*Auren Ba'ame*
Xaune Take a Tsakiyar Falo Cikin Shigar *Indian Gowns* Bisa Doguwar Kujerar dake kallon Qofar dake Fitar da mutum daga Falo din xuwa Side din Ummansu, Dora Qafar dama Tayi akan na hagu Tare da mayar da natsuwarta gaba daya kan wayar dake hannunta Wanda Take Kirar *iPhone 11 Pro Max*, Kallo daya zaka Mata Ka Gane Cewa Cike Take da Annushuwa, domin a wasu lokuta har Nakan Jiyo Sautin Dariyarta Qasa-Qasa.
Chatting Take cikin Wani Group Dinsu Me suna "Zumunta" Wanda Yake na Abokan Karatunta a Jami'ar Kaduna State University Wato(KADSU).
Da Qarfi Taji Ana Kwalla Mata Mata Kira, Aunty Ramlat, Aunty Ramlat, Mikewa Tayi don Ganin Wacece ke Mata irin wannann Kiran!
Qawarta ce Khairat Ta Shigo Tana Fadin Abba na Son Ganinki, Tace To Gani Nan.
Hijabi ta dauka Ta Yafa Sannan Ta Kama Hanyar Shiga Bangaren Abbansu, ba Jimawa Ta Iso, Isowarta keda Wuya Tayi Sallama Aka Mata Ixni Ta Shiga, Sannnan Ta shiga.
Alhaji Isma'il Harris Ne Xaune Kan Kujerar Tsikiyar daki Rike da Jaridar *Almizan* Yana Karanta Labarun Sati, Yayinda Hajiya Maryam Uwar Gidan sa Ke Kallon Maimaicin Shirin *Hukumce_Hukumcen Azumi* Wanda Sheikh Muhammad Auwal Ke Gabatarwa.
Neman Wuri Tayi A gefe Can Jikin Ummansu Ta Lamushe Tamkar wata Magen da Taso Yin bacci, ABBA Ina kwana! Ya Amsa Cikin Fara'a Lapia Lou Yar gidan Abba, wato kedai baxaki Girma da Hawa Jikin Ummanki ba Ko? Ko baki San Kin Girma Bane?
Maimakon Amsa sai Tabe baki Tayi Tare da Qara Mannewa Jikin Ummansu Tace Ni Bana Girma da Jikin Mummyna, dariya suka Saka dukkansu, Sannan Bayan Shiru Ya Gifta na wasu Yan Minute Alhaji Ismael Harris Ya Waiga Bangaren da Ramlat Take Yace;Dama na Kiraki Ne saboda Dalili biyu.
Jiya "Chancellor" Na Makarantar Ku Ya Kirani Yace Zaa Koma Hutu On Next Coming Monday, So Ga kudi Ki Fara Shirin Komawa School On Sunday.
Ta Karba Kudin Cikin Girmama Wa, Kudine masu Dan kauri Wanda Nidai Na LeQa amma Ban Iya Gano Muku Adadinsu ba.😉
Sannan Ya Cigaba da cewa: Kinsan Cewa Zakuyi Graduated On December This Year ne Ko? Tace Hakane abba, Yace to, Nayi Magana da Ummanki cewa In Time din ya Qara Matsowa Xamu Tsaida Lokacin Bikinku Keda 'SADIQ', Raf,Raf, Haka Xuciyarta Ya dauki Bugawa,
Cikin Dan Lokaci Hawaye Ya Fara Neman Zartuwa a bisa Kuncinta, Cikin Gaggawa ta Fakaici Idonsu Ta Share shi, Yayinda Kanta Ke Kasa.Kallonta Ummansu Tayi Tace; Yar Gidan Umma Meya Faru! Ko Auren ne Bakya So?
Cikin Muryr dake alamta kuka Na Gaf da Kufce Mata Tace A'a Mummy Banasan Rabuwa da Ke Ne!
Tashi Abbansu Yayi ya shiga Ciki Yana Fadin Wannnan Bansan Yaushe Zaki Girm ba
Baki Hajiya Maryam taci Gaba da bata tana Fadin haba Yar Mama, bakiga Cewa You Have To be Mother Ba ne,Kalleki fa Kyakykyawata, Ai Nima bazanso Inga Kinci Gaba gaba da zama A gida ba alhali Kin kammala Karatunki,Kuma Kinga Nima Inason Inga Yan Jikoki Na Ta wurinki, Cikin Zolaya Tace Fatar 'Yarki Mace Ta farko zaki Saka sunana Umma Ko? Hakan Yasa Ramlat Nemo Murmushin dole Tare da Girgiza kai Alaman A, Daga nan Hajiya Ta Mike ta Shiga daki ta barta anan.
Ynkurawa Tayi da Nufin Mikewa, amma bisa Mamaki Taji Jiri ne Ke Dibarta, cikin Halin Qarfin Hali Ta Mike Ta Nufi dakinta Yayinda Zuciyarta Ta Manta da wani Abu Me Suna Farin Ciki, Tambayoyi Takewa Kanta Yanzu Ya Zanyi da Soyayyar 'HABIB', Shikenan Zanrabu da 'HABIB'? Shikenan Na Rasa Kulawar HABIB? A wannan Lokaci Ta Barke da Kuka me Motsa Zuciya Tare da Fadawa Kan Gadonta Bayan Shigowarta Daki, Kuka Take Sosai iya Kan Iyawarta, Yanzu Taya Zata Gayawa Iyayenta Cewa Bata Son 'SADIQ' Alhalin Ansan Suna Soyayya Tun a Rayuwar 'FUDIYYA' A Yayij Yarinta, Saida Yanzu Sam Kurciyar Soyayyarta Ya Tashi daga 'SadiQ' Ixuwa 'Habib', Hawaye Me Zafi Ya Sakko Mata Yayinda Ta Tambayi Kanta Cewa! Taya zan gaya wa su Umma Cewa 'Habib' Nakeso? Kuma Taya Zan Sanar dasu cewa 'habib' BA'AME Ne ba dan Uwa ba?
Ringing din wayarta Ne Ya Katse Mata Tunani,Ta Share Hawatenta, Sannan Ta Mika Hannu Ta Dauko Wayarta
"MY HUBBY" Sunan da aka Ya Bayyana akan Fuskar wayar kenan, Wanda hakan ya Tabbatar min cewa 'HABIB' Ne Ke Kiranta.Daga Wayar Tayi Ta Dora a Kunninta Tare da Fadin 'Helo'
Oh My God What's Going On Dear Na? Kalmar da Ya Furta kenan yayinda Yaji Muryarta Alaman Tayi Kuka.
Bakomai, Kalmar Data Furta kenan, Ya Bata Rai Kaman Wanda Dagaske Yace 'Babyna In baki Gayamin ba, Nayi Alkawari Bazan Ci Abinci ba Har 2 Days'
No No My Princess Kabari To On Monday Zamu Hadu a Makaranta Zan Fada Maka.Nan Suka Cigaba Da Hira Irin Ta Masoya,Wanda daga Nan Bansake Gane me Suke Cewa ba Nima.🤫
Tin Bayan Kashe Waya Sadiq Ya Fada Kogon Tunani Yana Tambayar Kansa Meke shirin Faruwa Ne? Kardai ace duk wannan Waiting din da yayi don Cimmawa Boyayyiyar Muradinsa Yana Neman Zama a Banza? Ko an Gaya Mata cewa So Yayi Yayi Izgilanci ga Mazhabarta(Shi'a)? Nan Yaji Ya Qagu Sosai Monday Tayi don Jin meke Faruwa.
Ramlat Kuwa Tun Bayan Kammala Wayarta Ta Fara shiri domin Fita Zuwa Kasuwa, Doguwar Riga ce Fara Ta Sanya Tare da Dora Red Hijab Wanda Yake Anko dinsu Ne Na 'FATIMIYYA' Tayu Rolling Dinsa Ya Tsaya a Iyakan Kafadunta,sannan Ta Jawo Waya, Khadija M Husain Takira, Ringing 1 Aka Daga Wayar
Tace Khadija Mu Hadu a Markaz Wurin Zama Inaso muyi Magana bayan an Tashi, Meya samu Muryarki Qawata? Kadija Tayu Tambaya, Ajiyar Numfashi Tayi sannan Tace Mu Hadu Zakiji meke faruwa, sukayi Sallama Suka kashe Waya.
Madubi Ta Duba taga Dress dinta Sosai ya Mata kyau, Murmushi Taja Gami da Ajiyar Numfashi sannan Ta Fita, Kofa Ta Tasarwa Zata Fita, Muryar Ummansu Taji Tana Kiran Sunanta.
Sai Ina Kuma Ramlat? Xan Shiga Markaz ne wurin Zama Sannann Zanwuce Kasuwa wurin Siyayan 'Provision' na Koma School.
To, a Dawo Lapia, kuma kar a Dade Kinsan Yau Alhamis Abbanku da wuri Yake dawowa.Insha Allah Umma, Ta Fada sannan Ta Saka Kai Ta Fita
Ta Nufi Markaz Don Tattaunawa da Kadija Kan Matsalolinta.Xamu Cigaba....