DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:_mhiz_zahra_arkel.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
2️⃣5️⃣
Tana idarwa Mummy na shigowa d'akin ta kwance mata Baby Eve tana cewa "Sai a lallaba in sha Allahu zuwa gobe ma qafafun zasu ware,zazzabin ma zai sauka."Ta yi yaqe kawai bata amsa ba,Mummyn ta juya tana cewa "Saida safe,idan ta dame ki ta hanaki bacci ki kawo min ita dakina na dai bata magani dazun."
Ta amsa da to tana shirin miqewa,harta fita ta sake dawowa tace "Na manta dazu munyi waya da Innar ki kuna makaranta lokacin tace a gaishe ki ma."
Da murna tace "Ina amsawa,don Allah Mummy gobe ki kira min ita mu gaisa."
Tayi murmushi tace "Koda baki roqa ba,ai daman rashin samun lambar su ce ma yasaka bakwa waya akai akai amma yanzu nasa an kai mata qaramar waya saboda ke kuma an hada ta shine ma mukayi wayar ai,kema kuma akwai waya a dakina duk sanda kike son waya dasu kizo ki dauka kiyi kinji."
Ta jinjina kai tace "Nagode."
Ta amsa da "Babu komai Khadijatu,saida safe."
"Allah ya kaimu." Ta amsa tana qoqarin ajiye dardumar hannun ta a ma'ajiyar ta,tana kuma mamakin rashin hawowar su Jannah har wannan lokacin.
Agogo ta kalla,tara ta gota tana son shan ruwa bata son kuma barin Baby Eve ita kad'ai don Innar ta tasha gaya mata ba a barin yara qananu su kadai ko don saboda mutanen boye (aljanu) don haka ta zauna tana tunanin abinda ya kamarta tayi.
Cikin sa'a saiga Amnah ta hauro zata dauki abu,da sauri tace "Don Allah Amnah zauna min da ita zanje na dauko ruwa a qasa in dawo."
Amnah ta ce "To."
Ta fice da sauri,ta sauka zuwa kitchen d'in,a babban falo taga Jannah tana kallon wani american film na Tom cruise tayi dariya cikin tsokana tace "Ashe mutumin ake kallo shiyasa ba a ji ba a gani."
Tayi dariya tace "Kedai bari ai in ina kallon su shida brad pitt da angelina jolie ji nake na gama kallo kawai."
Cikin tsokana tace "Banda su Ali Nuhu."
Tsaki taja tace "Kece kika sanshi ma."
Dariya tayi ta juya,gwarab taji tayi karo da abu da sauri ta juya tana fad'in "Subhanallahi waya ajiye.."
"Uban kine." Ya fad'a a fusace tun kafin ta qarasa magana tare da tankada ta bayan ta ya bugu da drawer ta yi er qara saboda zafin da taji a mugun fusace yace "Ke wai wacce irin dabba ce?koda yake baqauye meya sani banda wawanci da hauka,kin taho baki kallon gaban ki kina hauka banza kawai."
A hankali tace "Amma bani na na buge.."
Kwaf taji an make bakin kafin ta gama magana,yace "Nina bige ki kenan ko?nine bana kallon gaban nawa nufin ki ko?wallahi jikin ki zai fara gaya miki banza kawai."
Ya wuce fuuuu kamar kububuwa ya wuce ta ta bishi da kallo tana matsar kwalla don ta bugu a bayan ta har lokacin zafi yake mata haka bakin daya buge mata hannun sa kamar katako saboda zafin da taji,ta shafa taji har dan tashi yayi ba iya zafin yake mata ba,haka ta d'auki ruwan ta koma jiki duk a sanyaye ko magana bata sake yiwa Jannah ba ta wuce itama kuma dake hankalin ta na kan kallon da take yi bata ganta ba.
Amnah ma data koma sauri take ta sauko ta qarasa kallon bata kula da yanayin ta ba ta fice.
Ta sha ruwan ta ajiye ta haye gadon tana share kwallar da take ziraro mata,a hankali take tuna ko ta taba yiwa Lameen wani laifi ne da yake mata abinda yake mata tayi tunanin duniya amma ta kasa tuna me ta tab'a yi masa na laifi ita dai ko sanin sa bata tab'a yi ba kafin zuwan ta kano banda sau daya data ganshi da Mooha kuma a wannan ganin bata yi masa komai ba,to meyasa ya tsane ta? "Saboda kina er qauye shi kuma baya son en qauye." Waya zuciyar ta bata amsa,ta juya tana cewa a fili "To ai idan qauyanci na ne yasa ya tsane ni mahaifan sa ya fara dacewa ya tsana tunda suma daga qauyen su kuma su ya fara ya sani a en qauye."
Abun ya soma damun ta don ya soma yawa,kuma idan aka cigaba a haka lallai zata cutu da yawa dole ta dauki mataki to amma wanne iri?bata son hada shi da iyayen sa don tasan dole zasu saba masa to me zatayi itama ta qular da shi?mataki dai dole ta dauka don kada watarana ya karya ta.
Duk iya tunanin da tayi ta kasa tuna meya kamata tayi kasa don ita ba fitinanniya bace sam,kuma Innar ta tasha gargadin ta akan girmama wanda ya girme ta ko yaya ne shiyasa bata iya yiwa mutum rashin kunya indai tasan ya girme ta ko girman da ya mata ba mai yawa bane balle Lameen data san ya kusan ninka shekarun ta.
Tana kwance sai juyi take Baby Eve ta motsa,haka ta lallaba ta ta bata abincin ta ta koma ta kwanta tana kallon yarinyar bata sani ba har bacci ya dauke ta.
***
Ruwa ya dauka da madara da cup sanda ya bige Immileey,ya koma d'akin sa ya ajiye kayan hannun sa kan d'an qaramin table da yake amfani dashi wajen karatu da en zane zanen sa.Tsiyayar madarar yayi a cup ya kurba sau daya,abun mamaki sai ya tsinci kansa da tuna abinda yayi wa Immileey da yanda ta buga bayan ta don ya lura da yanda ta yatsine fuska ya kuma san ta bugu sai kawai yaji ta bashi tausayi kuma shi kansa ya soma laluben me yarinyar tayi masa ne haka shi da babu ruwan sa da sabgar yara ma duka in sun tasa?.
"Saboda qauyencin ta,kuma kai me yasa zaka kula baqauyiya irin ta,bayan haka tazo muku gida ta kankane kamar na baban ta sai wari suke fama dashi." Zuciyar sa ta bashi amsa amma a fili si yace "Ita daman can bata wari,da alama tana da banbanci da sauran dana sani."
Sai kuma yayi tsaki yana jin haushin kansa don meyasa zai tsaya yana tunanin wannan baqauyiyar ai koma me ya mata she deserves it,yayi ta shan madarar ba don yana jin dad'in ta ba sai don wai a dole ya goge tunanin Immileey da abinda yake mata yasan baya kyautawa.
Daga qarshe dai dolen sa ya sakarwa zuciyar sa musun suka cigaba da tattaunawa akan Immileey shi da ita wani abun yaji haushi yayi tsaki wani abun yayi dariya don da yawa shirmen da suke da su Jannah Amnah na bashi labari sosai he just pretend kamar baya so kuma baya ji amma yana jin dad'in labaran wataran da kansa yake tsokano ta don ta bashi amma sai yayi ta inda baza ta taba gane labarin yake son ji ba.
ZahraArkel ce!