DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:_mhiz_zahra_arkel.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
*Assalamu'alaykum barkan mu da warhaka,dafatan mun yi azumi mun gama lafiya Allah ya karbi ibadun mu yasa muna cikin entattun bayin sa,ina ma daukacin en uwa musulmi barka da sallah dafatan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana cikin aminci da yassarewarsa amin.*
EID MUBARAK EVERYONE❤️❤️
3️⃣4️⃣
Ko mintuna hudu ba a cika ba Baffah da Ilah suka shigo tsakar gidan tare da Mooha a bayan su.Saida suka zauna sannan suka gaisa cikin girmama juna sannan Baffa ya dora da "Ance inzo Allah yasa dai lafiya."
Yafendo ta karkata kai don sosai take jin nauyi da kunyar bayin Allahn nan dubi dai abinda akayi musu amma ko a fuska basu nuna ba lallai sun cika masu karamci da dattako a duniya,cike da jin kunya tace "Dama Hauwa'u ce muka dawo da ita kuma muke sake bada haquri akan abinda ya faru sharrin shaidan ne."
Wani murmushi Baffa yayi har ga Allah yaji bala'in dadi har ransa amma sai ya kanne ya danne yace "To shikenan Allah ya rufa asiri ya kuma raya ta rayuwa mai albarka."
Duk wajen aka amsa da amin sannan Yafendo ta sake cewa "Ta samu kiwo da yawa a wajen mu don haka gobe za a kado dabbobin a kawo saboda mahaifiyar ta gani kafin su koma tunda naji ance tafiyar sai jibi ko?"
Goggo Lari ta amsa wannan karon tace "Allah ya kaimu,Eh sai jibi idan Allah ya kaimu."
Yafendo tace "Allah ya kaimu,mu zamu koma."
Duk suka miqe lokaci guda,Suka ajiye kayan Baby Eve,Mooha yayi saurin dauke ta yana cillata sama yanda yake mata ta soma dariya sosai saidai yanda ya santa da girma da nauyi duk babu ya rumgume ta a qirjin sa yana ji tana ta sauke numfashi kamar tasan meke faruwa sai ya tsinci kansa da share hawaye a ran sa kuma ya quduri niyyar komai nata ya dawo hannun sa don haka ma yana komawa zaiyi wa Abeey dinsu maganar aikinsa saboda ita.
A haka Baffa ya dawo ya same shi da ita,cikin sigar tsokana yace"Muhammadu mayar musu da ita fa za ayi."
Da sauri ya dago kan yace "Haba Baffa."
Duk suka kwashe da dariya sannan shima Baffan ya miqa hannu da niyyr daukar ta amma qememe taqi sai ma ta kwantar da kanta a qirjin sa tana kallon mutanen tsakar gidan daya bayan daya kamar mai son tantance su.
Baffa yace "Er nema ni zaki yiwa qiwa."
Jannah nq dariya tace "Fushi take Baffa baka je zance ba tunda ta tafi hutu."
Duk aka saka dariya Goggo Lari tace "To me zaije ya gani a wannan kodaddiyar fatar tata ai ba kishiya a gidan nan."
Suka sake saka dariya sannan Mooha yace "Aa Goggo fadi gaskiya kodai fatar nan ita ke tsorata ki shiyasa kika kora ta can."
Baffah yayi dariya sosai ya fice yana jin su baice komai ba,hira suka cigaba da yi tsahon lokaci kafin Mooha ya miqe ya shiga daki ya tadda Immileey zaune a qasa ta hada kanta da gwiwoyin ta tana zaune shiru da ita kana kallon fuskar ta kasan taci kuka.
Saida ya zauna sannan yaja qafafunta ta ware su ya dora mata Baby Eve data gama gane mahaifiyar ta,ta soma wasa da fuskar ta yanda take mata idan tana shan Nono cikin rashin tsammani sukaji tace "Maamah."
Kamar wadda aka kwarawa ruwan qanqara tsakiyar sanyi haka ta firgita kafin tayi mata wata wawiyar rumguma tare da fashewa da kuka duk lokaci guda,shiko Mooha mamaki ne ya sandarar dashi don shi har yanzu qanqantar ta yake gani sosai gani yake yayen da akayi mata ma don dai ba yanda zaiyi ne da bazai yarda a yaye tan ba.
Kuka tayi sosai wanda bai hana ta ba bai yi kuma yunqurin lallashin ta ba saida Baby Eve ta fara saboda matsar da tayi mata tayi yawa kamar zata maida ta ciki sannan ya banbare ta ya miqe yaje ya miqawa su Jannah ita ya koma,duk abinda yake Goggo Lari na lura dashi amma sai ta qyale su taga abinda zai faru kuma.
Ya zauna a gaban ta ya tanqwashe qafafuwan sa yana kallon yanda hawayen ta wasu ke korar wasu yana murmushi yace "kuka baya miki kyau Baby Girl."
Da sauri ta dago tana kallon sa jin sunan daya kirata dashi,ya kashe mata ido daya yace "Har yanzu ke baby ce ko don kinga kin ajiye Baby Eve?"
Ta kauda kanta bata yi magana ba amma hawayen sun soma raguwa,ya sake cewa "Ni yanzun dalilin wannan kukan nake son ki gaya min meya saki kuka haka?"
Share hawayen daya zubo mata tayi tare da jan majina tana kallon qofar shigowa ta girgiza kai kawai.
Dariya yayi yace "Nasani,amma ya kamata ace murna da tsalle za aga kina yi."
Da sauri ta juya tana kallon sa ya daga kai yace "Yes,ke ai baki da kunyar fulani kina nuna son diyar ki a gaban kowa ma don haka ya kamata kiyi tsalle tunda an dawo da ita sun gane basu kyauta ba ko?"
Zumburo baki tayi alamun shagwaba amma still bata ce komai ba,ya jima yana kallon abinda take cikin wani irin shauqi kafin yace cikin sanyin murya "Ya kamata yanzu ki daina yawan damuwa da abubuwa da yawa,ki sani komai qaddara ne Allah ne ke qadartawa bayin sa dukkan rayuwar su,kuma Allah yana jarabta bayin da yake so ne a cikin bayin sa,ki zama mai godiya da dukkan jarrabawar sa zaki sha mamaki a gaba."
Murmushi tayi har manyan dimples dinta suka lotsa tace cikin wata siririya kuma dusasshiyar murya "In sha Allah nagode."
Wani yarrrrr yaji don muryar ta ratsa shi,a ransa yace "Allah yayiwa yarinyar nan baiwa da yawa idan har na tsaya kallon ruwa ta girma lallai kwado zaiyi min qafa dole nayi wani abu kafin wani ya shigar min gaba."
Dagowa tayi jin yayi shiru kuma jikin ta ya bata ita yake kallo,karaf suka hada ido tayi saurin cire nata daga cikin nasa don ba qaramin ladabtar da ita manyan idanuwan nasa keyi ba ta miqe tace tana jan yatsun ta "Bari naje na qarasa wanki na kada yamma tayi min."
Bata jira amsar sa ba tayi saurin ficewa,ya jima yana kallon inda ta bi sai ka rantse itace a wajen kafin ya miqe ya fice tsakar gidan,turmi yaja inda take wankin ya soma taya ta da sab'i na biyu bata kula shi ba haka bata kalle shiba har suka gama ta dauraye ya shanya wasu ta shanya wasu sannan tace "Nagode."
Murmushi yayi yana kallon ta ta juya,Baffah dake fitowa daga dakin sa yace "Mallam Muhammadu kenan ana nan ashe."
Dariya yayi yana sosa kai yace "Eh Baffa munyi wanki ne da Immileey."
Yayi dariya yana kada kai yace "Yayi kyau Allah ya taimaka ni na tafi kasuwa saina dawo."
"Allah ya kiyaye hanya." Ya bashi amsa yana dan russunawa alamun girmamawa.
Yana shima yayi musu sallama ya fice,Inna Aziza ta karbi Baby Eve tayi mata wanka ta saka mata kayan ta masu kyau yarinyar sai ta fito tsaf da ita tubarkallah.
ZahraArkel ce!