Part 18

256 8 0
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭

1️⃣8️⃣
Su Mummy duk suna tsakar gida suka shiga kusan a tare suka gaggaisa da en gidan da surukan M Hafizu sannan Baffan nata ya kalli Goggo Lari bayan sun d'an kebe yace "Jibi fa zasu koma kuma yanzun nan Khamisu ke fad'a min da su Immileey zasu koma da nai magana zai min rigima kinsan halin sa dai."

Goggo Lari tace "Toh ai ni ba tafiyar bace matsala,bana jin tafiyar sam don nasan zasu samu kulawa aa dangin Turajo nakeji,ko zasu bari ayi musu nisa da d'iya?"

Baffah Hafizu yayi shiru can yace "To babu fa yanda aka iya da Khamisu gaskiya kuma abinda ya fad'a gaskiya ne sai yarinya tayi hankali ta zabi inda zata zauna don haka inaga kawai ki tura a sanar dasu nima zanje na samu mahaifin sa da kaina gobe,na sanar dashi."

Goggo Lari tace "Aa ai basai na tura ba indai kaje ya wadatar daman ai zancen ma na maza ne."

Baffah Hafizu ya jinjina kai yace "To shikenan sai ki farai musu shiri ai."

Tace "Toh."

Ya fice ita kuma ta kira Immileey sai Innah Aziza da takewa kallon d'iya don er qanwar tace suka zauna ta dubi Immileey tace "Yanzun nan da baban ku ya fita zancen komawar ku yake."

"Komawa kuma?" Suka tambaya a tare cikin mamaki.

Ta jinjina kai sannan tace "Eh! baban ku Khamisu ne yazo masa da zancen d'azun kuma ke Immileey kin sani ba ta yanda za ayi ya musa masa don haka ya amsa masa kuma jibi zaku wuce amma ni sai nayi tunanin ya barku zuwa wani satin su Fiddausi su raka ki kiyi yawo arba'in idan yaso sai ki koma amma ban gayawa fa baban ku ba na bari ne idan munyi zancen sai in fad'a masa."

Immileey tayi shiru tana tuna rashin mutunci irin na Lameen da tsawar da yake daka mata ta tabbatar idan yayi da wannan jaririyar a wajen matsala za a samu sai tace "Nidai gaskiya Innah bana son komawa."

Duk suka kalle ta da mamaki kana Goggo Lari tace "Badai zaki ce sun miki wani abu ba zuwan kin nan don kinyi kyau kin bulbul dake don haka saidai kiyi haquri babu zancen cewar baza ki koma ba tunda baffanki ya amsa masa kuma ko bai ma amsa ba kinsan halin Baffan ku na binni d'aukar ki zaiyi don da ya so d'aukar me sunan sa kuma bai samu dama ba ke kuma wannan qaddarar ta gifta miki gara ma kiyi tafiyar ki don kinsan Allah kika zauna anan aure ma sai ya gagare ki musamman da yake Ladingo ta saka miki ido fiye da komai kinsan kuma halin kutungwilar ta da shige shigen ta."

Tayi shiru tana nazari,da gaske ne dai da babu gwara ba dadi kuma acan Lameen ne kawai shima sai sun had'u nan kuwa dubban mutane ne ba kuma tasan yanda zatai dasu ba don haka tace "Toh Innah Allah ya bamu zaman lafiya."

Duk suka amsa da amin kafin Innah Aziza tace "To nadai san baki da matsala qanwata amma don Allah ki qara zama ta gari ki kare mutuncin ki ki kuma zauna dssu lafiya da zuciya d'aya yanda suke son kinnan kada ki bamu dasu kunya kinji er qanwa ta."

Tana dariya tace "Toh yaya ta bazan baki kunya ba."

Duk suka yi dariya sanda Ilah ya shigo yana kwada kiran Aziza,ta miqe ta fice haka Goggo Lari ta qara tata nasihar da ban baki da fad'a suna yi suna had'a kayayyakin su har suka kusan gamawa lokacin aka kawo Hauwa'u taci kuka ta gode Allah don tana can wajen matar wan Immileey Saratu sai da taga baza ta haqura ba tasa aka kawo ta.

Ta karb'e ta tare da fara lallashin ta don Goggo ta hana ta bata nono idan tana irin wannan kuka saita fara lallashin ta tukunna,dake mai haquri ce ba a jima ba tunda taji dumin uwar ta tayi shiru tasa hannu a baki sai ta zare mata ta shiga bata nono,duk abinda take Goggo Lari na kallon ta ita kanta da ta haife ta ba qaramin alfahari take ba da Immileey ta kasance jininta barin yanzun da take kallon ta tana shayar da jaririyar ta tana d'an goge mata zufar da takeyi lokaci lokaci ta nutsu sosai sai ta burge ta sosai.

Haka ta cigaba da koya mata dabarun rainon jaririyar har ta gama shayar da ita ta bata ita ta qarasa tattara abinda bata had'a ba sai en kayan su da zasu sassaka.

Baffan ta na dawowa Goggo Lari ta sanar dashi ya fad'awa Alhaji Khamis yayi haquri ya qara musu kwana biyu saboda suyi yawon arba'in.

Ya sanar dashi yace babu komai suma zasu qara sati saboda zancen auren er qanwar sa daya taso dole sai yaga me za ayi tukunna.

Haka suka cigaba da shiri,washegari aka ma Immileey qunshi aka sake tisa na Baby Eve,sunyi kyau abun su ba kamar Immileey inka ganta sai ka rantse ba ita bace ta haihu gabad'aya ta sauya ta qara girma da cika ido tubarkallah idan kuma tana shayar da Baby Eve sai ka rantse da Allah wata cikakkiyar macece mai girman shekaru abun gwanin ban sha'awa.

Haka sukayi arba'in suka zaga dangi sosai kwana hud'u suna zagaye dangin su sannan ana biyar sukaje gidan su Turajo wanda da shine suka rufe zagayen.

Tunda tabar gidan yau ne rana ta farko data koma shi,ta kalli d'akin su dake kusa dana Yafendo ta faki idon Jannah ta share hawayen ta wani abu na dawo mata a rai ita kad'ai tasan irin rashin da tayi,kuma ita kad'ai zata ce an wa rashi kusan kowa ya koma yanda yake ita kad'ai ya rage ta gane ta yarda kuma Turajon ta ya tafi kenan ba kuma zai dawo ba.

Zuwan ta ya dawowa da mutanen gidan mutuwar Turajo sabuwa fil musamman Yafendo kasa riqewa tayi suka had'u sukayi ta kuka sun jima a gidan kafin suka fito suka tafi,wannan karon Ladingo kanta saida taji wani abun ta dan tausayawa iyalan na Turajo don rashin miji ko uba ba qaramin tashin hankali bane ta sani shiyasa ko maganganun data saba yau batayi ba.


Don't forget to follow,vote and comment on wattpad.

Still comments na kad'an,this is the last page idan ba a gyara ba.

ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now