BABI NA SHA BIYU

465 16 0
                                    

Hey readers!!

There is this song that i have been listening too while writing this chapter,i don't know whether you guys can also download it and listen to it while reading it..Trust me is going to be fun😁.The name of the song is.

Wait for me by Johnny Drille

A nat'se yake tuqin motar sa bayan ya baro gidan su Maryam zuwa gida,duk kuwa da tarin abubuwan da ke cunkushe a ransa

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

A nat'se yake tuqin motar sa bayan ya baro gidan su Maryam zuwa gida,duk kuwa da tarin abubuwan da ke cunkushe a ransa.

Ba ya san ya chusa wa ransa damuwa game da al'amarin,sai dai hakan na nema ta gagare shi,domin yarinyar kara dama mishi lissafi take yi tare da hanashi sukuni da yadda yake jin ta a ran sa,in yana tare da ita manta wa yake yi da kowa da komai da ke kusa da shi,sai ita kwalli kwal...

Da wad'annan tunanin ya iso gida,a masallacin kofar gidan su ya yi fakin,don gabatar da sallar magriba da bai samu yayi ba tare da issha'in da ake ta kira..

Sai da ya idar,yayi adu'o'in sa,sannan ya karasa cikin gidan su, bayan mai gadi ya budo masa gate had'e da mai sannu da zuwa,hannu kawai ya iya dag'o masa,ka na ya fake motar sa a rumfar ajiye motoci,cikin yanayi na kasala ya fito daga motar bayan ya kullo ta.

A wannan lokacin babu abinda yafi bukata kamar ya karasa bangaren sa don ya samu hutu,tare da shigewa cikin bargo sa wajen tunanin ta yadda zai bullo wa al'amarin,da nemawa kan sa mafitar abinda ke damun sa,kan shi ne ya ji yana dan sara masa,ga sanyin da yake jin yana shiga jikin sa sosai.

Amma ya san rashin shigar sa zai iya sa iyayen sa shiga damuwa tare da tunanin ko bai dawo bane,tun da bai saba haka ba,duk inda ya je ya dawo sai ya shiga wajen su,sun gaisa,kafin ya musu sallama,ya koma bangaren sa..

Karasawa bangaren su yayi ,da sallamar sa ya k'ut'so kan sa cikin falon,Najib ya gani a zaune kan kujera shi kadai,hannayen sa rike da control pad yana buga Game a PS 4 din sa,yayi nisa cikin bugawa bai ma ji sallamar sa da shigowar sa ba.

Wani haushi ne ya turnike shi,ko kadan basu cika jituwa da yaron ba,sabida rawar kan sa,ga wasa da yayi masa yawa,uwa uba rashin bai wa ibada muhammanci,shi ya sa bai so aka siya masa Game din ba tun farko,ko a da baya maida hankali wajen karatu balle yanxu da yayi Game ai sai abinda ya k'aru,amma in yana mai fad'a,sai su Umma ga kamar dan baya san sa ne,basu san halayyar sa ce baya so ba,ya san yanxu haka yadda ya ke ta Game dinnan,kila ko sallah bai tashi yayi ba

Had'e fuska yayi kamar wanda bai taba dariya ba kafin ya yi magana

"Kai baka ji sallama ta bane,da baka amsa ba,ka tasa Game a gaba kana bugawa?"

Juyowa Najib yayi a dan razane da jin muryar sa,dan bai yi tsammanin akwai wani a falon ba bayan shi,tsayar da Game din yayi,tare dan yin yak'e na marasa gaskiya,sannan ya ce

"Kayi hakuri Ya Ya ban ji shigowar ka bane"

Kara dak'una fuska yayi,ya sake fadar

"Dama ina zaka ji kana wannan Game din naka da bai karewa,shin kama yi sallah kuwa?"ya ke sake tambayar sa,tare da t'sare shi da idanuwan sa...

K'ADDARA TA Where stories live. Discover now