DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu1️⃣1️⃣
Har yanzu ta kasa gamsuwa cewa Turajon ta shine wai aka tafi kaiwa maqabarta,shine wai ya mutu,ta kasa gaskatawa ji take gabad'aya kamar a mafarki ne don haka cikin kuka ta soma furta "Ya Allah idan mafarki nake Allah kasa na farka na daina ganin wannan mummunan mafarkin wayyo Allah na ya Allah kada kasa Turajo ne ya mutu wannan wacce irin jarrabawa ce idan har da gaske ya mutu?"Da sauri Goggo Lari ta miqe ta matsa kusa da ita don basu lura ma ta tashi ba saida suka ji sheshshekar ta,ta jawo ta jikin ta ta rumgume tana bubbuga bayan ta sannan a kunnen ta tana rad'a mata "Tun d'azun nake fad'a miki Innalillahi zaku riqa karantawa shine zaki samu nutsuwar ranki."
Kai kawai take kad'awa tana sake jin wani kukan na taso mata,ta toshe bakin ta da hannuwanta jikinta har rawa yake,Goggo Lari tace "Aziza jeki ki kawo mata ko fura ne tasha naga gashi har azahar ta kusa da alamu bata ci komai ba."
Innah Aziza ta miqe ta tafi wajen Yafendo ta rad'a mata abinda suke buqata,Yafendo tace "Nima nan tunanin da nake kenan muje na nema mata wani abun."
Koda aka kawo madarar qememe taqi sha da suka takura mata sai ta sake fashe musu da kuka,dole dai suka haqura suka qyale ta don ba yanda zasuyi da ita,saidai tausayin ta fal ciki.
Sai da akayi sallar azahar sannan en kai gawar maqarbarta suka dawo don ba a kusa take ba can gefen gari take daga ita sai babban titi dake fita daga garin wanda shi zai kaika har warawa ya fidda ka kano.
Koda taji sun dawo ana ta sake karb'an gaisuwa,yayyen ta su Ila suka shigo har cikin gidan da wasu yi musu ta'aziyya,tana ganin su tace "Hammah Ilah da gaske kaga sun sa Turajo cikin qasa sun taho sun barshi acan,ku baku san da duhu ba kuma baya son duhu,meyasa kuka baro shi?"
Ilah ya sunkuyar da kansa tausayin yarinyar na damun sa kafin yayi magana koya d'ago sai salati yaji na mutane ta sake kifewa ta suma Allah ya taimaka a jikin Goggo Lari take da inta fad'i Allah kad'ai yasan abinda zai iya faruwa.
Abu kamar wasa yini Immileey tayi tana suma saidai in bata ga maza sun shigo gaisuwa ba,idan mata ne susucewa take sosai taita surutai tana gaya musu yace zai dawo bai mutu ba.
Dasu Fad'ima kuwa suka zo anga tashin hankali kamar kwantacciya haka ta zama,sai dare su Goggo Lari suka ce zasu tafi,nan ma kafewa tayi ba inda zasuje saidai ta bisu suje tare duk fa yanda suka d'auki abun da sauqi ya wuce tunanin su lallashin duniya taqi yarda dole sukace sun fasa tafiya ta kwanta ta huta haka kuwa akayi ta kwanta dake tun safe a wahala take sai bacci ya d'auke ta,a sannan suka sulale suka tafi Goggo Lari nata tunanin d'iyarta da tsananin tausayin ta.
Cikin dare ta farka da yunwa saboda yinin ranar bata ci komai ba,da addua ta farka a bakin ta kafin ta soma tab'a Yafendo dake kusa da ita cikin bacci tana cewa "Turajo ka tashi yunwa nake ji zanci abinci."
Yafendo ta miqe a hankali don kar ta ankarar da ita batayi magana ba ta miqo mata kwanon tuwon data ajiye mata,aiko taci da d'an yawa ta bata ruwa tasha sannan ta koma ta kwanta,kuka ne ya kwace mata don bilhaqqi yarinyar ta bata tausayi ba kad'an ba yanda tayi kasan zancen mutuwar ya b'ace mata sam tunanin ta yanzun ba a kai yake ba tasan da safe za a sake tashi da wata sabuwar rigimar ne,haka taje tayo alwala ta tada sallah tana roqarwar Immileey sauqin rayuwa babu mijinta da kuma shi mamacin Allah yayi masa rahma.