_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
2⃣8⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
_*Ma chérie salima je t'aime au fond de mon coeur 💝, je te salue gratuitement 👌🏻, pluie de bonheur à toi trésor chérie 🌹🌹🌹, merci beaucoup pour ton encouragement c'est le pourquoi je te donne cette page gratuitement , faut faire tout ce que tu veux avec, si tu ne veux faut refuser a tout les fans de lire ça mais pas avec une seule personne qui est ma petite soeur cherie maryam ( official marcy) 💞💞💞*_
A bangaren Hafsat kuwa tinda Habib ya fita take zaune , kishi ya tokare mata wuya , kamar ta fasa ihu haka take ji a ran ta , ko kallon ledar kazar da ya aje batayi ba , ta jawo twins ta rungume a jikin ta hawaye masu zafi ne suke fita a idanuwan ta, batasan lokacin da bacci barawo ya saceta ba,
Ba ita ta farka ba saida Habib yazo yana tashin ta daga bacci, da kyar ta bude idon ta cos kan ta mugun ciwon yakeyi mata saboda baccin da bata samu ba a jiya , bayan yaga ta tashi yace da ita da ta tashi tayi sallah har safiya ta fara wayewa , bata kalle shi ba ta tashi ta shiga toilet tayi bruch da alwala sannan ta tada sallah, shi kuma sai ya koma wajen yar babyn shi Samira, yana zuwa dakin sai naga ya haye saman gadon ya jayo ta jikin shi, bai jima ba shima sai bacci ya kashe shi saboda jiya bai samu isashen bacci ba kasancewar ya kashe arna 70.,( Habib ba daga kafa) ko dayake sunna ce yayi saboda ana a raya sunna ranar da amaria ta tare, ita ko baiwar Allah sai bacci wahala takeyi batasan ma yazo ba , bacci suke abin su sai karfe 9 na safe ta farka, tana bude idon ta sai ta ganta a kirjin Habib, shima motsinta ne ya tada shi a lokacin, yana bude idon shi sai tayi sauri ta rufe idonta tana matsawa daga jikin shi , shi kuwa sai yace ,
"wa na kama tana kallo na"
Batace komi basai murmushi da tayi tana rufe fuskarta,
Habib yace
" baby wannan kunyar na kusa cireta , yanzu dai " bari in tafi inyi wanka" sannan ya tashi yayi dakin shi dake bangaren ta ( gaskiya Habib d'an gata ne ko ina da dakin shi, ) , da to kawai ta amsa sannan itama ta tashi tayi toilet , brush ta farayi, sai ta kara gyara jikin ta , ta kara shiga cikin ruwan dumi taji dadi sosai sannan tayi wanka, bayan ta fito daga wanka , ta goge jikin ta sannan ta shafa mai , podew da kwalli kawai ta shafa , sannan ta shafa humrar ta mai dadi, sannan ta sanya wasu riga da zani na atanfa dinki yayi mata tsaf yabi jikin ta , ta daura dan kwalin ta, ta sanya yan kunne kalar kayan ta, tana tsaka da fesa turare Habib ya shigo dakin da sallama a bakin shi, ai kamar ta tsaga kasa ta shige haka takeji saboda batada hijabi kuma ga riga komi ya fito, 🙈 dayake dinkin ya kamata , da kyar ta amsa mashi sallama, Shi kuwa habib yana shigowa bai tsaya ko ina ba sai bayan ta , ya rungumota ta bayan shi yana cewa
"waooo joli fille( beautiful girl )"
Ita kuma jinshi a bayan ta sai ya saukar mata da wani yanayi, tana jin wani abu na tsirkar mata zuciya a game da Habib ,
Juyowa yayi da ita suna fuskantar juna yana cewa
"baby taho muyi breakfast"
Da to ta amsa sannan ta dauki hijabin da ta fiddo zata sanya ya hana ta yace haka yake son ganin ta , babu yadda zatayi haka ta hakura amma duk a takure take kasancewar bata saba zama ba hijabi ba ,
Bayan sun fito palour suka tardo abinci saman table , Hafsat ce ta girka masu break bayan ta gama anyi sa'a Habib ya leka can lokacin da ya gama wanka , sai ta bashi ya biyo masu da shi,
Bayan sun zauna saman carpet inda ke palour ta suka aza wani towel inda zasu aza abinci sannan suka fara cin abincin su a tare cikin filet daya, a zuciyar Habib tausayi fal ran shi , yana cewa inshah Allah in ya samu kudi bayan aure sai ya sai mata kujeru tinda yasan basuda hali,
ВЫ ЧИТАЕТЕ
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
Любовные романыSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...