DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
*A HauwaAbdulkadir ina taya ki murna da kuma jajen sake zagayowar ranar haihuwar ki as u r closer to ur grave Allah ya baki ikon qarasa sauran shekarun ki cikin imani da farinciki,Allah ya albarkaci rayuwar ki ya raya zuria yayi musu albarka,Hbd Allah's khair always.*
2️⃣2️⃣
A lokacin Mummy ta kalle ta itama tana cin abincin tace "Kinaji Immileey."Ta d'ago daga kallon Baby Eve da take tace "Eh Mummy."
Ta cigaba "Inda zaki shiga yanzu waje ne na yara en uwan ki masu shekaru irin naki,saidai ina son ki sani karatu kikaje ba wasa ko qawaye ba,kina da kyau irin wanda kowacce yarinya zata so ace ke qawarta ce don haka ki kula ba kowa ce qawa ba ki sani yaran yanzu ba abinda suka iya sai rawar kai da shirme ki kula ke ba yarinya bace kinada d'iyar ki kisan girma ya kama ki ko bakya so,nasan baki da hali na rawar kai da kunji kunji na yaran yanzu amma ki sake kulawa kinji?"
Ta d'aga kai sannan tace "In sha Allahu Mummy nagode."
Daga haka ta zare Baby Eve daga nono ta miqe don shigowar Mooha don har bakwai da rabi ta gota,Mummy ta miqawa ita sannan ta miqe takai kwanukan kitchen ta fito suka tafi.
A mota dake ita Mooha yace ta zauna a gaba,nan ma ya sake mata fad'a sosai tare da nusar da ita abubuwa da yawa har suka qarasa makarantar.
Babbar makaranta ce mai gine gine da yawa,haka shuke shuken ta abun sha'awa kana kallon harabar ta da yanda aka qawata ta kasan lallai wannan ta yaran masu hannu da shuni ne,su Jannah suka wuce ajujuwan su kafin a fara assembly ita kuma suka wuce office din principal.
Acan aka yi mata interview dake ta dage da koyon turanci a zamanta a gidan kafin ta haihu sai gashi duk wani abu na turanci ta cinye math ne dai ta d'an samu matsala shima principal din yace idan ana yi mata extra lesson zata ware don yaga alamun tana da qwaqwalwa take kuma aka bata takardun interview din taci don haka SS1A aka kai ta ajinsu Jannah.
Taji dadi sosai don ko ba komai tana kusa da er uwar ta zata fi jin dad'in karatun gabad'aya.
Jannah ma taji dad'in don dama tunda ake zancen makarantar addu'ar ta Allah yasa a kawo mata ita ajin su,aiko sai gashi an kawo tan.
***
Basu tashi ba sai 5:00pm driver dinsu ne yazo ya dauke su,Immileey ta gaji sosai don kusan bata taba zama a makaranta irin haka ba sai yau a gajiye tiqis ta shiga gidan.Kai tsaye toilet ta nufa tayi wanka ta canza kayan jikinta zuwa wata doguwar rigar mara nauyi ta sa hijab ta fita ta nemi abinci taci a sannan Sabuwa ta kawo mata Baby Eve tana ta wasan ta.
Ta kalli Sabuwa tace "Hala tasha madara ne?"
Sabuwa tace "Eh gaskiya dazun yayan ku ya kawo mata katon guda to Mummy ta bata don bata ma dade da shanye ragowar ba."
Tayi murmushi tana sa mata nono a baki tace "Nagode."
Sabuwan ma murmushi tayi tace "To bari na koma bangaren mu idan kin gama bata kya kawo min ita."