Part 30

351 21 1
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:_mhiz_zahra_arkel.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭



3️⃣0️⃣
Yana isa airport na can motar makarantar ta dauke shi zuwa en gidajen sa ake tanada domin zaman dalibai.

Gidan ne matsakaici wanda ake kira da one room apartment komai a wajen yake saidai ya tsaru iyakacin tsaruwa duk kuwa da bai cika wani girma ba.

Shi daman abinda yake so kenan ya zauna shi kad'ai shi mutum ne da bai cika son takura ba yana son zama shi kad'ai shiyasa bai ma cika abokai ba.

Cikin sati guda ya gama duk abinda ya kamata har ya fara shiga lecture ta farko ya fito suka hadu da wani matashi wanda bazai yi tsaran sa ba amma za a iya kiran sa da sakon sa,kana ganin sa kaga hutu da jin dadi a tare da shi saidai shi duk ba wannan ne yafi daukar hankalin sa gare shi ba sai ganin kamar ya sanshi daya dinga masa ya riqa tunanin ina ya sanshi yayi ta tunani ya kasa tuna inda ya sanshi har saida matashin ya gane irin kallon da yake masa ya taso ya zo inda yake zaune ya miqa masa hannu tare da fad'in "Assalamu'alaykum." Cikin wata sassanyar murya mai cike da nutsuwa.

Muryar ma tayi masa kama da wanda ya sani amma sai ya basar ya amsa sallamar tare da miqa masa hannun shima,matashin yace "Abdulraheem Al'ameen by name."

Lameen yayi murmushi yace "Lameen Khamis."

Shima murmushi yayi yace "Nice to meet u Mr.Lameen."

"Nice to meet you Mr.Abdulraheem." Duk suka yi dariya.

Ya zauna a kujerar kusa dashi sannan ya soma magana da hausa "Kayi kama da mutumin nigeria hala kai dan can ne?"

Lameen ya kalle shi da mamaki yace "Kaii ashe kana jin hausa."

Yayi dariya yace "Iyayena duka hausawa ne en nigeria ne saidai ni tunda na bude ido ban taba zuwa ba."

"Tunda ka bude ido?" Lameen ya tambaya a mamakance.

Kallon sa Abdulraheem yayi kafin ya jinjina kansa yace "Eh."

Murmushi Lameen yayi yace "Kenan anan ka girma kayi wayo kome?"

Ya jinjina kai yace "Eh mana,amma ina son watarana nima naje nigeria din."

Lameen yayi dariya yace "Nigeria tana da dadi kusan tafi kowacce qasa dadi ai."

Abdulraheem yace "Wow i can't wait naje naji yanda garin yake."

Murmushi kawai yayi kafin ya sake magana mallamar da zata yi musu darasi ta shigo don haka kai tsaye ta gabatar da kanta sannan ta soma darasi saidai ga Lameen lokaci lokaci yake kallon Abdulraheem yana tunanin tabbas ba shi ya sani ba amma akwai wanda ya sani wanda suke kama sak hatta da abubuwa da kuma maganar sa ya san sansu somewhere.

Haka suka gama lectures na ranan kowa ya fito don tafiya gida,Abdulraheem ya qaraso wajen Lameen dake jiran cab yake yazo ya ajiye shi mana ba wani musu ya bishi ya ajiye shi sukayi exchanging num yace yana masa dariya "Gidan mu na a ta baya ne babu nisa da nan."

Lameen ya jinjina kai yace "Okay ni kaga nawa apartment din." Ya qarasa da nuna masa sashen sa.

Murmushi yayi yace "Okay saida safe,idan zan wuce sai in dauke ka mu tafi ko."

Ya jinjina kai yana wucewa Apartment dinsa shi kuma ya wuce gida.

****
A ta baya wajen shan iska ya tadda maman sa ana mata gyaran farce,saida yayi kissing goshin ta kafin yace "Am back Mum."

Ta shafa tattausar sumar kan sa data kwanta sosai sai qyalli take saboda baqin ta gashi dai ya tara ta sosai don ta rufe har wuyan sa amma ba qaramin kyau tayi ba,tace "Welcome son,akwai abinci a kitchen idan zaka ci."

Ya zauna kujerar dake fuskantar ta yace "Hi Venessa(mai mata gyaran farcen.)"

Ta dago tana murmushi tace "Hi Raheem how are you."

"Am gud,U?"

"Am fine." Ta bashi amsa.

Yayi murmushi yace "Good." Sannan ya maida hankalin sakan maman tasa yace "Ma na qoshi,yau na hadu da dan nigeria."

Kallon sa tayi tana murmushi tace "Madallah,iceko kayi aboki dashi?"

Yayi dariya manyan dimples dinsa guda biyu kamar mace suka lotsa kafin yace "Sosai ma,kuma bashi da nisa da nan gidan shima masters yazo yi daga nigeria."

Ta jinjina kai tace "Idan baban ka ya dawo saika sanar masa ya dubo shi idan da dama ma sai ya dawo nan gidan."

Wani irin ihun murna yayi har Venessa da bata tsammaci ihun ba ta tsorata don ita Maman nasa tasan zaiyi don duk lokacin da yaji dadi sosai ihun yake mai hade da Alhamdulillah.

Maman nasa ta kalle ta tana dariya tace "Don't mind him he's little excited about something."

Gyad'a kai tayi tace "Oh great congrats."

Dariya yayi shima ya miqe ya rumgume maman nasa tare da kissing chick dinta yace "Thank you First love,i love u so so so very much."

Duk suka bishi da kallo suna dariya Venessa tace "Your son is handsome ma'am you know that?"

Ta gyad'a kai tana murmushi ita kuma ta cigaba "I fell for him the very first time i saw him."

Da wani kallo ta bita mai kama da mamaki mamaki can tayi murmushi tace "And he's not going to love or marry you my dear."

Ta jinjina kai tana hade kayanta tace "Okay then,maybe i can make him do all the two things."

Murmushi itama tayi tace "Do it if you can." Daga haka ta miqe ta shige cikin gida,ita kuma baturiya ta bita da kallon mamaki na tsabar yaddar da tai cewa bata isa taja hankalin yaron ta ba,ta jima tana nazari kafin tayi qwafa ta fice daga gidan ta inda ta shigo wato ta baya don bata shigar musu cikin gida,ba ita bama kowaye muddin ba musulmi bane baya shigar musu gida saidai manyan abokan aikin Mahaifin Abdulraheem da qawayen ta da babu yanda zatayi dasu amma en aiki dai basa taka musu gida saboda haka duk maids dinsu musulmai ne.



ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now