Part 27

330 23 4
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:_mhiz_zahra_arkel.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭


2️⃣7️⃣
A kano kam Lameen tun da aka fara bada admission yayi applying kuma cikin ikon Allah yana yi ya samu don dama result dinsa yayi kyau don haka nan da nan ya soma shirin tafiya inda zai qaro karatun wato Australia.

Sanda suka tafi bai fi sauran sati d'aya ya tafi ba don haka yayi busy sosai,sauran kwana uku ya tafi Abeey ya takura shi suka tafi Gogel don yayi sallama da su Innah Amina ai ko yana qunci suka tafi harda Mummy.

Su Amnah na zaune harda Immileey suna taya Innah Amina tsinkar zogale sukayi sallama,da gudu sukaje sukayi musu oyoyo.

Ita dai Immileey wajen Mummy tayi Jannah da Amnah ne sukayi wajen Abeey sai kuma Amnah ta sake shi ta tafi wajen Lameen tana fad'in "Oyoyo Jaan L ashe harda kai."

Yayi dariya yana shafa kanta yace "Harda ni..."

Kafin ya qarasa magana Innah Amina tace "Uban en baqin hali nasan tattago akai ba yin kanka bane kai da baka son qauye kuma kullum ina gaya maka iyayen ka uwar ka da uban ka duk anan suka rayu binnin da kake yiwa duka har yanzu basu shekara talatin da komawa ba dan nema kawai."

Kauda kai yayi tana dan guntun tsaki,tako fusata amma Abeey ya fita don shi kansa yayi da sauri tace "Barshi yayi dan banza mai baqin halin masifa bani kai wa tsaki ba uban ka Hamisu da shi kake mara kunya kawai,naga tsaka ma wajen iya tsaki."

Mummy ranta ya baci tace cikin fusata "Ana maka magana kana tsaye qiqam vaka da bakin bada haquri ko?wai meyasa duk irin fada da nasihar da za ayi maka baka jine."

Sai wani ciccijewa yake kafin yayi magana Mooha ya shigo gidan,da fara'ar sa ya qarasa amma ganin yanda kowa ransa a bace yasa yace "Meya faru?"

Innah Amina tace "Wannan maras kunyar zaka tambaya." Ta qarasa da nuna Lameen.

Mooha yayi murmushi yace "Oh ke kam masoyiya meya faru kuma ake kiran brother na da maras kunya." Ya qarasa yana zama kusa da ita tare da dafa qafar ta.

Cikin masifa tace "Yo tsaki yake min niko naga tsaka ma don uban mutum wajen tsaki."

Dariya yayi yace "Aa kinsan bazai yi miki tsaki don yayi miki rashin kunya ba,wasa yake miki fa."

Harara ta galla masa kafin tace "Ni zakayi ma wayo wa?wannan uban en nuqufurcin ne zaiyi min wasa,to idan ma shi yake yi ni bana son wasan shashancin banza kawai kuma uwar sa da ubansa gasu nan a tsaye su yayiwa tsakin bani ba."

Yana qunshe dariyar sa yayi wa Lameen alamu da ido daya bata haquri.

Yana ta ciccijewa yace "Kiyi haquri."

Mummy zata yi magana Innah Amina ta riga ta "Banza haka zaka qare a quntace fice ni ka bani waje."

Ya juya da sauri ya fice,Mooha kuma cikin wasa da tsokana ya matsa qafarta yana cewa "Ni ban taba ganin amaryar da ke fushi da angon ta ba saike,kuma gashi baffa zamu ture mu baki shi."

Tsaki tayi tace "Ni wallahi Allah ya tsare gatari da saran shuka wannan matar sa ta shigesu da shegen nufurcin sa."

Jannah itama cikin tsokana tace "To ai kece matar tasa ko Ya Mooha?"

Daquwa tayi mata tace "Ungo er nema kema ai irin halin nasa dake amma ke naga kin dan sake yanzu ko don khadija ne oho."

Dariya sukayi sosai don daman Immileey dagewa kawai tayi ta riqe tata tunda akewa Lameen fad'a murna take yau meyi ne akayi wa.

Haka su Mummy suka zauna suka sake bata haquri,suka gaishe ta sukaci abinci sannan Mummy dasu Jannah suka tafi gidan iyayen Mummyn don su gaisa.

***
A washegari kamar yanda aka tsara Innah Aziza ta tafi itada qanwar Goggo Lari,Yadikko Lami suka kai Baby Eve gidan su Turajo kamar yanda aka tsara.

Matan gidan duk suna tsakar gidan suna hira suka shiga da sallama.

Amsawa akayi sannan aka soma musu maraba,Yafendo tace su shiga daki mana,suka ko shiga aka shiga gaggaisawa sosai,sannan aka kawo musu ruwa da dan abun tab'awa.

Yadikko Lami ce ta gyara zama tana kallon Baby Eve dake hannun Yafendo tunda sukazo don ta saba da ita ana kawo ta akai akai tace "Toh yarinya dai ce ta girma shine muka kawo muku ita asa mata albarka sai zasu koma za'a dawo a dauke ta."

Yafendo tana shirin magana Ladingo dake shigowa ta buga uban guda kan tace "Kai MashaAllahu matan gidan nan ku fito Hauwa kulu ta girma."

Duk suka tattaho d'akin Yafendon suna ta shafa kanta suna mata addua kala kala,sun jima a haka kafin kowacce ta fice.

Yafendo tayi murmushi tana kallon Ladingo tace "Kin fiye karadi Ladi ai addua za'ayi Allah ya raya ta."

"Amin." Suka amsa suna miqewa,Innah Aziza tace "To sai nan da wata d'aya zasu tafi zatayi sati uku anan sannan zamu zo mu dauke ta."

Yafendo tace "Allah ya kaimu."

Suka fice sam Baby Eve bata damu ba don ta saba da Yafendo ta cigaba da wasan ta a cinyarta,Ladingo tana kallon ta tace "Nayi zaton an dawo da ita kenan Innah?"

Yafendo ta kalle ta tace "Me kike nufi da an dawo da ita?"

Ladingo tace "Aa ba an yaye ta ba?meyasa za ki basu ita su sake komawa wani birni da ita a koyo mata dabi'u marasa kyau acan ga yara su girma gandama gandama ba aure sai wani shegen boko?"

Yafendo tayi shiru bata tanka ba amma da alamu dai maganar ta fara shigar ta,ganin haka sai ta sake gyara zama tana qasa da murya tace "Yanda Allah ya dauke Turajo kuma Allah yayi akwai jinin sa a duniya ita kad'ai zaki riqa kallo tana tuna miki dashi a kodayaushe yaushe ne zaki bari tayi nisa dake?"

Yafendo ta gyad'a kai kamar zata yi magana sai ta fasa,Ladingo ta sake cewa "Kuma na kan ji manya na cewa dangin uba sune yara sune jigon riqon yara tunda dai Allah yasa ta haihu kuma harta yaye ai kuma ke sai ki karbe ta ki cigaba da rainon ta da tarbiyyar mu amma har yaushe ne yarinya ga gatan ta za a kaita wani waje da ita kanta uwar tata a kare take bata sake ba balle ita?"

Yafendo tayi ajiyar zuciya tace "Kuma da gaskiyar ki Ladingo to ko Hauwa'u tazo kenan zan fad'awa Baffa Mai shanu yaje ya sanar da iyayen ta."

Ladingo cikin son danne farincikin ta tace "Ai haka yafi yarinya ta tashi a gatan ta kawai."

Yafendo tace "Gaskiya ne."

Ganin haqar ta ta cimma ruwa sai ta miqe tana cewa "Bari naje na surfe geron can a dama mata kunu Innah."

Yafendo tace "Toh."

Ta fice ita kuma ta cigaba da lugwigwita maganganun ta a ranta,lallai da gaske ne abinda Ladingo ta fad'a a kullum idan tana kallon Baby Eve ji take yi kamar Turajo take kallo shiyasa tana masifar sonta kamar tsoka daya a miya,yanda baiyi tsahon rai ba lallai zata so jinin sa a tare da ita aiko Baffa na shigowa zata sanar masa da halin da ake ciki kuma tasan bazai hana ta ba don shima zai so hakan.



ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now