ƁACIN TAH...!

19 1 0
                                    

_*ƁACIN TA..!*_

_MALLAKAR:HAUWA S ZARIA_
                         *(Mman Uswan)*

_*DIDECATED TO*_
  _*MY DAUGHTER*_

*SPECIAL GIFT TO*
*SAHEEBA HAFNAN*

                *🅿️15-20*

"Jiddah tayi mgnr ne haɗi da dafe ƙirjinta"

     "Take ta zare jakar dake goye a bayanta ta shiga tattara falon,tanayi tana tmbyr Ummiy dalili afouwan haka"

   "Wani ɗan tsautsayine kawai Ummiy tace da ita"
   "Kasancewar sanin hali Abbansu yasa Jiddah bata kawo kowa a ranta ba sai Abbansu"

   "Gani harda kwalaben turaruka cikin kayan da suka farfasa yasa Ummiy cewa"Jiddah ta bari kawai zatai da kanta Amma Jiddah taƙi,daga ƙarshe dai tare sukai aikin"

   "Suma ƙannin nata suka sanya hannu suna tayata, suna cikin haka saiga Harira ta fito, subhanallilahi tace"da sauri ta ƙariso wajan haɗi da cewa"su bari kawai zata gyara wajan"

     "Daga fiskan da Jiddah zatayi tai ido biyu da ummiy,cike rawan jikin ta dafe ummiy tana me tmbyrta meya sameta a fiska ya tunbura haka?tana cikin tamy kenan ta sake gani ynda jikin ummiy ya canza alamar tunburi".

   "Rusawa da kuka tai tana me faɗin na shiga uku na lalace,wayyo Allahana"

  "Gani kukan da Jiddah keyi ne yasa su Haneef da Anwar kuka dukkansu haɗuwa sukayi waje ɗaya suna kuka"

     "Duk ynda Harira taso danne zuciyarta Amma abu ya faskara,domin ita kanta batasan da zubowar kwallan ba"

  "Cikin ƙarfin hali Harira ke lallashin su Jiddah,haɗi da boye abinda ke faruwa tsakanita da Abbansu"

      "Sai da sukai shiru snn take tmbyr abinda ya dawo dasu a wnn lokacin?"

     "Jiddah ce ta bada amsa da koranmu akani,,kowa sukai su  bani daga yau zuwa gobe idan ban kawo kuɗi zana jarabawar da zamuyi bazasu sake bari na zauna a ajiba ba""snn ta juya dasu Anwar da Haneef dake tsaye  taci gaba da cewa"su Anwar da Haneef suma Anuty's ɗinsu suce idan har babu kuɗin school feels gwama kawai su zauna a gida domin koda su koma baza'a barsu su zauna a school ba"

    "Innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un,Harira tace"haɗi da sulalewa ta zauna a ƙasa"Jiddah ce ta kuma tmbyr ummiy da lafiya ummiyna?"

     "Babu komai Harira tace"
    "Ta jima zaune tana ƙunbiya-ƙunbiyan ta ynda zata bullowa al'amarin"

    "Daga ƙarshe dai tube uniform din sukai suka zauna a gida"

  "Tun daga lokacin ta shiga ƙunbiya-ƙunbiyan ta inda zata samu kuɗi"

  "Tunda Sabeer ya fita be dawo gidan ba sai bayan goma na dare lokacin duk yara suyi bacci,hakan yasa shima Yana shiga Kai tsaye cikin daki ya shiga yana shiga ya musanya kayan jikinsa zuwa na bacci ya kwanta"

     "Washe gari da safe gani su Jiddah zaune har takwas yayi basu shirya zuwa school ba yasa Sabeer jawo Anwar jikinsa yana tmbyrsa dalilin rashin tafiyarsu school"

    "Nan Anwar ke sanar masa Anty's ɗinsu ce ta koresu snn kuma tace in har babu kuɗi gwama su zauna a gida kawai,domin koda mu koma koranmu zatayi"

   "Da kuka faɗiwa mmnku me tace daku?"

    "Batace komai ba"
"Uhmm yace"snn yai kwafa"

"Jummai dake zaune a office,gani har goma yayi harira batazo ba yasata kiranta domin ji abinda ya hanata zuwa"

    "Jiddah dake riƙe da wayar gani number Jummai ne yasata kaiwa ummiy wayar a guje"

  "Harira na amsar wayar ta kara a kunni haɗi da sallma,bayan su gaisa Jummai ke tmbyrta lafiya yau batazo aiki ba?"

    "Murmushin yaƙe tai snn tace wlh banaji daɗi yasa ban zaba"

    "Subhanalillahi tace,snn ta tmbyeta jikin"

   "Da sauki tace"
  Snn sukai sallma, haɗi da cewa"idan ta tashi aiki zata biyo taga jikin"
"To tace, da ita".

    "Kmr ynda ta alƙawanta tana tashi daga aiki ta biyo, dai-dai lokacin dukkansu suna falo,sallmrta ne ya katsesu da miƙewa sukai su Anwar da Haneef suna yimata sannu da zuwa"

    "Yawwa tace dasu snn ta sami waje ta zauna,bayan ta zauna ne duk suka duƙa domin gaidata,suna gama gaisuwar suka miƙe zuwa ciki,falo ya rage daga Harira sai Jummai"

   "Sannu da jiki tace,snn suka gaisa suna gaisawa idanu Jummai nakan Harira,harata buɗe baki da niyyar mgn saiga Jiddah ta dawo hannu ɗauke da ruwa a goran swan da glass cuo a hannu,tana miƙa mata tasake ficewa daga falon"

   "Sosai Jummai Tasha ruwan sabida zafin data ɗibo a hanya,duk da a mota take Amma be hanata jin zafin rana ba"

   "Tana cire cup ɗin a baki tai hamdali ga ubangiji haɗi da cewa"gsky ana rana"

       "Wlh kuwa,sai nake gani kmr rabomu da zafin rana irin na wnn shekara tun muna yara"

    "Gaskiy kam,dan Allah na tmbyeki mana"

      "Allah yasa na sani"
   "Da gske ne zazzaɓine ke damuki ko"""

    "Au baki yrda ba kenan Jummai?"
  "A'a ba haka bane Harira"""
  "To menene?"
"Kawai dai"

      "Kawai dai me? Nace dake zazzaɓine ke damuna""

   "Duk harira na mgnr ne Amma jikinta babu kuzari,kallo ɗaya zakai mata ka gano akwai alamar tmby a tattare da ita"

     "Ƙarewa harira kallo tai haɗi da gyara zama snn tace"Harira!!!"

    "Kai Harira ta ɗaga"
"Kin San dai babu ɓoye-ɓoye a tsakanimu ko?"

    "Kwarai kuwa"
"Faɗimi gskyn abinda ke damuki"
"Shiruuuuu Harira tai haɗi da sauke nannayar ajiyar zuciya snn ta kuma cewa babu komai"

     "To shi kenan naji babu komai,Amma ki sani daga yau sai yau,babuni babu keee"""

    "Da sauri Harira tasa hannu ta rufewa Jummai baki snn tace dan Allah kada muyi haka dake"

    "Ɗauke kanta tai gefe snn ta miƙe""
     "Da sauri itama Harira ta miƙe haɗi da kamowa Jummai hannu tana faɗi dawo ki zauna Dan Allah,kada muyi haka dake Jummai"""

    "Duk da Jummai taji daɗin nuna muhimmacin da harira tai a gareta Amma besa ta zauna ba tace"bazan zauna ba in har bazaki faɗimin ba"

    "A marerece Harira tace"wlh Allah zan faɗi maki Amma ki zauna dan Allah,snn Jummai ta koma ta zauna,bayan ta zauna ne itama Jummai ta zauna"

   "Nan harira ta fara kwalla haɗi da wasa da yatsukan hannunta tanayi tana bawa Jummai labarin dukkanin irin abinda ke tafiya tsakaninta da Sabeer"""

    "Da yake Jummai macece me zafi,what???!!! Tace haɗi da miƙewa snn taci gaba da cewa kin San da haka shine tutuni baki faɗi ba kikabar abu a zciyrki? Haka ko ban ceba biri yai kama da mutum,kullum mutum na aiki Amma kullum cikin rashin kudi kike, wato kenan hatta abincin da kike amsa a office a cikin albashinki ake cirewa?"

      "Shiruu Harira tai""
     Jummai tace"to wlh bazai saɓu ba,duk ma Wanda za'ayi sai dai ayi""
   Da sairi harira ta miƙe haɗi da kamowa Jummai hannu tana faɗi me zakiyi?"..

Jikin na mutuwa daku jama'ar Wattpad, kwata-kwata bani gani comment ɗinku,idan baku buƙatar buk ɗine gwamma tun wuri na sani kada nayi kitse da kwarkwata😇.
FATAN alkhairi gareku masoya a duk inda kuke.

   

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 04, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƁACIN TAH...!BABI NA HUDUWhere stories live. Discover now