PART 1

58 2 1
                                    

2nd, June, 2020AD          10/10/1441AH

       𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊

SARKI GOMA
                     ZAMANI GOMA

             RUBUTAWA
                BASIRA SABO NADABO
        SALAHUDDEEN MUHAMMAD

               SADAUKARWA
                HANNAT MAHMOUD

    GABATARWA
Da Sunan Allah Mai Rahama Da Jinƙai, Tsira Da Aminci Su Ƙara Tabbata Ga Manzon Tsira Annabi Muhammad (S.A.W).

  SHIMFIƊA
     Ƴan matan Hausawa, sun kasance kyawawa da kuma tarbiyya. Al'ummar Hausa dai, al'umma ce da ke zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar.

     Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka da ƙasashen Larabawa kuma a al'adance masu matuƙar hazaƙa, aƙalla akwai sama da mutane miliyan hamsin waɗanda harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A tarihi kaɓilar Hausawa na tattare a salasalar birane. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma Fulani.

     A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda ƙabilar Hausa ke yunƙurin kawar da mulkin Aringizo na Fulani, sai Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa ƙarkashen mulkin Birtaniya, ƴan mulkin mallaka sai suka marawa Fulani baya na ci gaba da manufofin Aringizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne ya yi kane-kane a arewacin Najeriya.

     Kodayake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da zuwan Addinin Musulunci da kuma ƙarɓarsa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bamban.

     Ginshiƙoƙin al'adun Hausawa na da mutukar jarumta, ƙwarewa da sanayya fiye da sauran al'ummar da ke kewayenta.

Zazzau Ƙasa ce wacce a kasani mai daɗewa da tarihi a ƙasar Hausawa.

     Sana'ar noma ita ce babbar sana'ar Hausawa, sabo da ingancin noma; Hausawa ke wa sana'ar noma kirari da cewa, "Na duƙe tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar." Akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saƙa da kira, fannonin da ke mutuƙar samun ci gaba a harkokin sana'o'in Hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana.

     Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanayyar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman Larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cuɗeni-in cuɗeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa bane a nahiyar Afirka.

     Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacin Afirka da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima su na bi a hanyar ta zuwa aikin Hajji.
______________________________________

        SHAFIN FARKO
     Gudu suke yi ba ji ba gani, ba su gushe su na wannan gudu ba har sai da suka shiga cikin jeji suka yi nisa. Ba su samu natsuwa da kwanciyar hankali ba har sai da suka je wani wuri mai yawan duhuwa da dogayen bishiyoyi, a nan suka tsinki ganyen bishiya suka ɗaɗɗaura a jikinsu gaba ɗaya, sannan suka haye kan doguwar bishiyar da su ka tsinki ganyenta suka kwanta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 03, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SARKI GOMA ZAMANI GOMA.Where stories live. Discover now