SANADEEN BIKIN SALLAH!!🤦♀
Bilyn Abdull ce
NIKA'DAI WRITER ASSO......🤪
Gajeren labari......✍🏿
1⃣
Masallacin cike yake damk'am da mata, matasan 'yan mata dattijai, harma da zawarawa da tsoffi.
Malam sai kwarara addu'oi yakeyi, kasancewar yaune za'a rufe tafsirin massalacin.
Tsit masallacin yake, tamkar babu wani mahaluki, sai jefi jefi sukan amsa addu'ar Malam da ameen, saikuma yara dake wasa harma damasu k'aramin kuka (saboda takurasu da akayi akan zaman waje d'aya.Zaune nake agefe kusada wani gungun matasan 'yammata, ak'alla sunkai su 8, tunda suka shigo atare suke, hakama wajen zama d'aya suka samu, sumadai sukan amsa addu'ar Malam d'in da amin.
Tsawon mintuna 50 Malam na addu'oin har aka kammala, tareda sallamar kowa.
Ananne aka fara k'ananun hayaniya, wasuna yunk'urin ficewa daga masallacin.
Kasancewar muna kusan tsakkiya da 'yammatan nan yasa bamuko motsaba, munajiran nawaje sufara fita dana bakin k'ofa.
Hankalina yanakan danna wayata, Dan ina k'ok'arin saving d'in tafseer d'in yaune danayi recording d'insa.
Firar 'yammatance tad'an fara Jan hankalina garesu, saidai kafin naji misuke fad'a harsun fara mik'ewa, kasancewar anragu sosai acikin masallacin.
Da sauri namik'e nima natake musu baya, Dan inasonji hirartasu.
Aiko kusan atare muka fito harabar masallacin.Tafiya muka farayi.
d'aya acikinsu tarik'e k'ugunta tareda yin k'aramar mik'a tana fad'in wash ALLAHna! Yaukam mun zaunu wlhy, malamin nan kamar bazai sakemuba.
Dariya mafi yawansu sukayi, wadda ke gefenta tad'an daki bayanta tana kiran ragguwar banza, ALLAH zee mijinki yashiga uku, koda yake jabeer ne.
Wani wawan tsaki wadda aka kira zee taja tareda ballama mai maganar harara, cikin 6acin rai tace bar had'ani da wawannan mana, ai wlhy *_Sanadeen bikin sallar_* nan nidashi kowa zaikama gabansane.
Ido suka kwalalo suduka, Hafeeza ta ce, zee anya kinada hankali kuwa? Asamiki biki damutum amma kice zaku rabu *_sanadin bikin sallah?!_*.
Mtsooww yo ALLAH natuba Hafeeza saime idan mun rabu?, ace wai kana shirin auren mutum amma yagagara maka d'inkin sallah. Jiya yazauna saiwani tsarin banza da wofi yakemin.
Hanci khadeejah tahuro, cikin 6acin rai ta ce, "wlhy zee ina bayanki, narantse da Al'kaseem yayi gigin k'in yimin d'inkin sallah dayaga jakar uba, Dan tun aranar zamuyi walle-walle, to amma ALLAH yataimakesa jiya yayarsa takawo kayan gidanmu. Amma dukda haka saimun yita, Dan kala 5 nayi dashi amma yakawo 3........
Takusa da itace mai suna yagana takatseta da fad'in dak'yau khadeejarmu kina wuta wlhy, ai mazannan wutar karane Saida iji narantse.
Maryam ta ce, hummm wlhy kudai kubi asannu, kada kuyi nadama a *_Sanadin bikin sallah_*.
Wata uwar harara saudah ta watsa ma Maryam, to ustazu munji, kedama aii Ibraheem yasaba rainamiki hankali damaidaki baya cikin k'awaye, shekara biyu dakai kud'in aurenki amma ko sark'ar sallah baita6a siya mikiba.
Baki Maryam ta ta6e tana fad'in aibadan wannan nakeson saba, inasonsane domin ALLAH, *_Sanadin bikin sallah_* bazan haddasa fitinar dazan dawo daga baya ina nadamaba.
Wata shewa Bilkeesu tayi tanawani fari da idanu datafiyar k'asaita, mudai mun wuce wajan, Dan kowa yasan my Mahfouz akwati guda yamin na kayan sallah, har lallen kunshi Saida yasaka aciki.
Wani uban tsaki Ameena tayi tareda fisgar hannun Taufeek'a tana fad'in kankudai akeji marasa aikinyi kawai.
Gaba d'aya suka shek'e da dariya tareda tafawa suna fad'in jealousy ooooo!!!!!.
Cikin hanzari Taufik'a takwace hannu ta daga na Ameena tana fad'in uban miye abin jealous agurinku? Banzaye kawai, aii maiyi baya fad'a, kowa yabari sai ranar sallar mana, aiza'a tantance *_WAYE WANE!!?._*
HHHHHHH khadeeja tasa dariya, takoma gabansu tana wani jijjiga kai, gskyarki Taufee, shiyyasa nake sonki, Dan kanki akwai kawo wuta wlhy, wannanma shawarace.
*_sanadin bikin sallah_* za'asan kowa shi waye?.
Dariya suka shek'e da ita suduka.
Hafeeza tace kai dukma Ku tsaya, yaushene zamuje gidan mai k'unshin?.
Bamunyi da'ita alhamis ba cewar Bilkeesu.
Eh hakanefa zee tafad'a tana dafa kafad'ar Bilkeesu, tace to yau suwaye za'a farama kitson?.
Da sauri Maryam tace kuma kunsan nice, daga nan sai yagana.
Ameena tace wlhy yagana da maryam muna fukaine, kutunafa barama sune farkon kitso.
ALLAH tsine uwar mai k'arya cewar yagana cikin masifarta.
Saudah ta ce, ''kai yagana, nifa matsalata dake saurin fushi wlhy, daga fad'ar haka miye abin tada jijiyar wuya?.
Bansaniba cewar yagana afusace.
Zee Ce tashiga tsakani dantasan ayanzu saisuyi sama.Kunga ya isa haka mana, yanzu kumuje rana na k'arayifa, kuma akwai meeting yau Dan bamu tsara da'ina da ina zamujeba.
Hakanefa!!! Suka fad'a arazane kowa nak'ara saurinsa.Nace hummmm🤔.
Cakwakiya.
YOU ARE READING
SANADIN BIKIN SALLAH!!
Short StoryYanda ƴammata ke mancewa da kansu da martabarsu a yayin bikin sallah, burinsu su haska kawai wajen samari, ko ina suka zagaya a yabasu su da kwalliyarsu, ajiye al'ada da addini dan kawai ace kaine wane, bin kowacce hanya wajen neman kayan bikin sall...