EPISODE 1

426 19 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

🌐  *RASHIN SIRRU*
(Sharrin Abokai)

BY JANNAH JAY
Wattpad @jannahjay8

Assalamu Alaikum 'yan uwa da abokan arziki yau na dawo tare da sabon novel dina "Rashin sirru" Wanda zaiyi magana akan rashin kame baki da fayyace sirri wanda nakirashi da tallata kai da ma'aurata kanyi ga abokansu, had'e da bayyana cigaba wanda wasu garin burga da show up kan janyo hassada tsakanninsu,  wasu kuma sukan daukeshi a wayewa, wadda son rayuwar turai kan ingizasu ga yin hakan,  mafi akasari anfi jinginawa mata hakan sai dai fa mazan ma kanyi hakan da nasu salon duk da nasune bai fito filiba, ba a tsarin aureba ko a fanni na zaman rayuwa baki shikan janyowa mutum nak'asu dayawa, komi  yakasance na mutum awaje hakan kan bawa mai cutar dakai dama.Bazan cikaku da surutuba ku biyoni don kuji me wannan littafin ya k'unsa.

E:1
 
Tsaye yake yana gyara zaman links ahannunsa inda abokinsa Hamza ke kallonsa yana sauraron yanda yake kod'a Zee d'in tasa, yana tallab'ar fuskarsa yana murmushi sai kuma yace " Sulaiman gaskiya ina son naga Auran ku ko wane irin zama zaku yi? Da alama Zee ta cika duk wani qualities da kowanne namiji ke so ga mace" maganar Hamza ba k'aramin dad'i tawa Sulaiman ba take yace " K'warai aboki ai da ana wuce wa da zan iya ce maka tuni Zee ta wuce hakan, don gaskiya a mata sai ka jera d'ari baka samu irinta d'ayaba" haka suka cigaba da hirar rakinsu duka kan 'yan matansune, a haka Salman yazo ya samesu shima ya d'ora.

Kwance take akan medium gadonta tana juye-juye hade da sakin murmushi, yayin da wayarta ke hannunta tana chat da Sulaiman, hira suke mai cike da soyayya mai tsafta mai kuma saka nishad'i, a nan yake sanar mata zai zo da abokinsa Hamza wanda tasanshi abakinsa amma basu tab'a had'uwaba, bataji komiba don ta saba da gaisawa da gayyar abokansa, domin shid'in mutum ne mai abokai sosai sannan yakan basu muhimmanci, kuma matuk'ar zaka yarda ka biyoshi to lallai zai kawo ka kaga Zee, saboda a wajan Sulaiman cewa yake " Zee nasan bawanda zai ganta ya kushemin ita, sannan dole a yaba da zab'ina, ga kyau ga diri ga ilmi ga nasaba wato asali, ga uwa uba ta waye ta fannin addini da zamani" ba k'arya Sulaiman yayi ba  sannan kuma ba giyar soyayya yasa yake kaita wannan matsayin ba, tabbas Zee Allah ya mata baiwa sosai duk da ba mugun kyau gareta ba amma tana da nata sirrin, sannan kuma daga gidan mutumci ta fito, kuma tana kiyaye  tarbiyyar da iyayenta sukai mata, a halin  yanzu ansaka bikinsu da Sulaiman Saura wata d'aya jal a d'aura aurensu.

   Kafin zuwan su Sulaiman sai da ta sanarwa Umma mahaifiyarta akan zuwansa, kaman yanda al'adar gidansu yake hakan aka k'ara gyara mata sitroom wanda ke kusa da dakunan yayyenta maza, ta kintsa komai yanda ya dace inda ta tanadi snacks da banana shake don sauk'ar bakin nata.

Bayan wasu Awoyi

Sulaiman yazo da Hamza inda Hamza daya k'agu yaga wannan halitta da Sulaiman ke zuzutawa ya ware ido tas yana nazarin Zainab, ya yaba kam baiga laifin abokin nasaba na son da yake mata, sai dai ya zaci zai ganta kamannin larabawa, dan idan Sulaiman yana fad'a maka ita dauka zakai ba d'aya a tribe d'in Africa ta fito ba, kanta sunkuye take amsawa  Hamza hirar da yake sako mata,  ba kunya Sulaiman yake zungurar Hamza sanda ta ke ajiye masu plate na drinks gaban su yake ce masa " Ya ka ganta? Yanzu nasan ka yarda da abinda nake fad'a maka" a kunnenta "Hmmn" kawai ta furta don ta saba da hakan, shikuwa Hamza sanin tana wajan yak'i bashi amsa sai murmushi da yayi, ya lura taji maganar ana shi  tunanin Sulaiman baiyi don tajiba, tana komawa tana zama kan kujera sai Sulaiman yace " Kinji ina tambayarsa yak'i baki marks kisan zaman da zakiyi da shi" yana kallonshi da sigar zolaya, hakan yasa Hamza yace " Ai ta girmi marks don ko A na bata na karya mata daraja, amaryarmu sai dai nace Allah ya tabbatar da Alkhairi" amsawa sukai gaba d'aya itakam sai d'an murmushi take na kunya, sun jima suna hira a junansu suna sakata tana bada amsa jefi-jefi.

RASHIN SIRRU (sharrin abokai) Where stories live. Discover now