Part 32

354 23 2
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:_mhiz_zahra_arkel.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭

Kwana biyu duniya ta tsinci kanta a cikin rud'ani da tashin hankali da neman mafita ruwa a jallo,saidai mu sani ga mu musulmi wannan izina ce daga ubangiji na mu qara imani mu koma gare shi,wallahi wallahi wannan duniyar ba a bakin komai take ba idan yaga dama cikin qiftawar ido zai juyar da ita saidai Annabi (saw) ya roqa mana,jama'a muji tsoron Allah mu koma gareshi mu yawaita istigfari mu yawaita neman sauqi daga gare shi Allah ya yafe mana zunuban mu ya rufa mana asiri ya kare mu daga wannan cuta da dukkan abun qi a dage da azkar🙏

3️⃣2️⃣
Mooha ransa yayi masifar baci ya tsame hannun sa daga tuwon yana cewa "Wallahil Azeem Baffa ko ka qyale bazan qyale su ba,wallahi sai sun bamu Baby Eve, a wanne jahilcin ne akace sune suke da haqqin riqe ta yanzu?to ai ko a musulunci sai tayi wayon da zata iya zabar inda zata zauna sannan ta zaba da kanta balle kuma su wannan ma basu da imani,yanzu mijin nata ba rabuwa sukayi ba mutuwa yayi amma suyi wannan wulaqancin wallahi bazata sabu ba bari naje."

Da sauri Baffa yace "Muhammadu."

Ya juyo yana huci,Immileey ta leqo ta window tana kallon sa abin ya daure mata kai don tunda take da shi bata taba ganin ya bata rai ko yana fada ba,mutum ne mai asalin haquri da kawaici amma wannan karon kana kallon sa zaka san ba qaramin bacin rai yake a ciki ba sai huci yake kamar kumurcin maciji a hankali Baffan ya sake cewa "Zauna Muhammadu."

Ya koma ya zauna jijiyoyin kansa har sun tashi rudu rudu idon sa yayi ja,cikin lallami Baffa ya soma cewa "Muhammadu wanda baisan kara ba ba a koya masa ita sai tazo ta same shi lokacin da yake matuqar buqatar ta,basuyi mana kara ba a matsayin mu na surukan su,a matsayin yarinyar nan data zauna a cikin su na kuma tabbatar bata samu matsala da kowa ba don me mu zamuyi fad'a dasu?daman kowa Immileey yake ji,kuma tunda dai har Allah yasa ta nuna ta haqura shikenan don Allah kaima ka qyale ta abu d'aya zanta nanata muku shine duk daren dadewar da za ayi Hauwa'u saita nemi Khadijatu domin itace mahaifiyar ta ba su da kuma yanda zasuyi su canza wannan yarinya dai ayi mata addu'a Allah ya raya ta kawai mu kuma mun musu karar da su suka kasa yi mana."

Mooha ya girgiza kai yace "Baffa duk naji komai,amma ina son ka qara duba lamarin nan,kwata kwata yaushe Immileey  ta farfado ta soma sakewa daga rashin mijin ta da tayi?sannan yanzu don rashin adalci daga yaye er da inda a qa'ida ne ma bata isa yayen ba sai su karbe ta?er da ko shekara da rabi batai ba don dai anwa shan nonon nata karan tsaye ne haba ai babu imani ma a cikin wannan lamarin,don haka don Allah Baffah ka bari naje na karbo Baby Eve don Allah."

Baffah yace "Na roqe ka da Allah ka basu lokaci daga nan har zuwa ranar da zaku tafi idan har basu gane kuren su sun dawo da ita ba don Allah don annabi ka qyale musu ita don Allah."

Mooha yace "Kai Baffa." Sai kawai ya miqe ya fice kamar wanda ake ja don mugun saurin da yake yi.

Kusan tun daga ranar idan ya shigo gidan ko neman Immileey baya yi idan ba ganin ta yayi a tsakar gidan ba,saidai yaci abinci ya fice da abokan sa baya qara dawowa sai daree yayi musu sallama,yanzu ko er hirar daren ma baya zama Goggo Lari tayi tayi yaqi ya dawo ya cigaba da zaman gidan sai kace sune sukace kada a dawo da ita,haka nan Immileey takan ci kuka duk sanda ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya kalli inda take bama ita bata gane ta shaqu dashi bama sai yanzun abun ya taru yayi mata yawa.

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now