*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
2⃣5⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
Alhamdulillah anga wata kowa yayi jajibir in shi dai dai karfin shi,
ko wane gida sunata shirin abincin sallah kamar gidan Hafsat da tinda yamma suke gyaran kayan miya , sun gyara komi nasu nayin abinci sallah tareda Nafisa sukayi aikin kasancewar tazo yin sallah gida.Washegari tinda asuba suka tashi suka fara aiki, sune basu gama ba sai wajen karfe 9 , tin kafin su gama Nafisa ta fara shirya su Iman ,suna gamawa suma sukayi sauri sukayi wanka su a lokacin tuni Habib ya shirya shima cikin shaddar su wanda sukayi anko , itama Hafsat bayan tayi wanka ta sanya shaddar ta dukan su kayan su kala daya ne , sunyi shirin su tsaf sannan suka tafi sallah i'di, Hafsat da Habib ne gidan gaba tana rike da sudais , a bayan motar ko Nafisa ke rike da uneisa, su Muslim suna kusan ta, suna tafe suna hira har suka kai masallacin idi, suna zuwa ana shirin tada sallah saboda sun makara, ba bata lokaci kowa yayi nashi bangaren da zaya sallah shi , Habib ya tafi da Muslim su kuwa sauran sukayi wajen da mata suke ,
A bangaren su Samira kuwa suma tinda safe suka girka abincin su , sannan suka zubo sukaci abincin, bayan sun gama cin abincin sai sukayi shirin zuwa masallaci, kasancewar da d'an nisa daga gidan su zuwa masallaci sai suka shiga adedeta sahu , sun dan jima da zuwa sannan aka tada sallah ,
Suna dawowa daga sallah bayan sun dawo gida sai Samira ta tafi gidan su kawarta zainab wajen yi masu barka da sallah , tana zuwa kuwa suka gaisa da maman zainab sannan sukayi daki itada zainab , bayan sun shiga daki ne zainab taceda ita
"ma voisine (my neighbor) ya banga kwalliyar sallah a fuskar ki ba"samira tace
"ni fah kinga bani son wannan kwalliya ba gashi ba na shafa poda da kwalli ba"zainab tace
"kin ma yi magana , ni dai tashi in maki ko simple ce kinji"Samira tace
"ni fah bi barni haka "Zainab tace
"haba amaria Habib please taso mana ko so kike yazo ya tadda bakiyi kwalliya ba"
Da kyar dai ta yarda akayi mata makup mai dan karan kyaw ,nace mashah Allah ashe dama Samira haka take ban sani ba, shiyasa iya tace sai shegen kyaw ashe ita ta sani , lalle yaw na kara tabbatarwa da Habib yayi mata biyu masu kyaw da uwar gida ga amaria.Suna gama kwalliya ta nada dan kwali mai kyaw sannan tace su zo suyi selfie , bayan sun gama ne kuma sai tayi ma Samira ita kadai , tayi kyaw gaskiya babu karya .
Sunyi hoto babu laifin sannan ta maida hijabin ta saman kayanta akayi mata da hijabin ta , wajen kala biyar , suna gamawa sai ko ta turawa habib hotunan ta whatsapp , a lokacin da kuma ta tura mashi suma a lokacin suna can suna nasu hoton .Bata jima ba sosai a gidan sannan tayi masu sallama ta tafi gida zainab ta rakkata , tace itama bari ta biya ta gaida inna tinda samira ta rigayeta zuwa , suna saman ne take cewa da zainab
"ma cherie( my dear) na mance ban fada maki ba yace banda gobe abokan shi zasu zo tareda ku , ku shirya yadda zakuyi events da kuma abinda zasu baku"Zainab tace
"ok zan fada ma sauran kenan sai ki fadawa maqwaftan ki, ko mu 6 ne mun isa saboda kar muyi yawa"Samira tace
"haka ma yayi"suka cigaba da hirar su har suka kai gida ,
*Gidan Alhaji Habib*
Bayan sun dawo daga sallah suka zo suka ci abinci kasancewar basu samu damar cin abincin ba saboda sun makara a aiki, bayan sun gama cin abinci ne Hafsat ta zubawa maqwaftan ta aka kai masu , sannan suka gyara kwalliyar su , suka fara daukar hoto, da wayar Habib , sun sha hotuna babu laifin sunyi kyaw abun su kamar ka sace su ka gudu,
VOUS LISEZ
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
Roman d'amourSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...