page 1

17 2 0
                                    

👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻

           *SURUKARMU CE*

👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻👵🏻

*Book 2*

*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*🤝🏻
________________________________
*We are here to educate motivate entertain our readers*
_______________________________



*BISMILLAHIR RAHMANIRRAHEM*



*Zan cigaba da kawo muku cigaban book dinnan amma gaskiya zan fi sakawa a wattpad dina,dan haka duk sanda nasa zandinga turo link din dazaku samu damar zuwa ku karanta.*



*Page 1*
Inna Larai tana futa waje tahau yin kuru ruwa tana ihu, nan take mutane suka nufo indda take suna tambayarta lafiya kuwa? Bata yimusu magana ba tanufi cikin gidan dan haka suma suka rufa mata baya zuwa cikin gidan, dakin Bilkisu tanufa suma suka rankaya ciki.

Ganin Bilkisu tanata jijjiga abban su wanda ko motsi bayayi tana kuka ga Sani ma akwan ce agefe ne yasa mutanan sukayi kansu da gaggawa, Inna Lairai tana kuka take magana,"Wasu ne suka shigo gidan suka kulle mu adaki sukayiwa Bilkisu fyade su biyu suka kashe Sani ganin haka yasa malam shima ya yanke jikinsa ya radi matacce". Salati kawai mutanan gun suka saki, wanda yake kan abban su Bilkisu yadago kai yace, "Bai mutuba yana numfashi, kuyi maza mu kamashi akaishi asibitin cikin gari, kaikuma malam Audu maza kaje asanar da mai gari dan ayiwa Sani sutura akaishi makwancin sa, kekuma Larai ki kula da Bilkisu". Jin wannan bayanin da akayi saida yasa Inna Larai ta sandare bahaka tasoba Sam.

Nan da nan aka kinkime shi suka fuce dashi ragowar kuma suka futo da Sani suka shin fude awaje.

Bilkisu jin anje abban ta bai mutuba tadan ji sauki ta wani fannin, hakan yasa ta rarrafa zuwa gun kayan ta tacire zanin gadon data lillibe jikinta tasaka doguwar riga ta futo tsakar gidan, inda ta zauna kusa da gawar Sani tana kuka mai matukar cin zuciya.

Nan da nan zance ya kaure cikin garin, mutane sunata zuwa dan ganewa idonsu harda yan gulma, duk wanda yashigo inna Larai saita sanar dasu cewa an yiwa Bilkisu fyade ko ajikinta.

Nan da nan akayiwa Sani wanka aka kaishi makwancin sa na gaskiya, mutane sai kallon Bilkisu sukeyi suna surutu kasa-kasa, yayin da ita batama san abunda sukeba tana tunanin abunda yasame ta alokaci daya.

Sallamar mutane ce tadawo da Bilkisu daga dogon tunanin data fada, wadan da suka tafi kai mahaifin ta asibitin burni ne, sun dawo dauke da mahai finta, cikin azama ta mike tanufi inda suke tana jero musu tambaya, "Mai mutuba ko? Yadawo dai-dai ko?". Daya daga cikin su yace, "Fara yimasa shin fuda acikin inuwar nan tukun". Cikin azama tashiga dakinta ta dakko tabarma da bargo da fulo ta shinfida suka kwantar dashi.

Inna Larai dayaran ta suma suka zo gun suka zazzauna, daya daga cikin mutanan yafara magana, "Likita ya dubashi yatabbatar mana da dama can yanada ciwon hawan jini to jinin nasane yayi mumman hawa saikuma zuciyar sa data yi kokarin bugawa amma  sunso kwantar damu, saboda kudin da sukayi yawa yasa mukace su salla memu za'a kula dashi agida, ga magun gunan sanan Larai ki kula dashi sosai dan Allah kar adinga yawan bata masa rai ko abunda sai sosa masa rai, kudin da aka kashe kuma kyauta muka biya karkuji komai yanzu mu zamu tafi".

Inna Larai tayi karaf tace, "To mun gode zan can bacin rai kuma ai saidai kar akara ayiwa yarka fyade har mutun biyu aikunsan zaiyi huya ya manta, shiyasa ma nace wa kowa bazaman makoki tunda ba abincin basu bane da mu".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 11, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SURUKARMU CE book 2Where stories live. Discover now