Page 26

650 38 7
                                    

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟

2⃣6⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

Assalam Aleikum fans kunga al'adar garin mu a cikin wannan page , dan jin dadin karatu bari in d'an fahimtar da ku wani abu wasu abubuwa  *kumshi* ana yin shi ne ranar da amaria ta shiga lalle, tafya ake gidan su aboki ko kuma dan uwa sai ayi ma angaye abinci su zo su dauka su bada kudi, *Kudin abincin break na yan mata amaria* ana basu su in amaria ta shiga lalle su rika break da su har ta fita duk da ana break gidan amaria, *kudin abincin ran biki* su ma ana ba yan mata amaria ne su dan suyi girki ranar biki in basu bukatar abincin da iyaye suka dafa , sannan *damu* shi kuma a washegarin da amaria ta tare aka kai ma angaye fura ko yagourt su sha su bamu kudi😅😅, da fatan zaku gane al'adar mu.

Bacci da basuyi ba tare ba, saboda Hafsat taso ta nuna mashi ita bata ma ga komi a wayar shi amma sai gashi ya gani saboda ita kwata kwata ta mance bata fita dqga inda keda hotunan Samira ba,  amma dan ya raina mata hankali shine wai hada hakuri yake, to wai ma hakurin mi zai bata tinda ita keda ikon shi ba, abu daya ta daukar wa ranta mudin yarinya bata girmama ta ba sai ta shayar da ita mamaki, shiyasa kawai ta dawo daki duk itama tana bukutar bacci a tareda shi.

Ya dan jima yana juyi kafin bacci ya dauke shi yana so yaje ya rarrashe ta amma kan shi yake mashi mugun ciwo kamar zai tarwatse , har ya samu a
bacci ya dauke shi,

washegari da ta tashi nuna mashi tayi kamar ma babu abinda ya hada su jiya da dare, suka sake girka abincin da zasu kaiwa yan uwa da abokan arziki na nesa saboda jiya maqwafta ne kawai suka kaiwa abincin da suka girka, suka sake shirin su yaw ma materiel suka sanya mai azabar kyaw ,  sunyi kyaw abun su sannan sukaci abinci saboda a lolacin har 12 na safe tayi , yaw ma Habib ne ya kwashe cikin motar shi suka yayi gidan su , bayan sun zo an gaggaisa sannan aka fiddo abincin da suka zo da shi akayi rabo zuwa yan uwan su Habib .
Shi kuwa Habib bayan ya fita daga gidan su gidan malan tsoho ya nufa domin yi mashi barka da kasancewar jiya bai samu damar zuwa ba, a can ya tardo babyn shi su ma sun zo , yaw tayi kyaw cikin wata atanfa yar cote d'ivoire , mashah itama tayi kyaw sosai duk da batayi wata makup sosai ba daga poda sai kwalli sai man lefo, Habib yaso su dan kebance da ita amma ba dama , haka dai yayi masu sallama ya tafi, suma yaw gidan malan tsoho suka yini sai kusan magriba suka koma gida.

Washe gari ma Hafsat a gidan su ta yini , can ma ta kai masu abinci kamar yadda tayi gidan su Habib .

Bayan karfe 3 na rana lokacin da zainab zata tahowa gidan su Samira tare suka taho da mama ta saboda tana son ganawa da inna suwaiba game da auran Samira, bayan sun gaisa ne take fada mata abinda ke tafe da ita. Aiko saida inna suwaiba tayi hawaye lalle wani lokacin abinda d'an uwan ka na jini zai kin yiwa ka shine bare zai maka, lalle wanan mutane sunada mutumci, mi zata cewa, bayan Allah ya saka masu da alkairi, inna suwaiba tace
"nagode nagode sosai Allah yasaka da alkairi "

mama zainab tace
"haba maman Samira ai Samira ma y'a take a gurin mu wlh inada niyar yin haka , kawai ina zaune sai Alhaji yake cemani mi zai hana mu dauke daurin auren Samira, wlh bakiji yadda naji dadi ba , sai kawai nace bari in zo in tambaya kar azo wani ya kama duk da nasan dangin baban ta basa garin shiyasa nace bari dai inzo"

inna suwaiba tace
"inshah Allaku ku zaku daura mata aure ,in dangin baban ta sunzo zani fada masu gidan ku ne za'ayi daurin aure "

Mama zainab tace
"to mun gode da karramawar da aka mamu, ta kara da cewa kuma ana saura sati biki Samira zata rika zuwa ana mata gyaran jiki nan gidan mu , "

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Where stories live. Discover now