Part 38

283 26 3
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:Northern_life_stories.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭


3️⃣8️⃣
Bacci sosai sukayi don har saida aka kira magriba Mummy taga ba wanda ya fito taje ta tashe su.

Shikam Mooha sai wajen tara na dare tashi a gigice yaje yayi alwala yayi sallar magriba da isha'i kafin ya shigo cikin gidan.

Duk suna falo ya bisu da kallo,Immileey na ta bawa Baby Eve abinci don qiwar ce ta tashi taqi yarda da kowa amma tana ganin Mooha ta fara tsalle tana d'aga masa hannu tare da gwaranci.

D'aukan ta yayi ya d'aga sama yana juyawa tana ta qyalqyala dariya shi kuma yana ta ihun "My Baby,My princess,My Queen."

Saida sukayi wasa sosai sannan ya mayar da ita ta cigaba da cin abincin da Immileeyn ta gama quluwa akan sa don ta tsani cin abinci ana tashi.

Ya zauna yana kallon Mummyn yace "Kuka barni Mummy inata sharar bacci sai yanzu nayi magrib da isha?"

Mummyn ta zaro ido tana cewa "Allah?wallahi nayi tsammanin fa bama ka gidan sam banyi tunanin baccin kaima ka kwanta ba,suma wad'annan sai magribar naje na taso su ai,shiyasa wannan kirikun gata nan idon ta qir ta hana uwarta sakat kai kad'ai ta yarda dakai saboda wariyar launin fata."

Amnah tace "Nima yau da take yarda dani qememe taqi ta taho wajena sai Mamanta."

Dariya yayi yana d'aga ta don sake rarrafowa tayi ta dawo wajen sa ganin ya zauna,ita kuma Immileeyn ta miqe a fusace tana cewa "Allah saidai ya baki nina gaji da wannan wasan ke baki ciba baki barni nayi abinda ya kamata ba."

Hararar wasa ya balla mata kafin yace "Eh bani ance miki ke kad'ai ce mai hannu?kuma meye abinda zakiyi da yafi Princess d'ina?"

Bata kula shi ba ta dangwarar masa da kwanon ta tafi kitchen abinta.

D'aga murya yayi yace ta taho masa da abincin shima zaici sannan ya sauka qasan carpet ya cigaba da bawa Baby Eve din suna ta wasan su.

Mummy tace "Abin fa da take so kenan ita kuma Khadija baza ta iya ba."

Mooha yace "Shiyasa ai abincin ma in ita ta bata bata qoshi."

Daidai sanda ta ajiye masa abincin sa,suka had'a ido tayi saurin kawai da kanta ta koma ta zauna ta d'auki littafin ta na makaranta tana dubawa don monday zasu koma makaranta.

Ya sake kallon ta yana mamakin yanda tayi wani kicin kicin da ita,don haka yace "Mummy wai meya samu d'iyar taki ne haka ko duk missing su Goggon ne har yanzu take fushi?"

Mummy ta kalle ta ta maida idon ta kan Moohan tace "Mhmm ba wani missing gida,qila yanayin ta ne ya dan chanza."

Ya jinjina kai yace "Toh Allah ya kyauta."

Ta amsa da "Amin."

Moohan yace "Wai ya Bro kuwa ni tunda ya tafi bamuyi magana ba."

Immileey ta d'ago tana kallon sa don daya ambaci bro din saida gabanta ya fad'i.

Mummy kuwa cewa tayi "Yana can lafiya yace min tuni sun fara lectures ma,har abokai yayi harda wani d'an nigeria."

Amnah tace "Yawwa Mummy don Allah ki kira min shi video call nayi missing My Jaan."

Jannah ta tab'e baki tana maimaita abinda ta fada.

Amnah tayi dariya tace "Oho dai naji."

Mummy tace "Wallahi Firdausi kinji kunya,gashi nan ita ta dauki girman ta bar miki qanqantar."

Jannah ta turo baki tana cewa "Kai Mummy."

Mooha yayi dariya yace "Ba a taba haka ba ai dole dai babba babba ne ba yanda za ayi."

"Da yanda za ayi mana,sai babban ai ya zama na kwabo sai girman jiki dana shekaru bana hali." Mummy ta fad'a tana daukan wayar ta ta soma kiran Lameen.

Yana lecture kiran ya shigo don haka yayi excusing kansa ya fita ya d'auka yana murmushin nan nasa yace "Mummy na."

Murmushin ita ma tayi tace "Na'am ya kake?"

Ya amsa da "Lafiya lau,yanzu ma lecture muke yi na d'anyi excusing kaina ne na fito kiyi haquri anjima zan kira ki idan na fito na nutsu."

Ta jinjina kai tace "To Allah ya bada sa'a sai anjiman."

Suka katse tace tana ajiye wayar tata "Kinji da kunnen ki lecture sukeyi inya gama ya kira."

Tace "Toh ba damuwa sai gobe mayi waya ai."

Daga haka suka cigaba da hira,har wajen sha daya suna zaune a falon kowa da abinda yake Mooha da Mummy ne dai suke ta hira har aka gangaro kan komawar su makaranta.

Mooha yace "Nifa tunani nake anya Immileey baza ayi mata promotional exam in taci kawai ta tafi Ss2?"

Mummy tace "Meyasa?"

Ya d'an sosa kansa yana kallon ta ta gefen ido yace "Saboda gara ace ta gama da wuri ta tafi university don so nake kamar tana year 2 haka sai ayi."

Mummy ta qunshe dariyar ta don taga yanda yake ta wani soshe soshe na jin kunya tace cikin son tsokanar sa "Sai ayi me?"

Dariya yayi don yasan ta gane sarai so take tayi teasing d'insa yace "Wannan d'in."

Dariya tayi sosai kan tace "To ke Immileey wai kin ma amince da tayin nasa naga yana d'ebar muku shekarar da zakuyi wannan d'in ta bakin nasa?"

Wata matsananciyar kunya ce ta kamata kamar ta nutse a wajen ta kifa littafi a fuskar ta,kafin ta miqe da gudu ta haura sama.

Dariya suka saka gabadaya Jannah tace "Immileey sarkin kunya,Mummy baki ga abinda ta dinga yi bafa da mukaje gidansu Turajo."

Amnah tace "Ai nima nayi mamaki yanzun fa ba surukan ta bane amma abinci ma ta kasa ci."

Dariya Mummyn tayi tace "To ai zamanin nan ma kunya irin ta fulani ta ragu, da fa da hatta qawar surukar ka baka iya kallon ta ko kuyi magana da ita saboda kunya?kai ko muryar su kaji baza ka zauna a waje ba balle surukar ce da kanta tapdi jan ai bakwa hada hanya sai dole."

Jannah tace "Tap aiko yanzu to ba ayi tunda gashi nan har gidan su mukaje."



ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now