DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:Northern_life_stories.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭
3️⃣6️⃣
Duk sai suka kafe shi da ido suna kallon sa tsahon lokaci kafin Abeey yace "Wannan abu d'an takara,sai ka bari yazo ya gwada sa'ar sa duk wanda ta zab'a a cikin ku shikenan sai ayi dashi."Yadikko tayi saurin cewa "Aa fa Alhaji baza a yi haka ba,ni daman sha'awar irin ce tasa nace a bashi d'in ba shine yace yana so ba kuma yana da matar sa daman don haka a bashi shi wannan d'in ai duk daya ne fatan mu duk inda yaran mu zasu je Allah ya basu nagari ya zaunar dasu lafiya."
Duk suka amsa da amin,Mummy tace "Amma da kin bari dai an gwabza din Yadikko don ni bana son ya same ta cikin sauqi zaifi daraja min yarinya ta idan yasha wahala."
Goggo Lari da sai yanzu tayi magana tunda aka fara zancen tace tana tab'e baki "Hmm er taki sai kace wata kayan gabas,mu aka ce za a wahalar damu basai mu nema masa wata ba er gaske abu da ga en matan nan yanzu ake sake haifo santala santala ma."
Mummy ta kama hab'a tace "Iyyeeee!au haka ma zakice?to shikenan a nema masa watan mu gani in ruwa zai zama sa'an kwando."
Duk suka sa dariya,Yadikko tace "Aa ni na nemawa yarona alfarma ayi haquri a bashi dai don Allah,ai sun dace naga Immileeyn tamu tubarkallah ta sake girma,a kira ta mu sake gaisawa."
Goggon tace ta kwala mata kira,ta fito da mayafi ta lullube kanta qato dashi ita da su Jannah,ta zo ta durqusa gaban su Goggon,ita kuma tace da ita "Yadikkon ku ce take kiran ki bani ba."
Ta miqe cike da jin kunya da nauyin ta taje ta durqusa a gabanta ta sake soma sabuwar gaisuwa da fillanci cike da kunya,itan ma da kunyar ta dinga amsa mata sannan tasa Dijangalan ta bata kayayyakin da suka zo da su tace "Gashi ba yawa kayan gona ne na kawo muku Allah yayi muku albarka kinji."
Ta jinjina kai tare da amsawa da "Amin."
Daga haka suka miqe suka yi musu sallama suka tafi,suma iyayen nasu sai suka miqe mazan suka yi waje Abeey yana cewa "Anayin sallah zamu tafi kowa ya tabbatar da ya had'a komai nasa."
Jannah tace "Mu komai namu a hade yake saidai Immileey."
Mummy tace "Jannah ki kiyayeni da takurawa Khadija fa,itan ma nasan kayan nata a had'e suke ko Khadija."
Dariya tayi tace "Eh Mummy."
Amnah tace "Allah bata qarasa had'a na Baby Eve ba,ko dazu saida Hammah Mooha ya ninke mata nakan igiya ya sa mata ajaka tace akwai ragowan panties."
Mummy tace "To sai ku tashi ku taya ta qarasawa kafin ya dawo kunsan dai baya jira."
Duk suka miqe suka yi d'akin Goggo Lari inda Immileey ke tattare ragowar kayan da bata hade suba tana sasu a jakar su,suka qarasa sukayo alwala sukayi sallah suka zubo abinci suna ci suna hira har su Abeey din suka dawo."
Suma abincin aka zuba musu shida Baffan Immileey suka ci suka qoshi sannan aka soma fita da kayan su,Baby Eve na hannun Mooha yana mata wasa sai ka rantse da Allah hankalin nasa akan yarinyar yake saidai kacokan yana kan Immileey duk wani motsinta akan idon sa tun bata lura ba harta gane irin kallon qurillar da yake mata ta soma takura,a haka suka gama shigar da kayan mota sukayi sallama dasu Goggo Lari suka tafi gida Innah Amina suka yi mata sallama itama suka dauki hanyar kano.
Mooha ke tuqin,Alhaji Khamis a gefen sa,Mummy da en matan ta a bayan,hira sosai ake a motar Immileey ce kad'ai bata saka baki saidai idan anyi abin dariya ta danyi murmushi kawai.
Ta bayan Mooha ta zauna don haka yana kallon ta ta madubi duk abinda take,Baby Eve ta rarrafa ta kwanta a kan cinyar ta da alamu bacci take son yi don har ta sa hannu a baki tayi saurin dan ture ta zuwa kan cinyar Jannah dake kusa da ita.
Ta ko canyare da kuka don taji dadin kwanciyar sosai,da sauri Alhaji Khamis yace "Lafiya? Meya same ta."
Kan suyi magana Mooha yace "Khadija ce ta tunkude ta ina kallon ta."
Baki ta bude tana zaro ido kamar bata yi ba,Mummy tace "Eyi ai ta burgeni don iyayi dukkan munan bamu isa tayi bacci a cinyar mu ba sai taje can."
Amnah tace "Kai Mummy uwa fa,ai zata so jin d'umin ta don ma ba'a barin ta taji dumin sosai."
Ita dai kawai dakai tayi tana jin yanda Baby Eve din ke tsallara kuka,wasa wasa kowa ya karb'e ta banda Mooha dake tuqi amma taqi yin shiru yau harda Amnan taqi lallasuwa a wajen ta.
Alhaji Khamis ya kalli Immileey dake ta kallon waje kamar bata san me ake acikin motar ba yace "Ke dauki yarinyar nan kada ta shide kinji,ni wannan kunyar taku bansan ina zata kaiku ba wannan ai daukan haqqi ne."
Kamar bata ji ba haka tayi saida Jannah ta dora mata ita a cinyar ta yarinyar ta kwanta ta saka hannu a baki tana ta cin zuciya amma qememe taqi tab'a ta sai kace an samata wuta a cinyar haka tayi baccin Allah ma yasa ta kwanta daidai da saidai tayi ciwon wuya qila bata kula ta ba.
Suna isowa gida tace da Jannah "Sis don Allah dauke min ita ai tayi bacci."
Jannah cikin tsokana tace "Idan bazaki dauke taba ki kwana a motar."
Abinka da me neman kuka aka jefe shi da kashin tumaki,kawai sai tayi qwal qwal da ido da daman maida ruwan su take tunda suka taho take son yin kukan sai ko ga hawaye shar shar.
Duk basu lura da abinda ya faru tsakanin ta Jannah ba sai kukan suka gani,Mummy tace "Ikon Allah wannan kukan me take kuma?me kika mata Jannah?"
Jannah da mamaki ya ishe ta tace "Wallahi Mummy ba abinda na mata cewa kawai tayi na dauke ta maka Baby Eve nace in baza ta dauke taba ta kwana a motan shine ta fara kuka."
Amnah tayi dariya tace "Tun safe ina lura da ita she's emotional daman kukan take son yi bari ni na dauke miki ita Baby na dai ba zata saki kuka ba."
Hannu biyu tasa tana goge hawayen amma sunqi tsayawa,Mummy ta ja hannun ta suka shiga ciki kai tsaye kuma bedroom d'in ta suka nufa a sama saida ta kullo qofar sannan ta zaunar da ita a bakin gadon ta itama ta zauna tana fuskantar ta tace "Khadija."
Immileey ta d'aga kai ta kalle ta a hankali ta amsa da "Na'am."
"Ki fada mini gaskiya idan har kin fison zaman Gogel wallahi ba takura goben nan sai a sa Muhammadu ya mayar dake."
Da sauri ta girgiza kanta idon nata na sake tara ruwa tace "Wallahi Mummy nafi son zaman nan,bansan meke damuna ba tunda satin nan ya fara bana jin dad'i ko yaya aka min abu sai nayi kuka dana kuka da ba na kuka ba kuma gabana yai ta faduwa inata jin ba dadi kamar wani abun ne zai faru dani."
Jinjina kai Mummyn tayi tace "Ba abinda zai faru dake da izinin Allah ki qoqarta ki ta zikirai kina hirji kina istigfari,komai zai koma miki normal kamar da kinji kinga school zaku koma cikin next week in kika saka damuwa a ranki taya zaki iya karatu?"
Ta jinjina kai itama cike da gamsuwa tana goge hawayen ta tace "In sha Allahu zan dage nagode Mummy."
Murmushi tayi mata sannan tace "Sannan ki daina yiwa Baby Eve abinda kike mata jan yaro a jiki na qara qauna da soyayya tsakanin sa da mahaifiyar sa ki daina korar ta kinji!?"
Tace "To." Cike da jin nauyi da kunyar Mummyn,kana ta miqe ta fice ta shige dakinsu ta kwanta kusa da Baby Eve inda Amnah ta kwantar da ita,itama Amnan na dayan gadon har ta kwanta tana shirin baccin.
ZahraArkel ce!