TAKAICINApart 1-20

22 0 0
                                    


Tsaye take tana kallon katuwar van da ta tsaya kusa da wata estate tana sauke dinbin jama'ar da ta debo maza da mata sai hayaniya da surutu suke tayi cike da nishadi..suna gama sauka suka canza surutansu da shewa zuwa wata magana cikin muryar waka Youths obey the clarion call
Let us lift our nation high
Under the sun or in the rain
With dedication and selflessness
Nigeria is ours, Nigeria we serve.jin wakar ya bata damar gane cewa yan bautar kasa ne aka kawo kauyensu kamar yanda aka saba kawo musu ko wacce shekara...tagumi ta rafka tana murmusa lokacin da idanunta suka sauka akan wani kyakkyawan saurayi daga cikin corp members din dogo ne fari ba rama a jikinsa,yana da manyan idanu me lemalema kamar hawaye ta kwanta a cikinsa Amman ba ita bace irin su ake cewa sexy eyes..yanada faffadar kirji a wata katsumba wacce tayi kyau a fuskarsa sai sheki takeyi da alama ta sha gyara sanye yake da farar Riga da bakar jeans trouser kafarsa sanye cikin farar foot wear idanunsa kulle cikin bakar glasses ya saka bakar face cap wacce aka rubuta NYSC da farar rubutu da alama shi yayi customizing din abinsa..ta yi nisa sosai a cikin tunanin da takeyi zungurinta taji anyi firgit ta dawo hayyacinta ta kai dubanta ga wacce ta zungureta tsaki ta dan ja haba mana dije wallahi kin bani tsoro wacce aka kira da dije tace ya bazaki tsorata ba?kin tsaya kin zabga uban tagumi akan hanya wai tsaya ma me kike tunani ne haka?kai ta dan sosa sannan ta kai duba ga inda van din tayi parking wayam ba kowa a wajen tsaki da dan ja tana zancen zuci lallai na sha'afa dayawa har mutanen wajen sun watse ban sani ba?kallon dije tayi tana kinga sai mun hadu a makaranta gobe yamma tayi sosai gashi ban ma je inda mama ta aikeni ba...hannu dije ta tafa tana tabe baki lallai ma amina allah dai ya shiryeki..amin amina tace tare da tafiya da sauri tabar dije na binta da kallo..
Yau ta kasance Monday ranan aiki wacce akeyiwa kirari da ko baturen ma tsoranta yake ji..kowa na hada hada zuwa inda yafi auki..dalibai na tafiya makaranta maaikata na zuwa wajen aiki haka yan kasuwa ma suna tafi wajen kasuwancin su..Amina ce ta fito daga daki sanye da kayan makaranta wadon ce doguwa dark blue sai Riga zuwa gwiwa light blue da hijab light blue zuwa daidai kirjinta kafarta sanye cikin lowfass ta Goya jakar makaranta a bayanta fuskarta fayau ba kwalliya Amman hakan ba shi ya hana kyaunta bayyana ba..
Wacece amina
Amina kyakkyawace ajin farko bata fiya tsayi sosaiba haka baza a kirata gajera ba,bata da rama kuma bata da kiba tana da cikar kirji daidai gwargwado ga kuma mazauna..irinsu ake cewa yan dumaduma..ba fara bace kuma bata fiya baki ba tana da hanci dogo har baka wanda ya zauna cas akan oval round shape face dinta,gashin idanunta zara-zara wanda sukayi wa manyan idanuwanta rumfa,bakinta dan karami lips dinta baki tana da mayalwacin suman kai sosai baki sidik.. Amina is a real definition of a brown skin girl...tana da yawan fara'a Amina ta hadu iya haduwa idan ka kalleta sau daya bazaka so kadaina ba.
'Yace tilo ga mairo da falalu wanda yan asalun nijar daga birnin agadez ne yan uwan juna ne dan auren zumunci aka musu ...fatauci ya fito dasu daga nijar suka ya da zango a cikin birnin kano ta dawo a karamar hukumar wudil...wudil ta zamo musu wajen alfahari dan malam falalu da mairosun ji dadin zama sosai a garin dan mutane ne masu son jama'a kuma sun iya zama da mutane cikin salama har basason a ce su ba yan asalin garin bane dan sun mance yaushe rabonsu da nijar sakomakon basu da kowa a garin iyayensu sun jima da rasu sakamakon wata mawuyancin yunwa da kishir ruwa da Allah ya jarabi garin nijar dashi Amman alhamdulillahi yanzu kam ba kamar da ba... Har iya yanzu yakan fita fatauci izuwa kauyukan kusa ya kan dan jima bai dawo ba duk dan ya Tara kudin da zai kai Amina makarantar gaba da secondary unibasity a cewarsa kaji tsoho ana university yana bata wa yan boko abinsu....Amina ta taso cikin gata sosai wajen iyayenta komai takeso daidai gwargwado tana samu,..yanda allah yayi wa amina kyau haka allah ya daura mata son mutane masu kyau balle ma ace farin mutum.. wayyo allah zaku daidaita da ita Amman idan tsabanin haka ne tabdi sai a slow...kawarta na hakika guda dayace wacce ake kira da dije dana da daidai gwargwado sannan farace sosai tare suka taso gwanin ban shaawa har akan kirasu da aminan asali,tare suka fara makaranta tun daga jss1 har izuwa yanzu da suke ss3.
Tana da natsuwa da kula da addininta bata shiga shirgin da ba nata ba,batada yawan fita dan bata da shirgin kawaye idan baka sameta a gida tare da mama ba to zaka sameta a islamiya, ta bawa ilimi mahimmanci sosai both Arabic and book,bata da lokacin kula samari a cewarta bata lokacine tunda bata fatan karatun ya tsaya a secondary level.
Mama!mama Amina ta tsaya kofar dakin mama tana kwala wa mama kira daga ciki mamar ta amsa tana haba Amina kira sai kace wata sabuwar makauniya baki shigowa ciki?labulen dakin ta dan daga ta rusuna daga bakin kofa mama antashi lfy?alhamdulillahi mama ta amsa dashi tare da murmusa tana cewa har an shirya kenan?eh mama na shirya...baba da yafito daga bandaki ya kara baki yana yan matan baba har kin shirya?ina fatan dai kin yi Karin kumollo?? Kai Amina ta kada alamar a'a baba idan na tsaya karya wa zan iya maka kasan yau Monday akwai assembly kuma nice headgirl.. Haba baba ya rike tare da cewa haka kullum kike cewa hannu ya saka a aljihu ya Ciro naira #200 ya Mika mata gashi kin siya abinci idan anyi break..karba tayi tana yawwa baba na gode ta mike sai na dawo tare suka hada baki suna cewa toh adawo lfy kuma a sa himma..
07/05/2020..Ramadan day 14
Gov't Girls college yayi makil da
Gov't Girls college yayi makil da dalibai..jeri2 according to class Amina ke saman stage tana leading din national anthem da morning prayers..principal ne ya karaso tare da wasu mutane biyar uku maxa biyu mata sanye cikin khakin nysc gaskiya sunyi matukar kyau tamkar daminsu a ka kirkiri nysc karankanta Amina bata bata lokaci ba wajen gano kyakkyawan gayen da ya tafi da imaninta ba jiya da yamman ..yau din ma shi ta kafewa idanu gyan mura principal yayi sannan ya gabarta da corp members din da aka turo makaranta... Kowannen su ya gabarta da sunansa da kuma subject da zai koyar..zazzakar huge voice amina ta zinkayo yana cewa Hi everyone my name is zaid tahir,am from Adamawa state,a graduate of Unilag. A Bsc holder of cell biology and genetics from the faculty of science...so I will be the one to handle Biology.. Nice to meet u gals..sunansa amina ta maimaita tana murmushi kamar wacce yau tafara jin sunan a rayuwarta..
Mathematics akeyi amman sam hankalinta baya wajen sai time table take ta dubawa tana dan jan tsaki tana bata rai ta kosa teacher din da yake koyarwa ya fita saboda next class din su biology ne,dije ta matso kusa da ita ta na mata magana kasa kasa yadai amina me ke damunki naga kinata cin magani?baki ta sake tabewa..taja tsaki out of anger bata san tsakin ya yi karaba teacher ya juyo yayi pointing dinta hey u stand up..da sanyin jiki ta mike...what was my last statement?shiru tayi tana wasa da dogayen yatsun hannunta..tsawa ya saka mata look up here da sauri ta kalla board din inda yake mata nuni ...can u come to the board and show us how we derived at the final answer??nan ma shiru tayi dan bata ma san me yake tayi ba tun da ya shigo cikin Bacin rai ya nuna mata hanyar waje get out of my class cikin sanyin jiki ta fita idanto ya kawo kwalla dan ta tsani embracement gashi sauran yan class sai dariya suke tayi..wata gindin bishiya da yake gaban staff room ta samu ta zauna..kai ta dukar tana tunanin abinda ya faru a class haushi ya sake cika mata zcy wai to tunanin me nake yi hakane har ban Masan abinda teacher din yake cewa ba take tambayar kanta..excuse me young lady da sauri ta daga ido izuwa inda taji sautin ya fito corp zaid ta gani yana mata alama da hannu da sauri ta mike ta isa kofar staffroom inda yake tsaye cikin rawar murya tace goodmorning sir,ba tare da ya amsa gaisuwan ba yace..why are u outside by this hour while u r not on break isn't lecture going in ur class?cikin rawar murya tace there is sir the teacher sent me out of his class due to some certain reasons sir,and pls don't me d reasons sir bcz I cnt actually say it...tun da tafara magana bakinta da face dinta yake kallo yanda take magana cikin natsuwa da idanunta sauke a kasa..hmmm really ?whats ur name and ur class ya tmbyta Amina falalu sciece class SS3A..oh dats nice u r one of my student kenan?yes sir ta fada a takaice ohk je ki kiramin class rep.dinku I guess I suppose to have ur class today,am the class representative and d head girl of the sch...ur class is immediately after the maths leactures...kai ya jinjina tabbas yarinyar ta burgeshi hannu ya Mika mata nice to meet you Amina falalu.
hannunta ta Sanka cikin nasa ta is my pleasure uncle zaid..Dadi fal ranta.
Like every other Monday it was hectic sai 2:pm suka tashi ko wacce daliba ta nufi hanyar gidansu...
Kullum labarin Amina baya wuce na uncle new biology teacher din su uncle zaid tun dije na biye mata har ta kosa..
Tafe suke daga islamiya suna fira mafi akasarin firan da Amina keyi zancen uncle zaid ne,kwafa dije tayi sannan tace Amina kenan anya kuwa ba wata a kasa kuwa?dubanta aminan tayi tace ban gane wata a kasa ba..?I mean anya kuwa bakya crushing akan uncle Abdul? Taba ta Amina tayi Allah ko?nima fa bansani..nadaisan i do fell something strange wen ever i thought of him..hmm oya tell me how u do feel about dije ta bukata..wani kayataccen murmushi Amina tayi tadanyi fari da idanunta tace duk lokacin da na Gandhi ko naji an ambaci sunansa ko nayi tunaninsa sai na ji zuciyata ta buga,bana iya yini batareda tunaninsa ba..wlhy dije idan naje sch bana son a tashi saboda ina rasa sukuni na rashin ganinsa har zuwa wata safiyar,hannun dije ta kama lokacin da suka kai kwanan gidansu ta daura a saman jirjin ta ki natsu kiji yanda zcyta ke bugawa da karfi wani Abu nakeji a game da uncle zaid wanda bazan iya yantance ko mainene ba.. Tausayin Amina ce ta mamayi zcyr dije ganin yanda tayi serious akan abinda take gaya mata nunfashi dije ta saukar tace Amina ki natsu ki dawo hnklinki kar ki bari tunanin uncle zaid ya rushed miki tattalin karatun ki da kk jima kina yi da dukkanin alamu infatuations(farfadiyar so) ne ke damunki a game da shi wanda insha Allah u will over come it with time..infatuations Amina ta maimata me hakan ke nufi?
Infantuation is an intense but short-lived passion or admiration for someone or something. ta bata amsa a takaice ,hmm amina ta sauke ajiyar zcy..tare da cewa kina nufin av fallen in love with uncle zaid kenan?kai dije ta kada alamar a a sannan tace love is different from infatuations.. Like how?amina ta katseta,amsa ta bata well Infatuation happens early on and tends to become obsessive. ... Lust and infatuation are usually fleeting and short-lived and don't tendto turn into love. When you are in love, you will have intense feelings for a guy, and be attracted and connected to him on the level of mind, body and soul.
Hmm amina tayi shiru tana kokarin auna maganar dije akan love n infatuation..kallon dije tayi tace zan shiga gida dije sai mun hadu a school gobe..da sallama ta shiga gida baba na alwala kasancewar magrib ta gabato dukawa tayi baba barka da war haka yawwa barka amina an dawo lfy kai ta kada ta mike ta shiga dakin mama jikin mama ta fada ta kwanta tana kumshe ido jikinta duk na kuzari fuskanta mama ta shafa lfy dai kinshigo daki ba sallama? Mama kaina ke dan yimin ciwo ta fada dan bata san mama ta Matsa mata da tmby,assha tashi kije dakinki na ajiye miki abinci ki ci kisha magani tashi tayi ta fita kan katifarta ta fada ta rumtse ido tana ta tunanin zancen da sukayi da dije tana son gane me zxyrta take ji gameda uncle zaid Tabbas tasan takan yi tunanin uncle zaid ta ko wani fanni tun ba ta wajen haduwarsa ba akwai lokacin da tayi mafarkin sa wai taje staffroom domin kiransa lokacin koyarwarsa yayi ta sameshi shi kadai zaune yana yin research akan darasin da zai koyar musu sanye yake cikin body hug me v-neck da jeans trouser,ana hango tsumar kirjinsa wanda ya kwanta luf a samar farar fatarsa a gaban rigar an rubuta i don need girls i need swaggs yy masifar kyau har ta kasa dauke idanunta a kan kirjin nasa hello yace mata amman bata ma san yanayi ba dan tayi nisa sosai a cikin tunanin marasa misaltuwa da takeyi mikewa yy ya isa dab da ita bata Sani ba kamata yy ya bada da kirshin nasa ya rike ta gam sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta shiga kokarin kwacewa kara kwantar da ita yayi ya buggguga bayanta tareda hura mata iska mai sanyi a kunne daidai nan mama ta shigo ta tashe ta wannan mafarkin ya tsaya mata a rai she's not use to all that sort of life but tana fatan how she wish her dream will come true..ajiyar zcy ta sauke tana cewa a ranta whether is infatuation or love she dont care itadai she wants to b close to him kila ta sami saukin abinda takeji game dashi ta mike ta fita domin ta daura alwala tayi sallah.
Kamar kullum da begen zuwa ganin uncle zaid ta tashi daman shine first darasin su na yau saboda haka bata dauki lokaciba wajen shiryawa a gurguje ta fita gida zuwa sch,tana shiga harabar sch din tayi arba dasu,shi da friends dinsa shigar kaftan suka yi both muslims and Christian sbd yakasance jumaat babbar rana,yafi ko wa yi mata kyaua, shadda yasa coffee colour wanda ta saje da skin dinsa ya sanya hula wacce ta dace da kayan,yayi kyau matuka wanda hakan ya kara Sosa mata abinda ke kwance a zcyrta game dashi..da sauri ta isa inda suke tana fara'a Gm sir,kallonta sukayi dukka suka amsa a tare jakar hannunsa ta amsa tana sir biology is our first class this ta nuna jakar hannunsa bari in wuce maka dashi,jakar ta amsa ta wuce zuwa class dinsu
Jingina jikinsa yayi a kofar shiga staffroom din Yana murmushi Wanda Shi kansa baisan meye dalilin yin Saba..sabir ne ya dafa sa (a friend nd Corp member)man please be urself Naga alamar kanason ka Faller dayawa mtsss tsaki Zaid yayi hade da Bata Rai fall in love under my foot Kaima kasan I didn't believe in love..love don't exist just catch fun and get ur way that's my believe...ya na Kai Nan ya juya tare da nufar hanyar class sabir Kam Kai ya girgiza Yana cewa Allah dai ya kyauta.
ZAID TAHIR NAIRA
Flashback◀️
Zaid ya kasance Da tal ga Alj. TAHIR naira Wanda ya shahara wajen kasuwanci,Yana daya daga cikin attajirai masu fada a ji a jahar adamawa yayi kaurin suna wajen kirki da taimakon alumma...
alhj.Tahir naira mutum me kamili Wanda bayason hayaniya matarsa guda daya ce haj.fatime Yar jihar maiduguri gogaggiyace sosai wacce da ka ganta kasan Boko ya ratsata Amman hakan baisa ta yin fiffiko ba..kwararriyar likitace wacce ta karbi lambobin yabo sosai a gurare dayawa tayi suna sosai wajen attajirai da talakawa tana da riko da addini..dansu daya Wanda sun Jima sosai kafin Allah ya Basu Shi,Wanda ya ci suna Muhammad zaid.tayi tayi akan mijinta ya Kara aure ko ya.kara samun 'ya'ya Amman Sam yaki a cewarsa ita kadai ta ishesa duniya da lahira ko da kuwa Bata haihuwa balle Kuma har ta Haifa Masa sanyin idaniyarsa..Zaid ya taso cikin so da kula da Kuma tarbiya Basu Bari ya sangarce ba..sun bashi ilimin addini daidai gwargwadon iyawarsu.
Mahaifinsa Bai fiya Zama ba saboda yanayin kasuwancinsa yakan zagaye kasashe da dama kafin ya dawo najeriya...haka Nan gajiya fatime kunsan dai yanda aikin asibiti yake balle ga kwararriya wacce tayi suna sosai ...itama hidima sun mata yawa ga yawan zuwa conferences..nasan masu karatu suna son jin wani kasuwanci yake Yi,well kasuwanci da dama Dan ya mallaki companies da dayawa irinsu
Tahir Mai naira enterprises,Tahir oil and Gas,Tahir Mai nera textiles and more,Tahir shopping mall,Alhj Tahir Mai nera teaching hospital, and lots more.
Sistern baba Zaid Haj larai wacce ta kasance Yar siyasa ita ke Zama a gida tare da Zaid a duk lokacin da iyayensa basa nan...tun da aurenta ya mutu ta kiyin auren a cewarta aure Babu abinda ya Tara sai bakin ciki da takura yayanta alh tahir yayi ta sake wani auren Amman Sam Taki tace sai ta huta Ido ya samata...tana da ya guda Maryam wacce take Kira da fanna wacce da aurenta ya mutu tace sam bazata barta a wajen ubanta ba Kar ya sake wani aure a musguna wa yarta haka baban fanna ya hakura ya barmata Yar.
wani abu da Basu sani ba shine Haj larai mace ce Mara kula da rashin kamun kai tana da yawan son more rayuwa..duk lokacin da iyayen Zaid basa gari itama Bata Zama ta kula da shiga da fitarsa Kamar yanda iyayensa suka bar mata amanarsa..Zaid ya kasance Mai son hutawa da yawan socialization tun Yana secondary school..Daman iyayen sa me takura Masa dazarar kuwa sun bar gari Shima yake fara fantama club,hotels da Yan mata da house parties...idan iyayensa suna gari kuwa ba abinda yake fitar dashi waje idan ba school ko islamiya ba ..idan kuwa Ranan ba school ko islamiya to Yana gaban system Yana nazarin karatunsa.. Allah sarki bayin Allah kullum suna cikin Shi Masa albarka saboda yanda yake bawa ilminsa dukka biyu muhimmanci ...ko kafin Zaid ya Gama secondary School yayi Nisa a harkar Mata... Gashi kyakkyawa ajin farko hutu ya ratsashi ..da flaying colour ya Gama o level dinsa yazana jamb karan farkon yy hitting din target point dinsa..ya Sami gurbi a unilag.
Ya kasance daya daga cikin hottest guys din unilag gaba daya Mata kuwa zuka zuka sai Wanda ya zaba,har Yan 400lvl idan ya gadama daukansu yake. Sai dai Zaid akwai ilimi duk shekiyancinsa baya wasa dakaratunsa,addininsa,da Kuma ibadunsa..Zaid ya kasance Kamar Mai jazz..duk ustazancin yarinya yasan yanda zai bi da ita har ta bada Kai..
Zaid had a believe din love don't exist he never believe in so called love...all he knows is lust...
Zaid ne yayi focussing a kan wata kyakkyawar face da ke kan screen din wayarsa a Instagram ya ga pic din. sanye take cikin hijabi daga sama har kasa kafarta rufe cikin safa haka hannunta ta sa likaf Amman ta daga sa zuwa sama ta bar face dinta fara ce me kyakkyawar murmushi yayi Nisa cikin kallon pic din sabir ya zungure Yana cewa kwalelenka dai da wannan halittar da sauri Zaid ya kallesa Yana guy kasanta ne?dariya sabir yayi ehman baka santa ba?ya tmby Zaid tare da cewa ai department dinmu daya siyama sunanta shes d most decent among all d ladies in the sch..Baki Zaid ya tabe tare da cewa tana da kyau gsky Amman she's not my type..sabir yace ko ma dai type dinka ce baza ka sameta ba sbd Bata ba kowa take kulawa ba a Mata Yan uwanta balle ma Kai da kayi kaurin suna..Kai intakaita ma Bata ma magana da maza tsaki Zaid yy tare da cewa shirme dai ya mike ya shiga bithroom.. yayi hakane domin yanason yayi nazari da brain dinshi how come this fine beb tana dept dinsu Amman Bai taba sanin her existence ba har sun Kai 300lvl?wanka yayi ya fito tare da dauro alwala..
Jumaat babban Rana ya Sha ado cikin kaftan sai kamshi yake fitarwa.Yana tuki cikin katsaita ya nufo ta hanyar thiethre fakawa yayi ya fito ya iso zuwa ga wasu Yan mata sallama ya musu cikin faraa suka amsa suna Allah Allah ya kyasa su.dan Zaid ya iyawa yanmata barin kudi..wayarsa ya Ciro hotan siyama ya nuna musu Dan Allah ko kun San inda zan ga siyama?face suka Bata dakyar suka Masa nuni da wasu squad din Yan Mata su hudu.. wayanda suke sanye da hijab kala daya har kasa fukansu a bude saboda sun daga likab din zuwa saman kansu..wajensu ya nufa da sallama cikin muryarsa Mai taushi a tare suka hada Baki suka amsa..gyaran murya yayi sannan yace Dan Allah idan bazaku damu ba inason ku bani aron Yar uwarku siyama..daya daga ciki ta amsa da bazamu iya Baka Aron ko daya daga cikinmu ba duk abinda zaka fada ka fadeshi Anan...siyama Kam haushi ne ya kamata sbd ta Jima tana crushing akan Zaid ita duk dabi'unsa Bata ganin aibunsu...daya tace Dan Allah mallam if u won't mind excuse us pls ta fada tareda nuna Masa hanyar da ya bi yazo...ran Zaid idan yayi dubu ya baci ba a taba Masa irin kalar wulakancin ba face din siyama ya duba wacce ta sadda kanta kasa Allah kadai yasan me yake Kai kawo a cikin zuciyarta gyaran murya yayi sannan yace well Daman na nemi izini a wajenku ne domin Ina tunanin kuna da Kamala Amman kun Nuna min akasin haka gyara tsayiwa yy ya Kai dubansa ga siyama yace malama siyama if u won't mind can u give me a spot out of ur busy schedule?shiru tayi ta rasa abinyi har ga Allah tana son taje taji uzurinsa but tana jin yanda zata bada squad dinta...Kamar ko sun San tunaninta Ido suka kafeta dashi Bata dago kanta ba balle tasan me dukkansu suke ciki wayarta kirar nokia take ta jujjuyawa ..yanayinta kadai ya ganar dashi abinda ke up nd down a zcyrta..batayi aune ba sai ji take ya fisge wayar da ke hannunta numbansa yasa a ciki tareda dialling karawa yayi a kunnensa sannan ya Ciro yana duban screen din tsaki yayi tareda jefa Mata phone din Yana cewa ashe ma ba card a ciki anyway my digit is in there inkinsa card pls give me a call ajiye Mata wayar yy ya juya ya tafi ba tareda ya dubesu ba Nan suka hau kan siyama da surutu daya daga ciki ta dauki wayar tayi deleting din numbern dayasa a phone din nata...
10:00pm siyama ce kwance ta kasa bacci sai juyi take tana tunanin Zaid wayarta ta ga Yana blinking alamar Kira dayake phone din na silent shiru tayi tana kallon numbers din da ke dancing akan screen din amsawa tayi ta Kara a kunnensa zazzakar murya taji ance assalamualaikum malama siyama gabanta ne ya buga da karfi jin muryan Zaid da sauri ta Kai dubanta ga friends dinta da suke sharan bacci a hankali ta tashi ta shige bathroom bakinta na rawa tace how comes u get my digits? murmushi yy calm down malama u know don't act cool..kinsan phone dinki akwai card and definitely I got ur digit time din da nayi dialling well nasan is late already a wajenku malamai..so I won't disturb bcz I don't want to cause misunderstanding tsakaninku da friends dinki but pls do me a favour meet me tomorrow at new extension by 00:00noon...Bai jira ta amsa ba ya kashe bin phone din tayi da kallo tareda yin murmushi...daki ta koma tankwanta.
Immediately after there lectures ta shiga duba time tana tunanin yanda zata Samu excuse ta bar friends dinta Amman ta rasa abinka da rashin sabo haka take ta binsu zugwi2 zasu wuce gida napep suka tsare zasu shiga Kai siyama ta dafe tace wash nabar joting book dina a class saukowa zasuyi tace no basai mun koma dukkanmu kutafi kawai will join u soon at home.. karmu batawa me napep time..haka kuwa akayi suka tafi..
As scheduled Yana zaune Yana pressing phone tayi Mai sallama juyowa yy ya amsa tare da cewa sweetheart kinyi late maimaita kalmar tayi a ranta murmushi yayi tare da cewa oh sorry na zake dayawa ko?nuni ya Mata da waje Yana pls have a seat Kai ta girgiza alamar a a am in a hurry so pls save my time..ohk then yace siyama I love you Ido ta bude tana kallonshi yes I mean it am sorry I didn't say it in a romantic way it's bcz u said I should save ur time..shiru tayi ta kasa cewa komai sunanta ya Kira yace siyama nasan kina Sona kawai dai kina jin tsoran friends dinki ne masu over reacting Kamar wasu parents dinki...yake tayi tace Zaid I will get going ohk then I really appreciate ur coming down here take care of urself I love you.
Soyayya Mai karfi ya kullu a tsakanin Zaid da siyama Mafi yawan soyayyan a Watap akeyin Shi sai dai Kuma Dan sneaking da takeyi su hadu a bayan idon friends dinta..Zaid ya share 1week baya zuwa sch,baya Hawa online no means of connecting to him siyama ta shiga damuwa sosai hakan yasa ta faki idon Yan kawayenta ta je wajen abokinsa sabir mamaki matuka ya kama sabir so dama da siyama yake flirting kwanakin ga...kawar da mamakinsa yayi tare da gaya Mata Zaid baya jin dadi malaria yake har ya kwanta a asibiti..taji ba dadi gsky Bata Bata lokaci ba wajen karban address dinsa..Bata tsaya sauran lectures ba ta fice daga sch sai apartment din Zaid Bata Sha wahala ba ta Isa inda yake lodging flat ne har da Mai Fadi ikon Allah tace a ranta kudi na inda suke motacinsa sun Kai uku a fake a harabar gidan doorbell ta Danna Zaid da ke kwance a favour sanye da short and singlet yana kallo ya taso ya Isa ga kofar yaji mamaki matuka na ganinta it's kuwa kunya ce ta kamata ta juya da sauri hannunta ya riko ya jawota zuwa cikin sannan ya rungumeta Yana marairaicewa Yana gaya Mata yanda yaji kewar ganin face dinta...
To cut d story short Saida Zaid ya Sami nasarar cire duk wata kunyar da siyama take dashi..ya maida ita party type tun tana boye new halinta da ta canza har friends dinta suka gane fada sosai sukayi hakan yasa ta kwashe kayanta ta bar gidan da suke zuwa apartment din Zaid..couple life suke living da siyama...har sai da aka sandasu a sch din siyama ta Zama hottest gal aure ne kawai ya rage basuyi ba da Zaid...Zaid promise her heaven and Earth..wannan shine takaitattcen tarihin Zaid.
Continuation

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 23, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TAKAICINAWhere stories live. Discover now