🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *RASHIN SIRRU*
(Sharrin Abokai)Alk'alamin
JANNAH JAY
Wattpad @ jannahjay8Marubuciyar:
A dalilin su
Faccala tace
Kuduri ko Manufa
Namijin KishiShafi na Hud'u
Tunda ya tashi da safe bashi da burin da ya wuce yaga fuskar matar abokin nasa, ga tulin miss calls daga masoyiyarsa amma ina baida sha'awar jin muryarta, haka nan yana cike da tsananin jin sha'awarta shiyasa ma yake abu a sanyaye, k'arshe dai a makare ya je office.
Tayashi saka kaya take suna hira cike da farin ciki, bayan ta gama shiryashi ta kalleshi tayi murmushi tace " Gaskiya kayi kyau sosai Baby" yaji dad'in yabon da ta masa yace " Kece silar yin kyau na domin kasancewa ta dake shine yak'e k'ara kyau a rayuwata" fitowa sukayi a tare hannunsu rik'e da na juna, shi ya janye mata kujera bayan ta gama zuba masu abinciol, ta hau sannan shima ya hau don yin breakfast, wayarsa ce ta shiga k'ara inda Zee ta d'aga masa wayar tasa mishi a handsfree kamar yanda ya umarceta Ja'afar ne " Ango Ango, yau makarar ce ko? Don Allah ka k'ok'arta ka shigo don akwai ayyukan da zakai ana nemanka" Akwai abinci a bakinsa sai da ya had'iye sannan yace " Ok ba damuwa insha Allah zanzo nan da awa d'aya" jan tsaki yayi yace " Har awa d'aya? Amma shikenan sai kazo" dariya Sulaiman yayi yace " Awa d'ayan ma ai don ba yanda zanyi ne , banda dole ai da zama zanyi kasan banson yin nesa da Halaly, kodan bari nayi shiru bazaka tab'a ganewa ba"
" Wallahi Sulaiman ka takuramin fa, karkasa nayi zuciya na auro uku a lokaci d'aya" murmushi Zee tayi saboda ta saba jin irin wannan wasan a tsakaninsu, Sulaiman da yake dariya k'asa k'asa yace " Koma hud'u zaka aura nadai riga ka shiga daga ciki, don haka dole kazo karban orientation" kashe wayar Ja'afar yayi yace " Sulaiman da Zee hmnn"
Koda Sulaiman yazo sallama sai da yasha salo iri iri daga Zee, har ji yake kaman bazai tafi ba, yana cikin mota har zai tafi yace "Halaly yau ma kiyi abincin da yawa don kaman su Uzee ma zasu shigo, kawai dai yafi na jiya yawa, ina fatan bana takura maki ko?" murmushi tayi tace " Ba matsala kasan girki hobbie na ne" shafa kumatunta yayi yana mata kallo mai cike da shauk'i, har ta juya zata tafi yace " Halaly minti biyu" dawowa tayi jikin motar ya manna mata peck a kumatu da tsinin hancin har zuwa goshi, sai suka kyalkyale da wata dariya mai salo ya d'aga mata hannu ya tafi.
Isma'il dake orthopedic shida Salman, tafiya ta kamasu zuwa Kano kan wani uzuri nasu, don haka bayan Sulaiman y shiga Office da awa biyu , har ya fara aiki sai gasu sunzo yi musu sallama, a lokacin Idris yana nan wajan aikin yazo wajan Sulaiman kan wani abu sai yake tayashi, kasancewarsa Radiologist amma shi a Generel hospital yake na katsina, ana hakane su Isma'il suka shigo, bayan sun gaisa suka shiga yan wasanninsu na abokai, sannan sukai masu maganar tafiya, cike da shak'iyanci idris yace " Kodai Madam ce tayi k'ira?" dariya Isma'il yayi yace " Kaji dashi, kasan in da itace tayi k'iran ba wata kwana-kwana zan fad'a, ba kaman kai bane da lokaci d'aya za'aji ka tafi ganin gida kaman walk'iya" gaba d'aya suka dara, don sun tuna farkon auren Idris da yamma zakaga bai yini da shirin tafiya funtuwa ba sai kaji yace zai tafi, don akwai sanda ya d'orawa kansa zai tafi gashi baida mota a lokacin, kaf cikinsu mutum biyu keda ita su din kuma basu nan, haka ya hau motar haya ta lalace musu a hanya, ruwan sama ya masa mugun duka, sai d'ayan dare ya jewa amarya, koda yaje yayi ta bugu tak'i bud'ewa, don batasan zai zoba, gashi wayarsa ya d'auke haka ya kwana a k'ofar gida, kafin yaji tsoron zuwa gidan yan uwa a zaci ko sab'ani suke da matarsa gari ya waye mura ta zabgeshi yayi tsamo-tsamo kaman jikak'k'en tsunma.
YOU ARE READING
RASHIN SIRRU (sharrin abokai)
General FictionYana shigowa yaji wayar matar tasa tana ringing sai dai kafin ya iso kan gado inda take tuni wayar ta tsinke, basarwa yayi ya isa kan gadon yazauna tare da furta "wash" ya zare hular dake kansa, karar shigowar message wayar tayi da same number da ta...