DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu1️⃣4️⃣
Baffan yace "Hmm Lari zata yi ni banga laifin ta ba dubi yanda ake baki labarin yanda yake mata ko a gidan nasu ko a gaban uwar tasa,ni nama ga qoqarin ta don ma da quruciya ne inda wata ai ko me za ayi mata baza ta daina jimami a en satikan nan ba amma ita yanda Hamisu yake bani labari ta waya har ta ware abinta tana ta wasa da en uwan ta na kuma tabbatar cikin nema zai hana ta wani abun."Goggo Lari ta jinjina kai tace "Allah sarki yaro kenan."
Haka suka cigaba da hira akan Immileey da Turajo lokaci mai tsaho kafin Baffan ya fice Goggon kuma ta cigaba da en hidimomin ta na gida.
✨✨✨
Kan magriba ta farka da matsananciyar yunwa kamar wadda aka yiwa sata duk tuwon da taci kafin ta kwanta.Ta miqe har wani dishi dishi take gani kamar wadda ta kwana ta yini bata ci komai ba,da sauri ta sauka tana kwalawa Sabuwa me aiki kira.
Da sauri Sabuwan ta fito daga kitchen hannun ta riqe da kofi da alamun had'e kwanuka take taji kiran.
Immileey ko harta fara kuka,Sabuwa ta gigice ta zata haihuwar ce tayi saurin ajiye kofin ta qarasa inda take tana cewa "Lafiya Lillimi(Abinda take kiranta kenan don bata iya cewa Immileeyn ba.)."
Cikin kuka tace "Yunwa nake ji har na fara jiri don Allah zanci abinci."
Sabuwa ta kamata jikinta har ya fara rawa irin na kaji yunwa da yawa ta zaunar da ita ta koma ta zubo mata sauran tuwon da aka rage na rana ta hado mata tea mai kauri ta kawo mata.
Ai kamar zata had'a da hannun ta haka ta riqa ci har saida ta cinye malmala guda qatuwa sannan ta dawo hayyacin ta fuska jage jage da hawaye,Mooha da Lameen suka shigo suka sameta tana shan tea.
Lameen ya kalli kan dinning d'in cike da takaici da bala'i yace da qarfi "Uban waye ya baki izinin zama a wannan kujerar,ke akan dinning d'in ma gabad'aya."
"Uban ka ne." Mooha ya fad'a calmly yanda daga shi sai shine suka ji,sannan ya d'ora da "Kada ka yarda Abeey ko Mummy su san halin da ake ciki domin d'azun da kayi mata ta safe saida kasa ta kusan b'arar da cikin jikinta kuma dake er halal ce mai dattako sai ta b'oye musu ta hana kuma a fad'a don haka wallahi ka bari suka gani zakaji ba dadi ne."
A fusace yace "Ni ka zaga?"
Mooha ya girgiza kai yace "Ni ba zagin ka nayi ba tambaya kayi na baka amsa kuma kasan Abeey da Mummy na nan idan ka bari wannan daga muryar da kake sukaji suka tambaya ni kasan fada musu zan."
Ya dubi Immileey datai tsuru tsuru kamar mai shirin sakin fitsari a wando yace "Acici yanzu duk tuwon da kika ci d'azun shine yanzu ma kika sake ci."
Idon ta yai raurau hawaye suka soma bin kumatun ta alamun ba tsokanar sa take wa kukan ba sai ya zauna kujerar dake kusa da tata ya kamo hannun ta ya soma bata haquri da maganganu masu dad'i.
Shiko Lameen kamar ya fasa ihu saboda wani mugun tuquqi da zuciyar keyi na baqinciki ya kalli inda take zaune,kujerar sace da indai ba Amnah ba ba wanda ya isa zama akan ta duk gidan sun sani amma wannan gidahuma baqauyiyar ta zauna masa take yaji dinning table din ma gabad'aya ya tsane shi,ya kalli plate da cup d'in da take shan tea,duka wanda suke amfani dashi ne ai sai yaji wani amai yana neman taso masa cike da takaici ya kwalawa Sabuwa kira.
Ta fito da hanzari yace cike da tsanar ta itama "Ke yanzu saboda iskanci da rashin mutunci kwanon da muke cin abinci kike zubawa wannan qazamar abinci a ciki?to daga yau kada ki qara serving d'ina a wad'annan kwanukan sai na Abeey kafin na siyo nawa."
"To ranka ya dade." Ta amsa tana sunkuyawa alamun girmamawa.
Shi kuma ya juya ya fice kamar kububuwa.
Immileey ta sake fashewa da kuka mai ciwo sannan ta miqe ta haye sama,ranta in yayi dubu ya b'aci kamar ta had'a kayan ta tabar gidan haka ta dinga ji shine daren data soma danasanin zuwan ta kano kuma takejin baza ta iya sake zama ba bayan haihuwar ta gara ta koma qauyen su ta sake yin auren ta da wannan wulaqancin da Lameen ke mata.
Taci kuka mai isarta har saida ta ji shigowar su Amnah tayi kamar bacci take suka qaraci hayaniyar su suma suka kwanta.
Mooha kuwa a wani irin harzuqe yaje ya samu Lameen,wannan karon fad'an da basu tab'a yi ba suka yi ya kuma ce ya rantse da Allah idan ya sake yi mata wani abun har ya sata kuka saiya fad'awa su Abeey.
Shi kansa Lameen d'in yasha mamaki don bazai iya tuna sanda yaga ran Mooha ya b'aci irin haka ba,don shi mutum ne mai matuqar haquri da kawar da kai ga abubuwa kuma komai wasa yake maida shi,dole ya qyale shi don yasan idan yai irin wannan fusatar komai na iya faruwa.
Haka zaman gidan ya kasance,Mooha da sauran yaran gidan na jan ta sosai a jiki suna sonta haka ta zage tana koyon turanci da sauran karatuttuka kan kace kobo dake mai qwaqwalwa ce ta iya har doka Mooha yasa a gidan ta speaking vernacular kuma ta dage saidai ai mata gyara kad'an kafin cikar sati biyu ma gyaran baifi ai mata shi sau biyu ba a yini.
Satin ta hud'u da kwana biyar da zuwa kano ta tashi da nakuda cikin dare,wani irin azababben ciwo da tunda aka haife ta bata ma zaci akwai irin sa ba.
Salati ta somayi kafin ta soma tashin Amnah dake kusa da ita aiko da gudu tayi part d'in baban su,yayi tafiya sai Mummy kawai ta taso ta itama taje ta taso Mooha shiya sunkuce ta Mummy ta d'auki akwatin haihuwar suka tafi harda Jannah.
Suna zuwa aka karb'e ta akayi labour room da ita,taci azaba don tun wajen d'aya na dare har qarfe shabiyun rana tana abu d'aya likitocin har sun sare sunce ayi mata aiki kawai an ma gama shirya ta Mummy tasa hannu a takardar aiki sai kuma kan baby ya turo,dole suka tsaya suka taimaka mata ta haifo sankaceciyar d'iyar ta fara tas mai kama da baban ta kamar yayi kaki ya ajiye saboda kyau sai kace er aljanu ce hancin nan dodar dashi tubarkallah saidai ta wahalar da uwarta.
To maijego Immileey saidai muce Allah ya raya baby girl.
ZahraArkel ce!🥰