DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
2️⃣0️⃣
Washegari qarfe shadaya suka dauki hanyar kano,kafin su tafi Baffan ta ya kira ta dakin sa taje ta same shi yana jan casbaha kamar yanda ya saba bayan yayi walha ta samu waje ta zauna har ya gama addu'ar sa sannan ya juyo inda take yace "Khadijatu."Kanta na qasa tana wasa da zoben azurfa dake hannun tace "Na'am."
Yace "Er nasiha na kira ki na qara yi miki,bana jin ki nasan baza ki kunya ta ni ba amma tunatarwa bata da laifi,ki sani rayuwar binni data qauye ta banbanta,kalar wayewa yanda ake cudanya da juna da komai ba irin namu bane,don haka ki kiyaye kinsan yanzun ke duk da a shekaru yarinya ce amma a yanayin rayuwa kin girma tunda har d'iya ke gareki gata nan marainiya,idan baki kiyaye don kanki ba don girman Allah ki kiyaye don d'iyar nan marainiya kinji ko?"
Ta jinjina kai idon ta na cikowa da hawaye.
Ya cigaba "Sannan ki sani tsakanin halshe da haqori ma ana sab'awa balle mutum da mutum,mutanen nan sun nuna miki qauna sosai ba su ba ba ahlin su ba,don haka ki zama mai haquri da kawaici kiji kiqi ji ki gani kiqi gani duk abinda za ayi miki kada ki taga kinga dai daman ba a tab'a cewa mai haquri ya muzanta ko haqurin sa ya qare ba don haka na hore ki da haquri,kawaici da sanin ya kamata,sannan ki riqe ibada da addu'a a kodayaushe,Allah yayi miki albarka ya raya wannan d'iya taki ya baku zama lafiya tashi kije."
A hankali muryar ta na rawa tace "Nagode Baffah kuma InshaAllah bazan baka kunya ba."
Ya jinjina kai alamun gamsuwa sannan yace "Allah ya baki iko Immileey."
Ta miqe ta fice tana jin wani iri a ranta,lallai barin iyaye babu dadi don ita a duk sanda zata barsu bata jin dad'in hakan saidai ta tafi kawai don dole,ta barsu na farko da sunan aure yanzu ta barsu na biyu da sunan riqo Allah ya bata ikon haquri da juriya da zaka da iyayen goyonta,a fili ta furta amin.
***
Lameen na kwance kan gadon sa yana kallon film a system d'insa,nishadi yake ji sosai don yana son film d'in baya kuma gajiya da kallon sa yaji shigowar motar tasu.Ya miqe da sauri yayi waje yana fara'a yana fad'in "Oyoyo ga Mummy na oyoyo."
Ita ta fara fitowa da Baby Hauwa'u a hannun ta tasha kayan sanyi farare tubarkallah sai baccin ta take,ya qare mata kallo tsap kafin yayi magana su Immileey sun fito amma ita maimakon ta tsaya kamar yanda Jannah da Amnah sukayi sai ta wuce su ta shige ciki,ya bita da kallon mamaki sannan ya maido hankalin sa kan Amnah dake ta fad'in "My Jaan nayi missing d'inka."
Hannu ya bata suka tafa da gaisuwar daya koya mata tuntuni sukeyi yace "I missed you too My Jaan."
Ta jawo hannun sa tana sake cewa "My Jaan baka ga Baby Eve ba mai kyau?"
Ya sake kallon hannun Mummy,tabbas babyn ko ta waye mai kyau amma dake yasan daga inda suka fito sai yayi fuska harda yatsinewa yace "A ina kuka samo Baby ku kuma?"