👑👑👑 *WATA SHARI'AR* 👑👑👑 (sai a lahira) Alhamdulillah rabbil alamin, ina mutukar godiya ga *ALLAH (SWT) mai kowa, mai komi, mai yadda yaso a lokacin da yaso. Ya bani ikon fara Wannan littafi tare da kammala shi lafiaya, Wannan Wannan littafi ya banbanta da sauran litatta fai kuma 80% na Wannan littafi true life story ne, kuma da yarda da amincewar wanda abin yafaru a kansu zanyi Wannan rubutu, ina fatan zaku bani hadin kai Wannan littafi na WATA Sharia cikin wata unguwa da a ke kira *kusufa* unguwar kusufa unguwa ce da tai kaurin suna wajen ilimin islama, cikin Wannan unguwa Malam usmanu mai amajirai yake, datijjo ne da ya amsa sunansa, ma'ana mutum mai tsakanin hakuri da riko da addini, yanada almajirai masu dumbin yawa, yanada matar aure guda daya naja'atu wacce yaran unguwa suke kira da innatuwa,naja'atu matar Malam usmanu bata taba haihuwa ba Kusan shekara 20,har an fitar da rai, ubangiji mabuwayi maji rokon bayinsa ya amshi adduar Wannan bayinsa, ya azurta su da siya mace wacce taji suna ummu-rumana, kyakykyawar diya mai tsananin kama da mahaifinta, a yadda labari yazo Malam usmanu ba dan Asalin garin zazzau bane sae dae tun kuruciya yazo garin. Don haka yara samari masu tasowa basu san ba dan gari bane, kuma kaf cikin garin Babu wanda yasan daga ina Malam usmanu yaxo, duk da kasancewar Malam usmanu yana koyar da almajirai harma da yaran cikin unguwa. Haka baisa zuciyar sa mutuwa ba, mutum ne dan kasuwa mai dogaro da kansa. Maifiyar ummu -rumana wato matar malam usmanu naja'tu haifaffiyar garin zaria ce wata unguwa da ake kira ban-zazzau.tun shigowar Malam usmanu garin zaria mahaifin naja'atu ne ya sauke shi, lokacin yana tsakanin bukatar taimako, Malam Musa shine cikakken sunan mahaifin naja'atu wato matar Malam usmanu kuma mahaifiya ga ummu-rumana, Malam Musa cikakken manomi ni inda yake noman doya dankali, sannan lokaci zuwa lokaci yakan shiga kano domin kai doya da sauran kayan masarufi. Don haka Malam Musa shi ya fara koyawa mlm usmanu kasuwanci. Haka rayuwa ta kasance har usmanu ya fara dogaro da kansa baya bukatar komai, harma yakan iyayiwa wasu, ranar asabar da lahadi yakan hakura da kasuwa domin koyawa yaran unguwa karatu, sannu sannu har Allah ya daukaka abin a kan kawo yara daga unguwa unguwa karatu gurin mlm usmanu, makaranta ta bunkasa har daga garuruwa, ganin da Malam Musa yayi usmanu ya kafu yayi mishi kyautar 'yarsa naja'atu, dukkan su baisha wahala dasu ba, domin naja'atu dama da son usmanu a ranta, sai dai irin kunyar mu ta mata yasa ta kasa furtawa. 👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑. Zaman lafiya suke tsakanin mlm usmanu da naja'atu,...... Magrib ne garin shiru kasancewar ana sanyi a garin na zazzau shigowar mlm usmanu kenan bayan sun qidar da sallahr isha, da sallama ya ya shiga dakin tana zaune a Saman kujera mai cin mutum daya, da alama kaya take ninkewa domin gasunan zube a kasa. 'Salamu alaikum. 'Waalaikumussalam, ta karba masa sallamar tare da cewa yau sanyi ya koro wasu ta fada da murmushi a kan fuskar ta da alamun tsokana, ya karaso dakin tare da samun daya daga cikin kujerun ya zauna fuskarsa shima cike da murmushi, wato yau tsokana kikeji koh? Sha Mutuminki sanyi baya hanamu karatu, shima ya mayar mata da martani. Sai yanzu ne na sake kallon malam usmanu kyakyawane ajin farko sannan kallon girman da nake masa a riga ne bazai wuce 35 ba, fari ne tass yana gashi mai kyau irin na fulani wanda zakai zaton shampoo yake masa, 'ta ajiye ninkin kayan tare da debe wanda ta ninke ta Mayar cikin dirowar dake garke a dakin. Madaidai cin daki ne da ya cinye gadon ta sai mudubi daga gefe sannnan dirowar da suke amfani da ita wajen zuba kaya. Kasancewar ta gama aikinta tsaf ga samira saiti biyu data zuba abincin bayan ta kwashe, ta matso dasu yafara zuzzuba masa abincin. Sakwara ce a daya samiran kuma miyace dage dage da da taji busashen kifi, ta Mina masa er robar da zai dauraye hannun sa, ya sakko kasa domin cin abincin. Cikin nutsuwa yake cin abincin hankali kwance. Naja'atu na kallon sa. Ita dai a duniya mijinta yana burgeta komai nasa cikin nutsuwa yake. Ta numfasa wanda yasa mlm usmanu dagowa don yasan kwarai wata maganar ke cin ranta. Baice komai ba itama haka yasan dabi'arsa indai yana cin abinci baya magana har sae ya kammala. . 'Alhmdulh. Shine abinda taji Yace, kuma hakan ya tabbatar mata da ya koshi, ya dauki ruwa ya sha, tare da goge bakinsa, 'a hankali ta matso ta kwashe kayan da yaci abinci dasu ta Mayar gefe. Da murmushi ya kalleta 'yar kyakyawar matata ya a kayi ne? Da alama Wannan bakin cike yake da tambayoyi. Tayi murmushi ta sake matsowa ta dauki kafarshi daya ta dora bias cinyar ta, tana matsawa a hankali, sosai yake jin tausar saboda kwarai ya gaji, yana daga abinda yake sawa yake kara son naja'atu. Kamar bazatayi magana ba ta dago, 'nikam mijina inason tambayarka abubuwa, sai dai ban san ya zaka dau tambayar ba, ina fata kayiwa tambayata kyakyawar fahimta. Sosae yake kallonta don baisan tambayar da zatai masa ba, ya nisa yana kara gyara zamansa, inajinki matata me yafaru? Ni kam don Allah mijina ko zaka iya bani labarin waye kai? Ina nufin inane garinku, ina danginka suke? Kasan rayuwa, Allah ne kadai yasan gawar fari amma yakamata ko kowa baisan kasarka ba ni nasani kodon 'ya'yanmu. Sosai yake kallonta har ta kai aya, da alama bawai Itan yake kallo ba, da alamun ya tsunduma wani tunani na daban. Ta danja kafarsa kadan hakan ya taimaka wajen dawo da nutsuwarsa, yadanyi murmushi mai nuna takaici yaja numfashi kana Yace, karki damu matata insha Allah wataran zaki san wanene usmaan harki bawa wasu labari. Ko babu komai ta samu nutsuwa don yayi Alqawarin gaya mata watan wata rana☺☺ cin dabara irin tasa ya janye hankalinta daga Wannan maganar har ta manta suka ci gaba da hirarsu cikin nishadi da qaunar juna....... (Masu karatu inaso ku fahimci alaqar dake tsakanin mlm usmanu da mlm Musa saboda ku fahimci ainihin labarin don yanzu ko haihuwar ummu rumana bataiba sai dai shigar cikin) kwanci tashi ba wahala gurin Allah shekara 25 babu haihuwa gashi har Allah ya kawo cikin, cikin naja'atu ya girma haihuwa ko yau ko gobe, ranar laraba naja'atu ta santalo erta ummu-rumana. Sunyi farin ciki sosai sukaci gaba da rainon 'yarsu cikin mutunci da tarbiyya innata shine sunanda ummu rumana ke kiran mahaifiyarta dashi,kasan Cesar bakin bai kwari ba sai kazata innatuwa take cewa kuma sauran yaran unguwa kai harma da manya sukaci gaba da kiranta da innatuwa kafin kace me sunanta na ainihi ya bace sai innatuwa. Sunan innatuwa ya bita, sannu sannu ummu rumana take girma tasamu kulawa da tarbiyya tare da ilimin islama gurin mahaifitinta mai zurfi kaf hakurin mlm usmanu rumana ta dauke har takusan finshi. Ko magana bata dameta ba, ko da yaushe inba karatun ba to tana tare da innatuwa tana tayata aiki...... 🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔🔔. G. G. S. S DALA cikin garin KANO unguwar gwammaja (ina mutanen KANO ina miqa gaisuwa, kano ta dabo tumbin giwa koda me kazo an fika. Ina nan zuwa garin ku don cin gurasa lol😆) makaranta ce ta 'yan mata wanda suka amsa sunansu, kwarai makarantar ta tsaru kasancewar ta boarding (wato makarantar kwana) duk fatima sani indabo(kuyi hakuri idan sunan yazo daya da wata daliba hakan labarin yazo amma bama nufin da ita ake) tana daya daga cikin daliban Wannan makaranta wadda sardauna hostel shine hostel din da wannan daliba take, cincirindon en mata ne in banda hayaniya babu abinda ke tashi, nai saurin karasawa don sanin menene yakawoka wann hayaniya caraf naji wata daliba ciki tana magana'gaskia indabo abinda kike baya dacewa wato yanzu kin dena rokon kayan abinci kin koma sata? To wallahi Wannan ba halin kaiwa gidan miji bane, kuma wallah duk wacce kika karayiwa sata sai kin ci duka don bazamu kyaleki haka ba. Cen na hangota cikin dandazon daliban nan tsugene tanata gursheken kuka maitaba zuciya, wasu na dungure mata kai wasu na zaginta, kukanta ya qaru don kuwa ji take dama zata mutu ta huta da tsananin bakin ciki, lallai babu wanda ya jawo mata Wannan wulaqancin sai mahaifinta. Ya Allah kana ganin halin da nake ciki, ya Allah kaimana hisabi da mahaifina ka karbe duk dukiyar da yake taqama da ita ka nuna masa isarka, cikin kuka take wann adduar(nidai jikina yayi sanyi irin wnn adduar Anya kuwa mahaifinta ne? To ni me ruwana bari dai naci gaba da binta ko zan samu amsar tambayata.
YOU ARE READING
WATA SHARI'AR
Short StoryWanna littafi na wata SHARI'AR littafine da ya banbanta da sauran littafi kuma littafi ne wanda Kusan 80%true life story ne