Part 21

462 26 0
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML

*Assalamu'Alaykum warahmatullah,Hw r u all?i hope all is well,am not here to sorry u guys for dadewa da nayi banyi posting ba,nayi ne saboda nayi warning dinku, am here to let u know wannan shine page na qarshe idan baku gyara ba,donna ga baku san zuru ba almost all of u guys are taking what u have for free for granted bakwa darajta shi,idan da littafin da zaku biya ne zaku nema ko kuma wanda za a ja muku Allah ya isa duk zaku nema har ma wani prouding wasu daga cikin ku ske yi,to na gaji bazan dinga bata lokacina amidst all my schedules ina muku abun da bakwa appreciating ba,this is the last page i repeat idan baku gyara ba,am sick and tired of yi muku kara bakwa fahimta.*


2️⃣1️⃣
Kwanciya tayi a gadon su itada Jannah da suke kwana tana kallon Amnah dake ta kici kici da gashin da yayi mata yawa wajen taza,can dai tace "Wai kije Mummy ta taje miki mana."

Ta zumbura baki kamar zatayi kuka tace "Idan Mummy ta kama gashin nan bata yi min ta dadi gaskiya gara Sabuwa."

Tace "To kije Sabuwan tayi miki mana."

Ta miqe da mai da comb tace "Bari naje don na kasa wallahi."

Murmushi tayi don ita kanta nata gashin har yanzun bata iya taje shi da kanta a hankali ta d'an soma bacci har ya kwashe ta gabad'aya don daren jiya Baby Eve bata barta tayi baccin kirki ba gashi suka tashi da wuri don tahowa.

***
Mooha na harabar gidan yana ta wasa da Baby Eve shi kad'ai yake ta faman dariyar sa,abokin sa Muzammil ya shigo ta qofa.

Kai tsaye wajen sa ya nufa yana fad'in "Kaii mutumina irin wannan qiba kamar ba daga qauye ka dawo ba?"

Daure fuska yayi yace "Bana son wulaqanci kasan ni fa ba abinda na tsana irin ka kira garin mu qauye ko?"

Muzammil yace "Ha'a see me see this guy oo meye in ba qauyen ba."

Lameen dake fitowa yace "Ai shi baka cewa wannan kufan qauye yanzun zaku hau sama ku fad'o."

Murmushin gefen baki yayi irin na takaicin nan yace "Idan ana irin wannan maganar don Allah ka daina saka baki don da masu darajta mahaifan su ake yi ba kai ba."

Miqar da Baby Eve ta fara kamar zata fara kuka yasa ya d'aga ta yana cewa "Kefa idan baki ga dama ba rigima ce dake ki bar maman ki ta huta don Allah."

Muzammil yace "Ina ka samo baby mai kyau haka?" Ya fada yana karban ta,ita kuma kamar tasan an canza mata hannu ta tsala ihu da sauri ya mayar masa da ita yana cewa "Heyyy easy mana,chill."

Dariya Mooha yayi ya sata a kafad'a kafin yayi magana Lameen ya riga shi da jan wani wawan tsaki kafin yace "Aikin banza kawai kun cika mana gida da en qauye kuma hakan bai ishe ku ba sai kun d'auko baby mai jarabar kuka ta hana mutane sakat."

Mooha yace da Muzammil "Zo muje na mayarwa da Mummy Baby Eve mu fita ka raka ni wani waje."

Muzammil ya bishi,suka kai ta suka dawo suka fta a motar Mooha bayan ya shigo da tasa ciki.

S hanya Muzammil ya sake cewa "Don Allah babyn waye wannan babyn so nake naga mamanta nasan za ayi kyakkyawar mace a wajen."

Mooha yaji wani maqaqin kishi ya taso masa da jin haushi yace "Waikai meye damuwar ka ne?maman ta nada aure kuma in da rabon zaka ganta zaka ganta mana karka dameni."

Abun ya bashi mamaki amma yasan halin Muhammadu bamai fushi bane yasan dole akwai abinda ya faru kuma yasan shi kansa bai kamata ba abinda yayi don tunda yaga wannan danyen jegon yasan zaiyi wahala matar ba mai aure bace amma haka kawai ransa yake kwadaita masa ganin ta amma yasan shaidan ne sai ya fara neman tsarin ubangiji daga shaidan yayi qoqarin canza maganar da ta business din da suke shirin farawa ta gyad'a da auduga.

Nan kuwa yaga sakewar Mooha ya koma Muhammadun daya sani dama can take ya sawa ransa akwai abinda yasa Mooha yayi abinda yayi amma sai ya share yasan duk daren dadewa zai san halin da ake ciki.

***
En makaranta nata shirin komawa makaranta hutu ya qare monday duk zasu koma hakan yasa Mooha samun Alhaji Khamis da daddare duk ana zaune duk gidan yace "Abeey ni wani tunani nake."

Ya maida hankalin sa kansa yace "Inajin ka Muhammadu."

Ya sake gyara zaman sa kan ya cigaba "Inaga tunda Baby Eve ta kusan watanni biyu en kwanaki ne babu Immileey zata iya shiga makaranta tunda kullum shekarun ta qara ja suke gara ta kammala duka kafin ta gama Baby Eve ta girma."

Abeey yayi murmushi yace "Nima tunanin da nake kenan amma sai nace idan ance Khadijatu ta tafi makaranta ita kuma Hauwa'un fa wa zai dinga bata abinci tunda tayi qanqanta da abinci."

Lameen dake jinsu ya d'aga kai da sauri yana kallon Immileey dake wasa da pencil a hannun ta ya maida kallon sa kan Baby Eve dake hannun Mummy tana ta wasa irin na jarirai yarinya bul bul da ita tubarkallah,kawai sai ya tsinci kansa da maimaita "Wannan yarinyar wai da gaske itace ta haifi wannan babyn?amma tayi qanqanta ai." Haka yaita fama da zancen zuci.

Mooha yace "Sai a siyo mata madara kafin tayi wata hud'u ta koma cerelac ko frisocream."

Ya jinjina kai yace "To hakan yayi sai a nemi mai raino Mummy wadda zata dinga yin da ita kafin uwarta ta dawo."

Mummy da tun fara maganar bata sa baki ba tace "Aa haba Abeey,er wannan ai zamu zauna abun mu daman nayi missing raini sosai."

Yace "To ko zakiyo en biyu ne?"

Ta waro ido tace "Ni er haihuwa,ba haka nake nufi ba."

Duk suka sa dariya ya miqe yana kallon agogon falon yace "To kowa yaje ya kwanta gobe school gara a tashi da wuri kema Immileey ki kwana da sanin gobe zaki shiga school."

Ya jinjina kai cike da jin dad'i tace "Nagode Allah ya qara girma da wadata."

Cike da jin dad'i duk suka amsa mata da Amin.

Tunda ta canzawa Baby Eve pampers ta kwantar da ita saman cikin ta tana shafa bayanta yarinyar tayi bacci ita take faman kallon ceiling da tunani kala kala.

A ranta take fad'in "Daman bahaushe yace mutuwar wani tashin wani." gadai Turajo Allah ya masa rasuwa ita kuma gashi sanadin cigaba rayuwar ta kenan,inda Turajo na nan ita kanta ko tunanin makarantar baza tayi ba don ba al'adar su bace yin boko saidai tana so sosai shiyasa take da naci wajen yinsa koda yaushe,yanzun gashi ita ce zata je babbar makaranta mai tsada irin ta su Jannah wadda ta tabbatar sai dai yaran yan gayu hamdala kawai ta dinga yi daga baya ta juya ta kwantar da Baby Eve itama ta kwanta tayi musu addua sai bacci.

Bayan sallar asuba Jannah bata koma ba tayi wanka Amnah ma ta shiga tayi qarfe shida daidai suka tashe ta tana ta magagin bacci saboda rashin samun isasshe Jannah tayi dariya tace "Zama ki ware ne yanzun kika fara tashin asuba ai."

Wanka ta shiga tayi tazo ta shirya ta zura doguwar riga baqa mai maroon a jiki ta nade kanta da shi ta sauka qasa ta tarar har Sabuwa ta gama yiwa Baby Eve wanka ta shirya ta cikin riga da wando na babies pink and white tayi bala'in kyau sai raba idanuwa take Mummy tace "Yawwa zauna ki bata kina cin abinci don sai 5pm zaku dawo inta qoshi yanzun da sauqi."

Ta karbe ta hannun Sabuwa tana gaishe ta sannan ta gaishe da Mummyn ta zauna ta soma bata ita kuma Sabuwa ta hado mata abincin ta kawo mata.



ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now