Page 24

541 34 8
                                    

*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟

2⃣4⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

Bayan su dawo daga kauye suka tsaida maganar aure nan da wata uku masu zuwa(akwai shoki ashe💃🏻💃🏻💃🏻) ,
kuma sukayi rabon goro inda aka fidda ma kowa na shi , inna ta aika ma mutanen kauye nasu sannan ta ba yan uwan ta da abokan arizikin ta , sannan aka kai islamiyar su Samira , kuma aka bawa zainab kawarta da maman zainab in, da sauran wasu yan mata na maqwaftan su, wannan kenan

Bayan kwana  biyu da dawowar su inna daga kauye , suka tafi wajen mai yin gado suka kai kudi , irin nasu na talakawa sannan inna ta saye katifa da sauran kudi, ba laifi kayan da ta zaba masu kyaw ne.

Sannu sannu lokaci na tafya , al'amura sun cigaba da tafya dai dai wajen Habib da Samira inda yanzu ta fara sabawa da shi tinda suna hira da shi sosai in yazo wajen hira duk da so biyu ne yake zuwa a sati ba kullum yake zuwa ba,  saidai tafi magana in ya kira a waya , 
Ita ma Hafsat tuni ta jima da yin arba'in sai dai kuma a lokacin ne za'a tafi hutun karshen shekara shiyasa bata koma school ba hutun ta ya karu, tana gida abunta yanzu ita ke yin girki saboda lokacin da ta fada ma wata kawarta kishiya za'a mata ita ta bata shawarar har girki ta rika yi da kanta , ta kuma cemata dole sai ta fidda son jiki da ragganci in ba haka ba amaria in ta shigo in dai ta fara yiwa mijin ki abinda baki mashi to sai ya linka son da yake mata fiye da naki , aiko tin daga rannan ita ke yin girki , kuma dama Nafisa ta koma school an janye strike tin tuni.
kasancewar aiki yayi mata yawa (inji Hafsat fah😆😆) mai raino yar yarinya ta samo cikin dangin su kafin a koma school ta sallemata tinda in an koma gidan su Habib zata rika kai yaran ta kafin ta tafi school kasancewar Hajiyar su bata aiki ita kuma maman ta aiki takeyi. Wannan kenan

Su ma su Iman sunyi exam har an bada sakamako tayi aiki mashah Allah .
A bangaren auren da Habib zai kara kuma Hafsat tayi shiru ta nuna mashi tayi hakuri kamar yadda tace amma a ran ta ba haka abun yake ba saboda ta kuddira anniyar indai amaria tazo da rashin mutumci sai ta nuna mata tafi ta iya shi, kuma har yanzu bata san wacece Habib zai aura ba.

Lokaci yana yita tafya Shirye shiryen azumi ya kankama inda ko ina ana ta shirin tarban watan azumi , saboda watan azumi ya kusa inda bai wuce kwana uku ba , kenan auran Samira saura wata 1 da rabi tinda bayan sati ga sallah biyu ne auran , a lokacin kuma sun fiddo ankon su itada zainab kawarta da wasu maqwaftan su , atanfa da matarial ne suka fiddo itada kawayen ta 4 saboda batada kawaye sosai saidai zainab zata mata gayyatar yan school in su saboda habib yace hada Cocktail ( diner party) za'ayi ( aiko munada diner , ashe akwai sanya kayan sallah🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀💃🏻💃🏻💃🏻) 
ya

Alhamdilillah yaw litinin anga wata inda an gayi a TV ance za'a fara azumi gobe , kowane gida ka shiga sunyi abincin su na sahur , ba laifi su ma inna sunyi shinkafar su da miyar taushe
A bangaren Hajiya Hafsat kuwa yaw fah ta jigata saboda an fara abinda ba'a saba ba , tayi aiki sosai saboda abinci kala biyu ta girka , kala guda suci da dare guda kuma suyi sahur da shi , Bayan ta gama girki taje ta tsala wanka tayi kwaliya tana shirya kanta cikin wasu riga da skirt na atanfa tayi kyaw , bata wani yi kwaliya fah illa poda da man lefo da ta shafa,  bata wani jima da ta gama shiri ba mai gidan yazo , ta tarbe shi yayi wanka sannan sukazo sukaci abinci , daga nan suka dawo palour suna zaune tareda iyalin shi har lokacin bacci yayi sukaje suka kwanta.

Washegari da safe an tashi azumi dan haka Samira tinda suka tafi islamiya karfe 8 sai kuma karfe 1 na rana za'a tashi kasanv'cewar in azumi ya kama tashi daya sukeyi a islamiya , itama yaw fah azumin yana kai mata saboda ana kwala rana sosai , bayan an sauko daga islamiya tana zuwa gida tayi wanka da sallah sai bacci ba ita tashi ba sai da la'sar . Daga nan sukayi shirin buda baki , zogalen su suka saye suka gyara ta sannan suka dafa zobo , sabida jikon zobo zasuyi ,

Acan kuwa gidan Alhaji Habib  tare na tarda su shida ita suna gyaran kayan buda baki , suma zogale suka saye saboda basu son sayen takarcan nan ci wannan ci wancan yana bata ciki balle yanzu ga azumi , dama daffafa ce Habib ya soya a kasuwa shine da yazo ya rage mata aiki suka gyara tare sannan ya mata sallama ya koma kasuwa ita kuma ta shiga kitchen , domin girka masu abinda zasu ci .

Alhamdulillah an sha ruwa lfy inda kowa yakeda azumi daya , bayan an sha ruwa anyi sallah Habib ya kira matar shi yayi mata barka da shan ruwa kasancewar ba'a gida yake shan ruwa ba, bayan sun gama itama Samira ya kira ta ya mata barka da shan ruwa , suka taba hira sukayi sallama har yana shaida mata zaizo hira a washegari.

Sannu sannu lokaci yana tafya inda azumi har ya kai goma , iyayen Habib suka kawo kudin kayan sallah gidan su Samira  jikka 60 suka kawo tareda sugar katon babban ,
Su ko sukayi rabon sugar inda akayi kulli kulli aka kai gidan yan uwa da abokan arziki, sannan inna ta rike  jikka 60 (dubu 36 ne 😀  ) saboda su saye wani abu da su kasancewar sun kai kayan lefen ta wajen dinki itada Habib kenan cikin su tayi kayan sallah da su dan haka batada bukutar sayen wani abu

  *A gurguje*

Bayan kwana goma , yaw ne za'a fara kiyamullaili inda duk musulmi na kwarai yake tashi tsakar dare yayi ibadar shi , cikin goma karshe na wata ramadan , saboda ana so mutum ya linka ibadar shi a cikin su ,
karfe daya na dare su Samira suka fito itada inna masallancin dake unguwar su , ita dai inna tana zaune dayake batada jimirin tsayuwa

Suma A bangaren Habib dayake akwai masallacin kofar gidan su nan suke fitowa suyi sallah su , in zai fita yake tada Hafsat itama tayi alawala sannan ya tafi saboda yara dake gareta  shiyasa take zaman ta a gida.

Haka kullum suke zuwa in sun dawo suyi shurin sahur .
Tin ana saura sati sallah samira ta anso kayan ta daga wajen tela ba laifi kayan sunyi kyaw kuma yaw ne za'a basu hutun sallah a islamiya , sai zumudi akeyi an kusa sallah amma kuma in ta tuna da maganar auren ta da duka sati 3 ne yayi saura kacal sai gabanta ya fadi shikenan ta kusa rabuwa da innar ta , bayan sun taso daga islamiya an basu hutu bayan sati ga sallah za'a komawa.

Shiryen shiryen sallah ko wane gida ka leka zakaga ana ta yin shirin sallah , in ka leka gidan kitso da lalle zakaga mutane dankam , wajen masu tela ma gasu nan dai mashah Allah,

A gidan Alhaji Habib kuwa suma duka an kawo masu kayan su na sallah kala uku uku yayi masu , material , shadda & atanfa, shaddar su duka anko ce sukayi duka gidan , shima Habib da muslim kayan su iri daya ne, sai usaina da sudais sune duka yan kanti ne akayi masu ,

Yaw ne za'a yiwa Hafsat lalle da kitso tin safe masu lallen da kitso sukazo har gida domin yiwa uwar gida Hafsat lalle da kitso tareda iman dayake akwai CFA basujin wahalar zuwa har gida suyi maka, sannan Habib ya kai su Muslim akayi masu askin sallah .

Lallen da akayiwa Hafsat sai kace na amaria saboda ya hadu yayi kyaw, shima kitson ta yayi kyaw sosai.

Itama Samira yaw ne sukaje kitso itada zainab , an tsantsara masu mai kyaw sannan kuma a washegari suka tafi lalle ba'ayi mata wani  mai yawa saboda ana so ya goge kafin auren ta, kasancewar batada cin lalle amma da bama zatayi ba , ko kitso manya ne akayi mata amma fah ya tsaru , tsaf gwanin kyaw ,

Yaw ake tarban wata sallah ko ina se shiri akayi masu yanka nayi nayi sayen nama nayi ,
A gidan sarki kuwa anyi hawan kawo





_*kuyi hakuri da wannan banida charge wlh*_

_inshah Allah page in dare zai kayatarda ku_

*GOOD MORMING MY FANS*
*BONJOUR A TOUS*

Je vous aime tous
Love you all my fans❣❣❣

*💕NANA AICHA💕* ce

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Where stories live. Discover now