BAUCHIN YAKUBU
Janna! ke janna! ina miki magana wato bazaki sake shi ba. wata budurwa na gani ta makure wani saurayi sai kokarin kwace wa ya ke yi ya kasa da kyar aka samu aka raba su wallahi in ka kara zuwa kofar gidan mu sai na maka Wanda yafi wan nan. to ja'ira maza wuce ciki, kifin na fasa miki baki. ta wuce ciki tana kunkuni Dan Allah Malam kayi hakuri, no ba komai, yashiga mota jiki na rawa ya bar gun
Mama ta shigo gida tana fada
Wato ke jannah baza ki ta ba jin gari ko ban ce in an zo gunki zance karki kara kama samarin da fada bah ,ke kokuwa a gunki ya zama ruwan shan ki sai kace da namiji, to wallahi ko kibar halin ki ko kuma wataran ki gamu da mai miki duka , a haka ne ma zaki samu mijin auren bayan duk Wanda ya zo gunki saikin jibge shi, to wallahi kisan kin girman ke be kan kanuwan yarinya bace,Dan kawai kina jinki da karfi ki kama maza kina jibga , jannah bazaki samin hawan jini ba a garin nan. ki dube ki mace har mace amma maza suna tsoron miki magana. to mama bayan shi yaja, shine fa ya........ Ta tafi numfashinta Ya me? kullum in an tambaye ki kice wai shirya ja, dallah tashi ki je ki yi alwalan magriba kiyi sallah. ta tashi ta bar gun tana gun guniAisha Aliyu (jannah)
Diya CE ga Malam Ali, tsohon maaikacin gwamnati ne me ritaya , malam Ali yana da yara uku Asmau,Hashim da Aisha Wanda ake kira da jannah. matan shi Hajiya bilkisu. Malam Ali Dan asalin garin Azarai ne, it a kuma matan shi yar darazo ne amma suna zaune ne a garin bauchi Malam Ali yana da arziki daidai gwargwado. Diyarshi ta farko Asmau ta yi aure,ta auri sojan ruwa suna zaune a Lagos yaran ta biyar , ta haifi yan biyu maza da farko ta kuma haifan yan uku maza biyu mace daya . shi kuma Hashim ma aikacin banki ne be yi are bah , Jannah kuma ta gama makarantar secondary har ta jona state university dake bauchi, tana karatu fannin sociology.Ainihin labarin
Ya'u janna ta tashi da matsanan cin ciwon ciki a sanadin al'adan da take yi wato (mensturation) abunda bata taba yi bah tana kwance Maman ta shigo.
ESTÁS LEYENDO
IZUDDEEN
Ficción GeneralLabarin wani matashin Attajiri Wanda baya ganin girman kowa, daga baya kuma mace ita ta koya masa hankali ta saita shi ya gane zaman duniya