mata ido don babu wadda za ace ta fad'i sunan mijin ta na fari tunda ta had'u dashi aka tabbatar shi zata aura a cikin su kaf,babu ma wadda za ace don wani abu ya samu mijin ta zata nuna damuwa a gaban mutane kuma ta rasa wadda zata tambaya sai surukar ta,amma da yawa wasu a wajen sun mata uzuri don kana kallon ta kasan ba ta ciki cikakken hayyacinta wasu kuwa a ransu cewa suke bata da kunya bata da kara kaii har saida Ladingo ta magantu "Ke er nan yanzu duk wajen nan bamu isa ki tambaye mu ba sai Yafendo?"
Jamila faccalar ta tace "Ke Ladingo da zancen naki zata ji koda abinda ke damun ta."
A fusace surukar su tace "Dallah ku fita."
Sum sum suka fice Ladingo nata qunquni don sam ita mutuwar ba wani tab'ata tayi ba.
Jamila sai kuka take tana fad'in "Matuqar mutuwa bata zama aya mai tsoratarwa ga bawa ba kuma bata ladabtar da zuciyar mutum ba to babu wani abu da zai russunar dashi."
Yayin da ita Ladingo duk inda ta zauna sai ta fesa musu abinda Immileey tayi tama d'ora da nata,wasu magulmatan irinta su amshe wasu kuma su nuna mata rashin dacewar abinda tayi koma dai yaya ne taci nasarar b'atawa baiwar Allah Immileey suna cikin qanqanin lokaci tun kafin a kai gawar mijin ta data rasa.
Itako Yafendo sai ta kalli Goggo Lari bayan fitar su Ladingo itama ita take kallo,sai kawai ta fice daga d'akin tana share hawaye,tasani duk da qanqantar shekarun Immileey yarinya ce mai kara da kunya kuma tunda Ladingo taga wannan lamarin ta tabbatar sai an samu matsala nan gaba.
Atika matar qanin baban su Immileey ce tabi bayan Yafendo itama tana ta sharb'e hawaye.
Yafendo na ganin ta tace "Goggon ta ta kaita tayi masa sallama."
Atika tace "Kayya saidai ni na kaita tunda bata da yaya macen da zata taimaka mata."
Ta juya ba tare da Yafendo ta amsa ba ta shige d'akin,ta miqar da ita tace "Zo muje Immileey."
Ta kamata suka fice,a tsakar gidan mata suka bisu da ido kowa da irin tunanin da yake tsakanin su wasu na ganin rashin kunya da beken Immileey wasu kuma tsananin tausayin ta ne ya dame su,haka aka wuce da ita zuwa d'akin su.
Suna shiga Goggo Atika ta ajiye ta gaban gawar Turajo a kwance samb'al matashin saurayin da bai wuce shekaru ashirin da biyu ba a duniya kyakkyawa da shi,fatar nan luwai luwai sai ka rantse da Allah ba a qauye yake ba ga gashi mai kyau ya lullube fuskar sa don ma'abocin tara qasumba da saje da kuma gemu ne dake gashi ne mai kyau mai laushi dashi idanuwan nan a rufe amma kana ganin tsinin su da gashin su gazar gazar da sukea kwance saboda ruwan wanka ita dai kallon sa kawai take tana sawa ranta lallai bai mutu ba zai tashi bazai mutu ya barta ba.
"Immileey." Taji an kwada kiran sunan ta a tsakar gidan kafin aka dora da kururuwa da kuka mai sauti mai hade da hirji da salati da hailala "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shikenan yaro mai zumunci ya tafi yaro na gari mai karamci ya tafi,mai son 'yan uwa mai zumunci ya tafi,meyasa?meyasa Turajo zakayi gaggawa ka tafi?ya Allah meyasa ka d'auke mana mai had'a kan zuri'ar mu lokaci guda haka? Meyasa..."
Bata qarasa ba aka toshe mata baki aka shige da ita d'aki sannan akace a fito da gawar za a mata sallah.
Ai fa nan haukan Immileey ita kuma ya tashi don tana ganin an d'quke shi ta zunduma wani uban ihu ta haura kan makarar tana fad'in "Wallahi bai mutu ba,yace min bazan mutu ba bazai mutu ba sai mun tsufa tare kanar su Yafendo,cemin yai fa ko rani ya daina zuwa saboda ni ya zakuce ya mutu?don me zaku dauke shi,ku kwance shi yana jin zafi ku sake shi bai muku komai ba don Allah kada ku binne shi cikin qasa bazai sha iska ba,bai mutu ba,Yafendo kice kar su d'auke mana shi in sun dauke shi waye zai dinga miki aike warawa da binni? Don Allah ku dawo dashi."
Da qyar aka b'anb'are ta daga jikin sa tana kuka da ihu sosai kamar ranta zai fita,Goggo Lari ce ta qaraso a fusace ta tsinka mata wani kyakkyawan mari,ai sai ta shid'e ta tafi zata kifa akan cikin jikinta Allah ya rufa asiri aka taro ta.
Itama duk sai ta gigice ta shiga kuka sosai don dukan ne yai mata yawa,Yafendo ta qaraso tana fad'a na marin da Goggo Lari tayi mata aka d'ebe ta aka kaita d'akin Yafendon aka kwantar aka dinga shafa mata ruwa a fuska.
Mintuna kad'an ta farfad'o ta shiga sake rarraba idanuwa tsakanin mazauna d'akin,sai ta koma ta kwanta ta takure waje guda tana ta wuwwulla idanuwan ta kan mutane ko Allah zai sa ta gane wasa ake mata Turajo na raye bai mutu ba,tana jin d'an cikinta nata kusur kusur saboda takure shi da tayi amma bata sake damqe qafafuwan ta ba hawaye na wani irin gudu kan pillown data sa kanta har ya jiqa shi.
Don't forget to Vote and follow on Wattpad,,,,much love guys🥰
ZahraArkel ce!