page 6

60 3 0
                                    

*KUNCIN RAYUWA*
        _Kukan Yah'mace_😢



*Sainah✍*

*DEDICATED TO BILLY S FARI*



*Page six*
  Tunda daga wannan lokacin nakoma makaranta abina,  sai dai abinda gidanmu ba'a saniba shine, "Nayi wani saurayi mai suna kamal inda yazo bautar k'asa ne agarinmu, " Dalilin had'uwata dashi kuwa *K'AWATA CE SILA*

   Koda nadah tazo nan saita fashe da kuka mai tsanani tace, " Azrah nayi Nadama wallahi, domin shine silar lalacewar rayuwatah,Shine mafarin bud'emin wannan masifa danake ciki  tana mai share hawayen tace,,".....

     Wata rana CE ina zaune ina duba wani littafi da malamin mu yace zai mana text gobe ina cikin karantawa ne naji muryar k'awata LAYYAH tana cewa

  Assalamu Alaikum,""

Na'am samata da wa'alai kumussalam my best k'awa in d world tare da sakar mata murmushi Dan nasan jiya bak'aramin b'ata mata rai naiba

Harara ta wurgamin gami da jan tsoki mtsss tace,

"dilla ni ba wurinki nazo ba ,naxo wurin hajiyar mune,

baki na tab'e gamida da Jan tsiki Nace," matsalarki

Zama tai kusa dani tana cewa ai wallahi ke k'awata banza ce ,,harni zaki watsa ma k'asa a'ido kiman rashin mutunci dan nakawo maki mashin-shini

Tsaki naja nace, "kinga layya kifita idona inrufe dama  cemaki ai banda mashin-shinin ne zaki jajubomani mutumin da bama anan garin yake ba kicewai yace yanaso na ,Ni wallahi baiman ba kuma mani nan da kike gani karatu ne agabana dan saina zama likita da ikon Allah gamida washe baki koda naxo nan. Dan arayuwata ina mutuwar San inganni cikin fararen kaya

  Dariya layya ta fashe da ita tace, " lallai hajiya likita kina k'alular {rashin zuwa makaranta} zaki kira kanki da likita,,hmmm layya kenan da kika sani banda yanxu danni nan dakike ganin nakoma makaranta kuma ma yanxu haka da kika ganni karatun text nikeyi Dan gobe malamin mu zaimana ita,
   Baki layya tarik'e tace,"Ah da gaske kike nima ko zanwa babanmu magana ya maidani makarantar ku kinga sai mudinga karatun tare ke kizama malamar Asibiti ni kuma nazama lauya ko" Dariya dukan muka  fashe da'ita tare da tab'awa daga nan muka dinga fira yanda zamu dinga gudanar da aikinmu idan muka zama likita da kuma lauya,

    Wai k'awata miyasa kink'i ki kula kamal ne?naganshi kyakkyawane gashi fari kuma da alamu zaiyi kirki kidaure kikulashi kinga k'ilama daganan inyaga kina kulashi ya dinga koya mana karatu ko..nidai sororo nai ina kallonta yanda ta hak'ikance take yabon mutumin da batasan daga inda ya fito ba k'arshe dai nace ke nifa layya kin isan da surutu akan wannan mutumin kije ke kuyi soyayyar dashi mana mtss gamida tashi nashige d'aki..tsaki itama taja tatashi ta wuce gidansu
  Ashe duk abun nan da muke Hajiya kaka najinmu inashiga d'aki ta fara magana kamar haka..Habawa takwarata yanxu bak'in cikin ganin mijinki ki kemun ko sokike in mutu ban aurar dake ba kiyi hak'uri ki kula kalamun danaji ana maki magana akanshi ,"Mizanyi Niko inba dariya ba jin tace kalamunn.habawa hajiyatah kamal inajin yake fa .kuma da ki kecewa in kulashi bafa nan garin yakeba yazo wannan abun ne waishi bautar k'asa nefa.nidai Hajiya gaskiya bazan kulashi ba.qarshe dai da kalamai masu tausasawa tasani nafarajin zan kula kamal kamar yadda naji layya tafad'i sunan
  Bayan kwana biyu ko layya tacemun inshirya yau kamal yace zaizo gidanmu na amsa mata da to
    Ina zaune naci kwalliyata nayi kyau inajiran xuwan kamal.Sallamar yaro ce takatseni da tunanin Dana lula.wai ance ana kiran nada ,kafin in bashi amsa Hajiya kaka ta ansamai da kaje kace gata nan zuwa

  Harara na wurga mata dan ni azahirin gaskiya tafara takurani daga zuwa kirana babu ko d'an jan ajinnan danaji anayi zata wanice ganinan zuwa.
    hijabina na zara nayi zauren gidan mu cike da tsoro Dan abunne nakejin wani bambaraqwai wai nada da zance...
 

          _*Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata cikin sauk'i da rahusa zai turo katin Mtn na naira d'ari d'aya (100) ta wannan number d'in 08167453086, idan yaturo sai yayi screenshot ya tura shaidar biya ga no d'in da ya tura katin*_

#Vote
#Share
#Comment
#IWA
















*Mamyn Khairat*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 03, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KUNCIN RAYUWAHWhere stories live. Discover now