DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:Northern_life_stories.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
3️⃣5️⃣
Sassafe suke da lecture don haka qarfe bakwai a school ta masa shi yama manta da zancen Abdulraheem yace zai dauke shi bai jima da zama ba ya fara karatu wayar sa ta fara qara.Ya zaro ta a aljihu yana kallon sunan daya bayyana a screen na wayar ya daga "Hey dude."
Daga daya bangaren Abdulraheem yace "Hey man nazo inata knocking whats up?"
Ya kalli kewayen da yake zaune kamar mai neman wani abu yace "Am already at school man,I totally forgot komai sorry."
Qaramin tsaki yayi kafin yace "Ok am on my way."
"Okay man,see ya."
A tare suka katse wayar kowa ya cigaba da abinda yake,Abdulraheem ya shiga motar sa ya tafi school din shi kuma ya cigaba da karatun sa jefi jefi yana kallon yanayin wajen da dalibai dake ta karakaina.
A haka Ria da Sighn suka tarar dashi suma suka soma tattaunawa akan karatun kafin daga bisani Abdulraheem ya same su shima ya shiga discussion din don dama yawancin lokaci indai a makaranta suke aikin su kenan in kaga sunyi wasu maganar to a wajen ta ne.
****
Karfe goma na safe Alh.Khamis da Mummyn su Mooha suka shiga Gogel don cewa tayi itama sai an sake komawa da ita.Gidan su Alh.Khamis suka soma zuwa suka gaishe da Innar sa kafin suka wuce gidan su Immileey.
Duk yaran nacan acan sukayi kari suna ta hira ko wanka Immileey batayi ba saidai anyi wa Baby Eve tana ta wasa a tsakanin iyayen ta abun gwanin sha'awa.
Suna shiga Immileey ta miqe da gudu ta taro Mummyn tana cewa "Yanzu daman nakeji a jikina kamar kina garin nan ashe kuwa hakane."
Abeey dinsu yace "Oh ita kadai jikin naki ya gayawa ta shigo kenan saboda son kai."
Dariya tayi tace "Aa Abeey harda kai."
Duk suka sa dariya kafin yayi magana Baffah dake fitowa daga duba rumbun sa yace "Aa fadi gaskiya dai daman ku iyayen ku kadai kuka sani ai."
Abeey yace yana zama kan kujera er tsuguno "Haka suke kam iyayen su mata kadai suka sani."
Aka sake yin dariya Goggo Lari ta shimfida qatuwar tabarma suka zauna gabadaya aka shiga gaggaisawa kafin hira ta balle kuma.
Immileey ta miqe tace "Bari naje na yi wanka daman ni kadai ce banyi ba."
Mooha cikin tsokana yace "Yarinya da kin qara minti biyar baki shiga ba saidai mu tafi baki wanka ba."
Dariya Baffa da Abeey suka sa suka miqe suka fice Abeey na cewa "Bari muje mu dawo yanzu."
Immileey ta zumburo baki alamun shagwaba yanda takewa Mummyn su,kafin tayi magana Mummyn ta riga ta "Rabu dashi babu mai sawa ki tafi baki wanka ba dole a jira ki."