DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:_mhiz_zahra_arkel.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
*I wish u the happiest birthday dia Husnaty Abokiyar fad'a,as u get closer to ur grave,May Allah swt grant u all the wishes u've made,bless u abundantly,Fulfil all ur dreams and let u be among his best servants,i wish u all the best Hun,Allah ya azurta ki da miji nagari*
3️⃣3️⃣
Yana tafe yana shaqar sassanyar iskar daren yana furzarwa cike da nishadi har ya kai gidan,kai tsaye ya shige d'akin su yau ko sallama bai yiwa Innah Amina ba yayi kwanciyar sa.Tunda ya kwanta yake juyi,yasani shi tunda yaso Rahma yarinyar da University sukayi tare yayi mata so irin wanda shi kansa ya dinga mamakin sa daga baya tace wai iyayen ta sun zaba mata miji za ayi mata auren dole to da yake jinin sarauta ce sam bai tsammaci wani abu ba shine ma ya dinga lallashin ta tare da nuna mata muhimmancin bin iyaye har ta nuna ta haqura sai daga baya ya gane duk qarya ne daman suna tare da wanda ta aura din tun kafin ta shigo uni shi kam ta soshi ne saboda kyan sa tun daga nan ya tsani mata da sabgar su don har ya gama Uni bai qara soyayya ba sai yanzu da Immileey ta kutso rayuwar sa.
Ya lumshe ido yana tuna kukan ta da damuwar ta akan qin kulata da yayi kenan hakan na nuna itama tana sonsa ko menene?
Ya miqe zaune yana jan yatsunsa na qafa suna qas yana cigaba da harhada yanda yanayin ta ya zama lokacin da tazo da bayan lallashin da yayi mata sai ya tsinci kansa da murmushi harda dariya shi kad'ai.
Wayar sa da tayi qara ne yasa shi kallon ta Jannah ce ya dauka yana gyaran murya yace "Hello."
Daga bangaren ta tace "Hammah inji Innah ka shigo gidane?"
Ya gyad'a kai kamar tana kallon sa sannan yace "Eh."
Yana jin tana fad'awa Innan sai kuma tace "Tace wai ka kulle gida."
Ya miqe yace "Kice mata saida safe toh."
Ta amsa da "toh,saida safe."
Suka katse wayr a tare yaje ya kulle gidan sannan ya dawo yazo ya kwanta ya rugungume pillow kamar wanda za a kwace masa a haka yayi addua har bacci ya kwashe shi cikin wata irin nutsuwa da farin ciki.
***
Da daddare Alh.Ayuba Buba ya dawo gida yayi wanka yana cin abinci Abdulraheem ya shigo falon da sallama.Suka amsa ya zauna yana cewa "Wash na gaji."
Alh.Ayuba yace "Ba dole ka gaji ba kullum kana garari a gari anyi anyi ka kama aiki ka zauna wani karatu."
Haj.Maimuna tace "Haba dai Abban Abdul yaron naka nawa yake."
Dariya yayi yace "Ai kaji irinta,kullum uwar ka na kare ka tana cewa nawa kake sai ka tsufar mana a gida tukunna."
Dariya yayi yana kallon Haj.Maimuna yace "Mummy na gaskiya take fada nawa nake."
Alh Ayuba yace "Shikenan naga bakin ka na motsi fadi muji meke tafe dakai."
Yaja kujerar dinning table d'in ya zauna sannan yace yana kallon sa "Abbah aboki nayi dan nigeria ne shima yazo masters kuma dept daya muke,to yana appartment ne na makaranta shine nace ko don Allah zai dawo nan tunda kullum ina jin babu dadi banda abokin shawara banda dan uwa zan dinga kallon sa kamar yaya na pleaseeee Abbah."
Shiru ya danyi shiru na tsahon lokaci har saida Haj Maimuna ta zungure shi sannan yayi firgigit yace "Oh Okay zan bincika naga wanne irin yaro ne kafin na dawo dashi gidana."
Miqewa yayi tare da fad'in "Yessss thank you Papa." Yana maganar ya fice daga falon.
Alh Ayuba ya tsame hannun sa daga kwanon abincin ya miqe shima yayi dakinsa ba tare da ya sake kallon inda matar ta sa take ba,ta bishi da wani kallo dana kasa gano manufar sa ta jima zaune a wajen kafin ta miqe ta bi bayan sa.
💦💦💦
Yau Immileey da wanki ta tashi saboda tana son hada kayan ta duka a washegari don kar tayi mantuwa.Kayan ta ta kwaso na datti wanda tasa bata wanke ba a ciki ta dinga tsintar na Baby Eve,ta ware su gefe guda kawai sai ta zauna ta rumgume su tana kuka,tun faruwar abun yau ne ta samu tayi kuka mai isar ta yanda taji zuciyar ta ta saki ta jima a wajen kafin ta tashi ta hade su ta fita dasu tsakar gida ta soma wankin.
Goggo Lari na lura da yanda yanayin ta ya canza sosai amma bata mata magana ba don dai tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi duk suka yi jigum jugum ita tana ta wankin ta itama Goggon tana ta ayyukan ta,sallamar su Jannah ta katse shirun sune suka soma hira da Goggo Immileey na jinsu.
Mooha ma basu jima da shigowa ba shima ya shigo cikin kayan fulanin sa,ya zauna yana harde kafa ya bude kwanon saya shigo dashi a hannun sa,Amnah tace "Mene wannan kuma?"
Yana dariya yace "Taliyar hausa ce karki ma leqo bakya ci,kuma ba kwadayayyen da zan ba."
Abin ya bawa Immileey dariya don tasan da ita yake don yasha ya ganta tana ci a kano ya lallabata ta sammasa sai sun gama yaita tsokanar ta da kwadayayyiya mai cin manja da yaji,yawanci Mummy ke tare mata bata magana sai dai dariya idan en shagwabar kuma na kusa tai tayi kamar zatayi kuka shi kuma jin dadin sa kenan.
Ganin tana dariya ya sashi yin dariyar shima kana yace "Immileey kina ci ne?"
Ta juya tana kallon sa tana murmushi tace "Aa na qoshi."
Goggo da take taya su dariyar tace "Kaga ko ka tuna min yarinyar nan yau bata ci abinci ba tunda ta tashi banda wani guntun koko shima saida na mata da gaske."
Ya kalle ta yana waro manyan idanuwan sa yace "Whatttt?me nace miki?"
Ta turo qaramin bakin ta gaba tana cewa "Nifa......."
Bata qarasa maganar ba akayi sallama aka shigo,sai tayi difff kamar wadda ruwa ya cinye don sam baza ta manta muryar ba.
Can qasan maqoshin ta tace "Yafendo?" Kafin ta dago a hankali tana kallon ta saidai ba wanda zaice ita take kallo.
Bayan ta faccalar tace da surukanta harda Ladingo da fuskar nan tayi kamar ta bauna saboda hadewa.
Goggo ta amsa sallamar cike da karamci ta yi musu sannu da zuwa sannan ta shimfida musu tabarma suka soma gaisawa cikin girmamawa kamar babu wani abu da ya gifta a tsakani.
Yafendo ta gyara zama ta soma magana da "Zuwa mukayi mu dawo muku da Hauwa'u kuma mu baku haquri akan abinda ya faru wallahi ba da gayya aka yi ba."
Cikin mamaki Goggo Lari tace da Amnah taje ta kira Innah Aziza,tare suka dawo hakan yasa Goggo Lari sake yiwa Innah Aziza bayani.
Duk da taji dadi sosai don har er qwalla ce ta zubo kata hakan bai hana ta cewa "Toh maganar nan dai ta su Baffah ce kai Muhammadu jeka kira Baffan ko yazo yaji ka taho ma da da Baban su Auwal (Ilah mijinta babban yayan su Immileey) idan suna tare.
Mooha ya miqe yana cewa "Toh tare da kallon Baby Eve dake ta yunquri tana son zuwa wajen sa."
Da sauri ya fice Immileey kamar wadda aka dasa a wajen da take wankin haka ta zama saida Jannah taje ta janye ta bisa umarnin Goggo Lari sannan suka shige daki ta zaunar da ita bakin gado kawai sai ta saki kuka wanda ita kanta bata gane ko na meye ba.
ZahraArkel ce!