Part 15

299 22 4
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu


1️⃣5️⃣
Murna wajen bayin Allahn nan ba a magana musamman Mooha daya qanqame jaririyar ya hana kowa ita harda Mummyn balle su Jannah qiri qiri yace baza su iya ba saidai su kalle a hannun sa.

A gadon marasa lafiya aka gangaro ta tana ta baccin wahala,likitan da wancen karon ya ganta sune dai su biyu suka fito daga d'akin haihuwar,ya miqawa Mooha hannu yana murmushi yace "Congratulations."

Mooha ya karb'a yana dariya yace "Thank you."

Ya leqa baby d'in yace "Allah ya raya muku ita."

Ya amsa da amin,sannan suka wuce.

Har sun d'anyi nisa Mummy tace "Ahm Doctor."

Ya juyo yana murmushi yace "Dr.Heelal."

Ta jinjina kai tace "Ok Dr.Heelal sai yaushe zaku bamu maijegon?"

Yayi murmushi sannan yace "Muje Office Mama."

Mummy da Mooha suka bi bayan sa,suka shiga tsararren office d'insa mai kyau,kujerun da suke fuskantar sa ya nuna musu tare da cewa "Bismillah."

Bayan sun zauna yace "Khadija ta d'an sha wahala wajen haihuwan nan ku kanku shaida ne don haka muka ga ya kamata mu bata bed rest don haka zamu riqe ta har zuwa gobe in Allah ya kaimu lokacin ta huta sosai ku zaku iya tafiyar ku gida da baby d'in muna da masu kula da ita."

Mooha yace "Idan baby d'in tayi kuka me zamu bata?"

Yayi murmushi yace "Ku bata madara kafin maman ta ta tashi."

Mooha ya kalli Mummy yace "Madara kuma wacce iri?"

Mummy ta kalli Dr.Heelal tace "Likita rubuta mana sunan madarar da za a bata."

Ya rubuta ta bayar,har sun miqe tace "Amman zan iya zama ni?"

Ya jinjina kai yace "Zaku iya mana saidai ko kun zauna baza ku shiga inda take ba gaskiya saidai goben don so muke ta huta."

Tace "Bakomai."

Suna fita ta kira Abeey ta fad'a masa yayi murna shima sosai yace bari ya kira Gogel ya sanar.

Aiko suna jin batun duk matan yayyen Immileey harda Goggo Lari aka tattaro mota guda aka taho kano a wannan yammacin.

Sai gab da magriba suka iso asibitin aiko dai wannan jaririya tasha d'auka,Mooha fa ransa in yayi dubu ya b'aci sai gunguni yake shi kad'ai wai ana jagwalgwal ta (nidai nace ji su Muhammadu da qarfin hali.)

Haka tun basu gama tantance ta ba Mooha yayi kicin kicin ya karb'e ta,nan fa suka dinga masa tsiya amma qememe yaqi bada ta daga qarshe ma sai yace wai likitan yace kada a jagwalgwalata da yawa shiyasa,dolen su sukayi shiru suka qyale shi aka cigaba da hira har bayan isha sannan duk suka tafi gida don likitan yace ba sai an kwana ba duk da da Mummy ta dage ita zata zauna dole daga baya suka tafi da baby d'in.

Immileey kam sai wajen biyun dare ta farka,tayi miqa tare da salati nurse dake wajen tayi saurin qarasawa inda take tayi mata sannu tare da tambayar ta me take ji.

Ta girgiza kai tace a hankali "Bana jin komai saidai jikina yayi tsami."

Ta jinjina kai tace "Ok bakomai wannan zakiji dama da safe."

A hankali ta lumshe idonta tana tuno abinda ya faru,nan ta tuna irin azabar da tasha wajen haihuwar nan harta fita daga hayyacin ta,haka taita zuba ido ko nurse din zata ce mata ga baby d'in amma shiru daga qarshe kawai sai ta yanke a ranta maybe ya mutu shiyasa ba a bata ba don haka maimakon tambayar sai ta bige da neman abinci.

Brush ta taimaka mata tayi sannan ta hada mata kakkauran tea da kayan shayin Dr.Heelal daya basu yace ta had'a mata in ta tashi.

Ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta bayan nurse din ta bata magani.

Tunaninnika kala kala ta dinga yi na irin burikan da Turajo keci akan wannan d'an ko er da zasu haifa kodayaushe yana gaya mata abubuwa daban daban akan sa yau gashi ta haife Turajo bai gani ba,ita d'in ma gashi bata ganshi ba ya koma ga mahaliccinta.

Kuka sosai ta dinga yi tana tuna Turajo da lokutan su tana kuma ji a ranta bata ga wa zata so ba sama dashi don shine ginshiqinta shi ta fara so kuma shiya koya mata soyayya da sonsa kad'ai ta saba taya zata so wani bayan sa?

Nurse din ta dawo ta tarar da ita tana wannan kukan tayi tambayar duniya Immileey taqi kula ta,saita qyale ta ta koma ta zauna tana kallon ta da mamakin yarinya qanqanuwa irin ta to me zai sata kuka haka?a ranta tace "To kodai cikin shege ne?" Sai kuma tayi saurin cewa "Ba lallai ba wataqila dai akwai wani abun ba cikin ne ya sata kuka haka ba koma menene Allah ya sauqaqa mata don tayi yarinta da damuwa."

Da asuba Dr.Heelal ya dawo asibitin saboda Immileey,yazo ya tarar da ita tayi sharkaf da zazzabi saboda kukan da ta sha har nurse d'in ta bata magani saidai har a lokacin kuka take.

Shi kansa babu irin tambayar da baiyi mata ba amma taqi magana,magana daya tayi masa data ce ya kira mata Mummy da Hammah Mooha yace zai kira su zasu zo.

Tun qarfe 7 na safe kuwa suka shiga asibitin rankatakaf d'insu,ai tana ganin Goggo Lari sabuwar shagwaba ta tashi,duk suka dinga mata tsiya amma bata kula su ba.

Mummy ce tace "yanzu ke Immileey ko abinda kika haifa baza ki nema ba sai Goggon ki kika sani ko?"

Saida gabanta ya fad'i amma ta kanne taqi kula maganar ta cigaba da narkewa da Goggon nata kamar wata jaririya.


ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now