EPISODE 2

135 8 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

loadιng...........✍🏻

*RASHIN SIRRU*
(Sharrin Abokai)

Alk'alamin
JANNAH JAY
Wattpad @jannahjay8

Marubuciyar

A dalilin su
Faccala tace
Kuduri ko Manufa
Namijin Kishi

Shafi na Biyu

Tana kwance kanta na kan cinyarsa suna kallo a tv wayarshi tad'auki k'ara, da dan murmushi ya d'auki wayar yayi sallama suka shiga magana a cikin hirar ne yake cewa "lallai kin cika cikakkiyar 'Yar kasuwa wannan zuzutu haka, shikenan ki turo sai ta zab'a ni kuma indai akwai wanda ya mata zan d'auka mata" kallonshi tayi da murmushi tace " Anty Ladi ko?" yace " Kwarai kuwa kaman kin sani kinsan ta da son turo wa mutum kaya ko baka so ba sai ta zuzuta kyansu, wai laces ne ta saro yanzun zata turo sai ki
Zaba" tashi tayi ta rungumeshi " Nagode Sweet Ish" shafa gashinta yake da hannunsa yana cewa " Ba godiya tsakaninmu beside banda zumudi kinsan kalarsu ne kika fara godiya?"
"Kaima kasan duk wata kyauta daga gareka abar godiyace a wajena sannan koya yake zata burgeni" ganin alamun messages sun shigo mashi ta whatsapp ya bud'e pictures ne na laces din sai ya bata wayar ta shiga zabe sai tayi gaba ta dawo can dai ta nuna wani tace wannan yayi, take ya nuna ma Anty ladi tace masa 35k yake, yace to a ajiye mata sai ta turo account number d'inta, dad'i kaman ya kashe Fadila Allah-Allah take lokacin sallar Isha'i yayi ya fita ta bawa Zubaida labarin an saya mata lace, bazata iya jira a kawoshi bama.

Ishaq na fita Fadila tad'au waya " My half guess what? Yanzu My Ish ya sayamin wannan lace din irin wanda aka tura a group din Bussiness World wanda mukai ta sonshi" da mamaki Zubaida tace " Allah My half gaskiya na miki murna kice zaki gwangwaje, Ish yana ji dake, kiga duk da baku dad'e ba ya saya miki duk da tulin kayan lefenki? Ya kamata yaji d'inki mai kyau gaskiya" cikin jin dad'i tace " Wallahi kuwa kinga bama ni na nuna mashiba tallarshi a kai masa ya sayamin" komi tsaf Fadila ta fad'awa Zubaida tana nuna mata bama rokonshi tayiba on his on yaji zaiyi saboda yana ji da ita, sun jima suna waya har sai da ya dawo daga masallaci bata tashiba, jin zai bud'e kofar falon yasa tayi wuf ta shige bedroom d'inta ta tada sallar.

Karo na biyu da kiransa yasake shigowa wayarta kenan har tayi kaman bazata d'auka ba daga baya ta dauka, tana dauka ya fara magana " Pls haba Baby ya zakice bazaki fito ba? Bayan na fad'a miki mun taho dasu Uzee ne fa kice wai an hanaki fita ni gaskiya ban yarda ba" cike da haushi tace " Naji bazan fito ba an hanani fita balle ka d'ebo gayya har mutum 5, ka basu hak'uri kace an fara mun kulle kawai" jan tsaki yayi yana cije lips dinshi " Pls Baby wannan ne na k'arshe insha Allah" a jiyar numfashi tayi tace " Dont you get it? kai kanka ba'aso ka ganni balle wasu why not su jira Kamu sai su ganni why the rush eh? Nida zan zamo matarka kullum suke gani na ka basu hak'uri" tana wannan maganar Ummanta taji ta jijjiga kai ko ita dai ta karanci halin Sulaiman da kwaso abokai azo gidan, amma sai ta barshi da yanayin zumudinshi kan Zainab d'in tace " Tunda dai da wasu kar suga kaman wulak'ancine saka Hijab d'inki kije ko kya samu ki dawo da wuri mai turaren har tazo" haka ta tashi tana k'unk'uni ta fita, aikuwa su biyar banda shi tagani nan fa suka shiga surutu tana amsawa dai sai da tasami awa d'aya wajansu ta koma, tana shiga gida ya tura mata text " Thanks Baby.. Muah" ajiye wayar tayi batare da reply ba ko cikakken minti uku basuyiba da fara aikin turaren kiransa ya dinga shigowa wayar ita duk kunya sai ta kamata, haka ta danna wayar a silence sannan ta huta.

Bikin Sulaiman da Zee ya taho don yanzu suna cikin satin biki an gama komi na Al'ada da duk wasu tsare-tsare hatta kafun kaya anje Katsina an mata, duk wani wanda Sulaiman yake alak'a dashi a garin Funtuwa ya gayyace shi zuwa shagalinsu, sannan duk wani abun tsare-tsare abokansa ne akai ko abu takeso sai dai ta kira wani a cikinsu, don shi mutum ne daya yarda da abokai d'ari bisa d'ari, shiyasa tun Zee da k'awarta Humaira suna jin nauyinsu har sun fara sabo da su. Zasuyi Kamunsu a nan Funtuwa amma dinner sai an kai amarya a can Kt zasuyi.

RASHIN SIRRU (sharrin abokai) Where stories live. Discover now