DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
1️⃣7️⃣
Duk da ba taron suna suka so yi ba ko don yanda mahaifin yarinyar bai dade da rasuwa ba amma saida mutane suka taru,wasu tsakani da Allah barka sukazo wasu ko tsabar gulma ta kawo su don ana ta yamadidi a gari ana Immileey ta murmure tayi qiba wasu tsabar sharri ma har an fara lisafta wad'anda wai suka soma zawarci a kwanaki bakwai kacal da fitar ta daga idda kana da haihuwar ta.Da gaske ne Immileey ta murje ta cika musamman qirjin ta dake shayarwa take kuma ta samu kyakkyawar kulawa don ba a barinta ta huta da abinci mai kawo ruwan nono sosai don haka ta cika sosai.
Saidai ga wasu irin su Ladingo cewa suka riqa yi daman mutuwar Turajo take so don da alama daman ba tsarar sa bace kai harda masu cewa a binciki mutuwar nan ta farad daya haka anya ba sa hannunta.
Wannan dai baiyi tasiri ba don ansan yanda suka so junan su sosai saidai fa zagi kam tana kan shan sa musamman daga su Ladingo.
Yarinya tasha kyautuka na dabbobin kiwo kala kala haka aka kawo su wajen Baffan Immileey shi kuma ya ware kewaye guda ya zuba mata kiwon ta yace kuma Allah ya raya ta,shima ya qara da nasa daya bata.
Immileey ba qaramin dad'in zaman Gogel taji ba don ba fita take ba balle ta jiyo abinda zai bata mata rai haka nan tsakanin ta da Hauwa'u shan nono idan an kawo ta.
Anan hutu su Jannah suka tattaro suka yo Gogel,shima Mooha sai ya d'auki hutu a office suka taho tare ai ko gidan su Immileey suka tare shi kad'ai ke kwanan gidan kakanninsu shima safiya nayi yake tafiyar sa wajen su Immileey sai kuma dare.
Safiyar juma'a lokacin sauran kwana biyu su Immileey suyi arba'in tana zaune ana mata kitso suna ta hira dasu Amnah da Innah Aziza Hauwa'u na bayan Jannah ta goya ta ya shigo da sallamar sa.
Ko zama baiyi ba ya kalli Goggo Lari yana cewa "Don Allah Goggo bance a daina bawa yaran nan Eve ba?sai sun sa ta samu matsala a wuyan ta."
Goggo Lari ta kalle shi da mamaki tana cewa "Wacece kuma haka ni Lariya."
Amnah ta kwashe da dariya tana cewa "Yana nufin Hauwa'u da turanci."
Murmushi kawai tayi tace "To ni ya zanyi na hana su kuma dai suna iya d'aukan ta fa jibi yanda Fiddausi ta goye ta tsap fa."
Jannah tace "Kuma naga ko Khadijan ma na fita girma kuma tana d'aukan ta ta bata milk."
Immileey tace "Ni ki daina sani a zancen ku ba ruwana."
Mooha yayi dariya yace "To ko ma da ruwan ki yarinya nan da wasu watanni ne zan d'auke ta kema ban yadda da irin riqon da kike mata ba kullum sai an gyara miki."
Bata kula shi ba ta cigaba da karanta wani littafi na turanci da Jannah ta kawo ta,ihun da Hauwa'u keyi yasa ta d'ago ta kalle su Mooha na cewa Jannah ta sauko ta,ta kwanto ta tana ta zumbura baki.
Ya karb'e ta yayi mata kiss a chick d'inta kafin yace "Haba yarinyar sai azabtar da ita kike kin matse mata kumatu ba dole tai ihu ba."
Goggo Lari tace "Babu ruwan Fiddausi wannan kuma saidai kai wa uwar ta don nono ma wai er banzan er nan taqi ta bata yanda ya kamata a rana baifi ta d'auke ta sau d'aya ba shikenan."