EPISODE 3

105 11 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

loadιng...........✍🏻

🌐 *RASHIN SIRRU*
(Sharrin Abokai)

Alk'alamin
JANNAH JAY
Wattpad @ jannahjay8

A dalilin su
Faccala tace
Kuduri ko Manufa
Namijin kishi

Shafi na uku

Ango sunan ya bar amarya ta huta ne amma shikam zumud'i hanashi bacci yayi, ganin ya kasa bacci yasa ya d'auko wayarsa ya shiga whatsapp, ya shiga karance-karancen postings nasu na likitoci, can Hamza ya hango shi online, ya turo masa sak'o " Ango ya haka naganka online, me kake shirin yi kana son asarar falalar wannan daren kenan? " tura masa gwalo yayi tare da cewa " Kajimin gwauro ne zai min wani tsari, kaga ni fa yanzu bana sahun tuzurai don haka ka bar wata nasiha da zakamin" daga can shima Idris sai ya turo masa sak'o "Haba Sule ya zaka hau chat a cikin irin wannan lokacin, gaskiya ka bada maza" kaman had'in baki sai ga sak'on Ja'afar, suka taso shi a gaba da mita, dake ganin duka suna online sai suka shiga hirar cikin group d'insu na Abokai, suna ta zugoshi akan meyasa ya kyaleta Isma'il baya online Mukhtar ma bai ce komi ba illa dai yace bai kamata a ganshi online ba yaje yayi bacci, su kuwa su Idris da Salman da Hamza sai iya shege suke masa, shi Hamza dake yafi su duniyanci sai cewa yake " Wallahi da nine nake da amarya kamar kai da tuni na shiga duniyar manya, amma ba komai Allah ya kaimu lokaci " haka ya bi shawarar Mukhtar ya kwanta a hakan har bacci yayi nasarar kwasheshi.

A kwana na biyu komi ya wakana a dare na biyu tsakanin Sulaiman da Zainab, kuma Alhamdulillah ya sameta yanda ya dace koma ace fiye, hakan ya k'ara jefashi cikin sabuwar k'aunarta tare da sabuwar k'imarta da ta k'aru a idanun sa, soyayya yake nuna nata mai tsayawa a rai, inda ya nuna mata baya son nuk'u-nuk'u ta ajiye kunya su more rayuwarsu, to ba laifi tana d'an k'ok'artawa, jefi-jefi wasu a 'yan uwa kanzo wad'anda ke rayuwa anan katsina, yan gidansu sai dai tayi waya dasu, gaba d'aya sai ta k'ara zama mai sanyi sabo da rashin sabo da kad'aici.

Bayan kwana Biyar da tarewarta suna zaune a falo tare da Sulaiman ya nemi ta kawo musu drinks, ta tashi ta nufi kitchen ta had'o komi kan tray tare da ajiye wa kan centre table dake kusa dashi ta zuba masa tare da mik'a masa, nok'e kafad'a yayi alamun A'a, waro idonta tayi kad'an tace "Saboda me?" yace ajiye tukun ki matso kiji wani abu" tana matsawa inda yake ya fusgota ta fad'a jikinsa takama mutsu-mutsu zata mik'e don har yanzu kunyarsa take ji sosai, bata iya sakewa sai kace ba ita ke masa wasu zantukan a waya ba, ya gyara zamanta kan jikinsa yace " Kinga yanda ake zaman kallo da miji, bawai kina wancan kujerar ba ni ina wannan " kunyace ta kamata ganin yanda yasa ta bararraje akan jikinsa take ta sunne kanta wanda hakan yasa fuskarta ta kasance a k'irjinsa, shafa kanta ya shiga yi bayan ya ture d'ankwalin kanta ya shiga cusa hannunsa cikin gashinta da ya sha gyara, tuni ta rufe idonta jikinta yayi sanyi, shima ogan lumshe idonsa yayi ya k'ara rungumeta dakyau, tuni yanayin su ya shiga sauyawa zuwa na tsantsan shauk'in juna

"Assalamu alaikum" kawai sukaji muryar Idris da Hamza tuni sun bud'e falon sun fad'o, basu jira an musu iso ba, duk da kuwa sun san da da yanzu ba d'aya bane, turus sukayi inda tuni Zainab taji kunya ta kamata tayi saurin fusgar dankwalinta tana d'aurawa, shi kansa Sulaiman da suke abokansa sai da yad'anji nauyinsu, bako kunya suka shiga zolayarta "Amarsu ta ango kin yini lafiya?" cewar Idris yana fad'a bai d'auke idonsa a kanta ba, gara Hamza samun waje yayi ya zauna yana wa Sulaiman kallon dubiyanci yana dage masa gira irin abokina kana jin dad'i fa, had'e rai Sulaiman yayi yace " Look malamai kunzo kun sa matata ta gudu ko? " don tuni Zainab tayi hanzarin shigewa bedroom ko iya amsa gaisuwar Idris batayiba, tana shiga d'aki ta fad'a kan gado tana sauke numfashi, gaskiya Idris ya bata kunya don kuwa shi har Aure gareshi yakamata yasan yanayin rayuwar ma'aurata, kuma ma ko ba haka ba ai su ba yara bane sun san yakamata, wallahi shiyasa wani lokacin maza masu abokai basu fiya burgeta, dama bata gama warewa da kunyar Sulaiman ba sunzo sun sa zata k'ara shiga wata sabuwar kunyar.

RASHIN SIRRU (sharrin abokai) Where stories live. Discover now