DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu1️⃣3️⃣
A asibiti bayan sun kaita aka karbe ta nurses suka shigar da ita wani d'aki aka hana su Mummy shiga.Likitan matashin saurayi da bazai wuce shekaru ashirin da shida ba,ya gama baice mata kanzil ba ya juya yana shirin fita tace "Don Allah meke damuna?"
Ya juyo yana kallon ta,qanqantar ta tayi masa yawa ya gaya mata a ganin sa,sai kuma wata zuciyar tace masa idan tayi qanqanta ta d'auki ciki?ai dole tasan wasu abubuwan.
Sai ya juyo yana kallon ta sosai yace "Firgitar da kikai badon Allah ya rufa asiri an kawo ki asibiti da wuri ba komai na iya faruwa kuma akan wannan stage d'in za a iya rasa ki a rasa baby d'in."
Ta lumshe ido a hankali sannan ta bude su akan fuskar sa tace "Don Allah likita in roqe ka wata alfarma?"
Cike da mamaki yace "Ehen inajin ki."
Tace "Don girman Allah kada ka fad'awa su Mummy cewa firgita nayi."
Cikin wani mamakin yace "Meyasa,ai an fiso a kula idan matsalar daga wajen sune ko wajen mijin ki ba gara a sani ba don za a iya samun babbar matsala idan hakan ta sake faruwa."
Tayi guntun murmushi tana danne kukan da yake shirin taso mata tace "Don Allah kayi min wannan alfarmar na maka alqawari daga nan har na haihu babu abinda zai sake faruwa makamancin haka don Allah wallahi zan kula."
Yace "To amma menene dalilin ki na b'oye musu?"
Tayi guntun murmushi tace "Bazan iya fad'a maka ba kayi haquri,nidai ka taimaka kamin wannan alfarmar."
Ya d'aga kafad'a tare da watsa hannayen sa biyu yace "Well,tunda kince kada na fad'a musu me kike so na je na fad'a musu kenan ya same ki?"
Ta d'an yi shiru tana tunani can da sauri tace "To kace juyi ne mana." Ta qara da dariyar data fito da tsantsar kyanta dimples d'inta manya suka lotsa.
Ya qura mata ido cikin wani nazari har saida tace "Doctor."
Firgigi yace "Ju,juyi kuma?"
Ta jinjina kai tace "Eh."
"Menene juyi?"
Ta d'an sake yin shiru,itafa harga Allah bata san meye wani juyi ba ta dai ji ana cewa masu tsohon ciki suna yi,kuma itama nata cikin ya tsufa don haka tayi tsammanin itama ai za a iya cewa tayi d'in sai kawai tace cikin yarinta "Kaga ni bansan mene shi ba,kawai dai naji Innar mu na cewa masu tsohon ciki suna yi kuma kaga matan yayyen na su Hammah Ilah duk suna yi kaga nima in ance nayi ba mamaki ko?" Ta qarasa da zuba masa manyan fararen idanuwan ta tana kallon sa.
Duk ya daburce,amma sai ya tuna tsohon cikine fa da ita lallai kenan tana da aure take ya fara auziyya yana korar shedan.
Cikin mamaki tace "Menene kake a'uziyya kuma likita?."
Ya sosa kai kan yace "To shikenan Khadija zan fad'awa iyayen ki haka,Allah ya baki lafiya ya sauke ki lafiya amma ki kula kinji."
Ta rufe fuskar ta da zara zaran yatsun ta tana dariya wai ita kunya,kawai sai yaji ta burge shi,duk da kasancewar ta yarinya amma kana kallon ta kasan gaba za ayi mace dirarriya,ganin shedan na neman rinjayarsa yasa yayi saurin juyawa ya fice daga d'akin.