Part 19

309 21 0
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭


1️⃣9️⃣
Koda suka dawo gida ma daki ta shige ta cigaba da kukan da take don ko tayi shiru idan ta tuna yanda Turajo yake sai ta sake fashewa da kuka haka tana jin Baby Eve na kuka amma taqi karban ta.

Mooha ne ya karbe ta ya bita daki tana kwance ta rumgume pillow taci kuka har taji ba dadi cin zuciya kawai takeyi yace "Karb'e ta Khadija ki bata abinci."

Maimakon ta karb'e tan kamar yanda yace sai ta fashe da sabon kuka tana cewa "Don Allah ku qyaleni na gaji ku qyale ni."

Ya zauna a kujerar dake fuskantar gadon yana kallon yanda jijiyoyin kanta suka tashi sukai rudu rudu saboda kuka yace "Wai wannan kukan da kike na meye?"

Ta d'auke kanta daga kallon su da take ta cigaba da goge hawayen ta bata kula shi ba,ya jima yana kallon ta kafin yace cikin sanyin murya "Yi haquri Khadijatu ki karb'e ta don Allah,baban ta bazaiji dadi ace kina azabtar masa da d'iya da yunwa ma inda zai dawo."

A hankali ta miqe ta karb'e ta ta gyara mata kwanciya kan ta kalle shi tace "To fita zan bata."

Murmushi yayi don ta burge shi ba kad'an ba duk da qanqantar ta ta san qima da darajar jikin ta sabanin wasu matan da ko a kasuwa sai su ba jariri abinci kamar karnuka,sam ba ladabi kuma a tsammaci yaron zai tashi da tarbiyya da da'a alhali ba a koya masa ba.

Ya miqe ya fice ita kuma ta soma shayar da Hauwa'u tana kallon ta tana hawaye,tausayi da son yarinyar na qara shigar ta haka har ta qoshi tayi bacci,ta zare ta ta kwantar da ita a gefe sannan ta miqe ta qarasa had'a musu kayan su na tafiya tana yi tana share hawayen da suka qi tsayawa muddin zata kalli fuskar d'iyar ta sai taji Turajo da ciwon rashin sa ya dawo mata sabo fil.

Wajen magriba suna zaune a d'akin Goggo Lari suna hira,Immileey na gefe,Hauwa'u na bayan Innah Aziza Mooha ya shigo,Amnah tace "Hammah Mooha ina mummy."

Ya kalle ta yana murmushi yace "Tana gidan Innah Amina mana in zakije saidai ki tafi yanzu keda Cutie."

Ta girgiza kai tace "Aa gobe ma had'u."

Yayi dariya yace "Na sani ai daman abinda zaki ce kenan tunda kuka zo kuka samu Baby Eve shikenan kuka yaye zaman gidan Innah Amina zakuma kuje ku same ta kunsan halin ta sarai."

Jannah tace "Ahap,sai muyi mata shiru ta qaraci sababin ta."

Dariya duk sukayi yace "Au sababi ma takeyi kenan."

Tayi dariya itama tace "Ai Innah Amina halinta sai ita."

Goggo Lari tace "Aa wai uwar tamu kuke yiwa wannan abun kufa kiyayeni."

Duk suka sa dariya,duk abinda akeyi Immileey na gefe ko dariyar bata taya su yana lura da ita tunda ya shigo bata dago ba balle ta kalle su tasan me sukeyi don haka ya miqe yace "Immileey zo muje waje."

Suna fita Jannah tace "Uhmm Cutie kenan."

Amnah tace "Menene?"

Jannah tace "Ina ruwan ki dani bana son gulma."

Innah Aziza tace "Ya isa dai."

Jannah tayi dariya kawai suka cigaba da hirarrakin su da Innah Aziza.

Tsakar gida suka fita suka zauna kan kujeru en tsuguno da aka kawar gefe aka had'a su waje guda Mooha ya kunna fitilar wayar sa ta haske koina a tsakar gidan saida ya kalle ta na tsahon lokaci kafin ya fara magana a hankali "Khadija."

Ta d'ago ta kalle shi cikin sanyin murya da sarqewa ta amsa "Na..Na'am."

Saida yayi murmushi sannan ya cigaba "Shawara nake son baki akan wannan damuwar da kika saka kanki,an sani ko mutuwar qawa ko aboki na tab'a mutum balle miji wanda kuka shaqu amma ki sani ana son mutum ya zama mai tawakkali da miqa lamuran sa ga Allah,da wannan kukan da hirji da salati ki ka kama da duk ba haka ba,kuma Turajo a yanzu bazai so wannan kukan da kike masa ba don ba so bane kukan ki azabtarwa ce a gare shi addu'ar ki yake nema ita zaki yi masa yasan kina son shi,bayan haka me kika rasa?iyayen ki da en uwan ki suna bakin qoqarin su wajen kulawa daku wannan kukan kina tsammanin ba karya musu gwiwa zaki dinga yi dashi ba su dinga ganin sun gaza ne?kina son su riqa damuwa da gazawar da kike nuna musu sunyi?"

Ta girgiza kanta alamu Aa.

Sai ya cigaba "To in har bakya so lokaci yayi da kuma zaki maida lamuran ki ga Allah,gaki da qananun shekaru so kike ki kashe kanki da wasu cutukan,kuma dai wannan kukan naki bazai dawo da Turajo duniya ba dole ya tafi kenan,kuma Allah kad'ai yasan meya tanadar miki anan gaba Allah kuma baya jarabtar bawan da baya so don haka ki gode masa ki miqa lamuran ki gare shi sai yayi miki sakayya da mafi alkhairi."

Ta jinjina kai tana sheshshekar kuka,da gaske ne duk abinda ya fad'a Turajon ta ya tafi kenan bazai dawo ba ko hawayen ta zai qare kukan ta bazai sa ya dawo ba kuma gaskiya ne ansha fad'a musu mamaci baya son kuka ko a makarantar su don haka tace "In sha Allah na daina zan dinga masa addua kullum."

Yayi murmushi tausayin ta na sake kamashi har yanzu da yarinta a tare da ita,don haka yace "Yauwa yarinyar kirki haka ya kamata kiyi ta masa addua kuma kina addu'ar Allah ya raya mana Baby Eve."

Ta kautar da kanta tana share hawayen ta kamar batasan me yace ba.

Dan murmushi yayi yace "Tashi kije ki kwanta gobe da wuri zamu wuce."

Ta miqe jiki a sabule har tayi nisa ta juyo a hankali tace "Nagode."

Murmushi yayi ya jinjina kansa alamun yaji sannan ta juya ta cigaba da tafiya harta shige yana kallon ta,ya jima zaune a wajen kafin ya miqe yaje yayi musu saida safe ya wuce gida.

Ko wajen su Mummyn sa baije ba d'aki kai tsaye ya wuce kai tsaye yayo wanka yazo yayi nafilar da yake kullum kafin ya kwanta sannan ya kwanta d'in.

Tunanin sa kacokan na kan Immileey ne,ya amincewa ransa yana son ta zuwa yanzu saidai shi a qa'idarsa yana son auren aqalla wadda koda level 2 ne ta gama kuma a qalla shekarun ta sukai sha tara zuwa ashirin,Immileey ko duka duka yanzun take kammala sha biyar bayan haka yanzun ma ta haifi d'iyar ta sannan tana buqatar lokaci kafin ta saisaita nutsuwar ta tace zata sake karban wani d'a namiji a zuciyar ta in akayi la'akari da yanda take kokawa akan rashin mijin ta kasan tayi missing d'insa sosai,lallai tana buqatar lokacin da zata saba zuwa gaba don haka take ya yanke a ransa zaiyi yanda zaiyi in sun koma ta koma school daga nan zai fara gina soyayyar sa tunda ta tab'a aure da soyayya yasan komai zaizo masa da sauqi akanta da ire iren tunaninnikan nan yayi bacci saida asuba ya farka.

A b'angaren tana shiga ta wuce d'aki kai tsaye ta kwanta kan gado gefen Hauwa'u tana kallon ta tana tuna maganganun Mooha tana kuma gasgatawa zantukan sa,ta tabbatar gaskiya ne duk abinda ya fad'a a lokuta da dama tun kafin tayi aure maganganun sa na mata kama da na Turajo kusan yanayin su d'aya saidai wayewa bazaka had'a suba haka zalika baza ka had'a su wajen ilmi ba bata sani ba ko Mooha nada ilmin addini sosai amma tasan Turajo nada shi sosai kusan ire iren wad'annan sune banbancin su amma bayan haka wajen iya tsara magana da zance suna kamanceceniya a wajen furta su a hankali da wannan tunanin itama bacci ya d'auke ta wanda saida taso makara da asuba.



ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now