DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu1️⃣6️⃣
Ba a jima ba wajen tara saura aka sallame su sukayi gida suna zuwa Goggo Lari tace sufa zasu juya kuma da Immileey zasu tafi.Mummy tace "Ayya da na zata sai anyi suna zaku tafi da ita?"
Goggo Lari tace "Wallahi Baffan ta saida ya jadadda a taho da ita,sannan iyayen yaron nan suma sun roqi arziqin a mayar da ita can ta haihu,to kinga Allah yayi anan zata haihu gara kuma mu koma tayi wanka acan."
Dole ba yanda ta iya haka ta had'a mata kayanta tasa Mooha yaja motar da ta shiga,ai su Jannah kamar zasuyi kuka sune sukayi rakiyar ta har Gogel suka dawo.
Duk abinda ake Lameen na sashen su daki a kulle,saidai idan yana buqatar wani abun ya kira layin kitchen da suke da waya a ajiye Sabuwa takai masa sai mita yake kamar yayi menene don haushi,sanda yaga sun tafi wajen azahar kamar ya zuba ruwa a qasa yasha don murna ya dinga addu'ar Allah yasa Immileey ta tafi kenan.
A b'angaren su kuwa suna zuwa Gogel zancen haihuwar ya karade ko'ina,ai nan da nan gidan su Turajo aka samu masu shiryowa da en kayan al'ada da akeyi da farko lokacin haihuwa aka taho cikin masu tahowar harda Ladingo.
Sanda suka zo Immileey ana mata wanka an kuma gamawa jaririyar wanka itama,don haka aka basu ita har Immileeyn ta fito tazo ta shirya sannan tazo suka soma gaisawa ana ta mata barka da samun kai da kuma wannan carkwadediyar jaririya kowa na taya ta murna,ba amsawa take ba sai murmushi dai irin na alkunya.
Caraf Ladingo ta karb'e ta tana kallo tace "To yarinya Allah ya raya ki ya raba ki da rashin kunya irinta iyayen ki."
Kowa yaji abinda tace amma duk akayi shiru ba wanda ya kula ta can ta sake cewa "Ga yarinyar nan da kyau haka saidai bata kama da Turajo kuma bata kama ma da dangin mu kaf ko ina ta d'auko kuma oho don naga bata kama ma da Immileeyn."
Anan kuma Innah Aziza tayi magana tace "Ladingo kenan,ai kama bata tabbatar da jini na tabbatar kamar yanda Hamisu naki yazo a baqi wuluk kamar kad'o."
Cikin fushi ta miqawa Hadiza faccalar ta jaririyar kafin ta kalle ta tace "Aa Aziza menene nufin ki?"
Cikin murmushi tace "Ni ban da wani nufi kawai dai na gaya miki abinda yake dahir ne."
Ganin za a fara sa'insa yasa sauran suka ce a tashi a tafi,don dolen ta tafi saidai ta qudura a ranta zata dawo kuma zata ci mutuncin Aziza yanda taso cin nata mutuncin.
A hanya taita mita ba wanda ya tanka mata har suka kusan isa gida sannan Hadiza ta kalle ta tace "Kiyi mana shiru Ladingo kece kika fara tsokanar su kike neman shegantaka musu yarinya babu kwa ta yanda za ayi su qyale ki kuma in ba son zuciya ba kowa ya kalli yarinyar nan yaga mahaifin ta babu maraba amma kika fadi wannan maganar kinsan kuwa tunda ba tsoron ki suke ji ba baza su fasa mayar miki ba,kuma kiyi shiru tun kafin Yafendo taji ki kinsan zata ci mutuncin kine tunda Turajo na raye ma baya tab'uwa wajen ta balle tana ga ya rasu kuma wannan er zata dinga gani madadin sa tana jin dadi."
Ladingo tayi shiru tana ta cin zuciya don daman Hadizan ce kad'ai ke taka mata burki idan ta kwaso wani iya shegen nata dole kuma tai shiru da bakin ta.
A d'akin Yafendo sukayi ta bata labarin jaririyar nan tubarkallah,taji dadi sosai ta kuma sake azamar hada sauran kayan barkar da basu had'u ba harta haihu don a kai.
Da magriba aka dauki jaririyar aka kaiwa iyayen Turajo sukayi mata addu'a suka sa mata albarka kowa a cikin su ya yaba da irin kyan ta tubarkallah anan kuma yayyen Turajo suka dinga mata kyauta daga mai saniya sai mai tinkiya da rago da mai awaki da zabi da kaji haka aka tara mata kuma duk sukayi alqawari kafin suna za a kai musu can gidan su.
Bayan tafiyar su Immileey ta kalli jaririyar da Ladingo tace bata kama da baban ta sannan ta kalli Innah Aziza tace "Innar Hashim Meyasa Ladingo tace wannan yarinyar bata kama da Turajo kuma ni naga suna kama."
Kafin ta bata amsa Goggo Lari ta shigo d'akin da kwanon kunu tana kallon Immileey ta ajiye kwanon a gabanta tana cewa "Shiyasa ake ta yawo dake ana baki da kunya dubi wai d'iyar fari ce kike qarewa kallo har kina wannan maganar a kanta ba dole ace baki da kunya ba tunda kin gwada baki da ita."
Immileey ta turo baki alamun shagwaba kan tace "To Innah nifa ba wani abun nake mata ba kuma ni dana ji Ladingo tace basa kama ne nake mamaki ba wani abun ba."
Goggo Lari tace "Ey ai a hakan kin gwada rashin kunya a al'adar mu,mu a lokacin mu kallon arziqi baza kiyi wa d'an fari ba ke hatta abokin sa ko qawarta bake ba kulawa."
Ta jinjina kai tace "Tap."
Goggon tace "Baza ki iya ba kenan."
Ta kauda kanta gefe bata ce komai ba,Innah Aziza tace "Kinsan kuma jariri ma bai cika nuna kama ba sai ya tasa za a gane amma abune irin na Ladingo wannan yarinyar duk wanda ya kalle ta indai yasan Turajo ai yasan fuskar sace kamar tasa aka dauko aka dora a tata."
Goggo Lari tace "Ni dai na rasa me yarinyar nan qarama tayiwa Ladingo wadda ta ma girme mini don sanda aka mata aure muna emmatanci ne amma take wannan abun."
Innah Aziza tace "Toh naji ance ai so take ya auri Harira yar wajen ta da yaqi ya auri Immileey shine take wannan abun."
Immileey ta tab'e baki tana dai jin su ta maida hankalin ta wajen shan kunun da take lokaci lokaci kuma tana kallon er babyn ta mai kyau tana tuna fuskar mijin ta da wasu lokutan su da suka shude tare,wani lokacin tayi murmushi wani lokacin ta faki idon su Goggo Lari ta share hawaye.
Haka suka cigaba da zama Immileey na wanka safe da yamma haka jaririya na samun kulawa sosai har ana gobe suna,a sannan ne Immileey taji ana zancen saka suna ta je wajen Innah Aziza tace "Innar Hashim ina da magana."
Ta juyo tace "Ina jinki."
Tana wasa da yatsun ta tace "Zancen saka suna ne,Turajo tunda cikin ta yace idan macece zai saka mata Hauwa'u idan namiji ne Adam,ina roqon alfarmar don Allah a cika masa burin sa." Ta qarasa da goge er qwallar data tarar mata.
Innah Aziza cike da tausayin ta tace "Karki damu za ayi Allah ya raya Hauwa'u Jidda."
A ranta ta amsa da Amin sannan ta juya,haka kurum ta tsinci kanta da wata irin kewar Turajo ta takure can qarshen gado taci kuka ta qoshi sannan taje ta wanke fuskarta ta dawo ta kwanta tana cigaba da zirarar da hawaye.
Don't forget to vote,comment and follow on wattpad.
ZahraArkel ce!🥰