Part 40

510 30 11
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:Northern_life_stories.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭





4️⃣1️⃣-4️⃣2️⃣
........Washegari da safe Lameen ya kira Mummy Video call,da kanta ta kaiwa Amnan da ke d'akin su suna ta shirya books dinsu don sauran kwana biyu su koma makaranta.

Da murna Amnah tace "My Jaan i missed you so much." Ta qarasa da er shagwaba.

Dariya yayi yace "I missed you My Cutie Jaan."

Immileey dake gefe saida taji qirjin ta ya buga saboda jin muryar sa don haka da sauri ta miqe da litattafan nata ta fice daga d'akin ta bar mata Baby Eve da keta wasa da takarda a gefen ta.

"How are you?"

Ya tambaye ta ganin kamar hankalin ta yayi wani wajen.

Da sauri tace "Am good and you?ya studies?"

Dariya yayi yace "Alhamdulillahi baku koma school ba ko?"

Ta jinjina kai tana shafa kan Baby Eve tace "Eh bamu koma ba sai jibi."

"Ina Jannah fa?"

"Tana qasa inajin." Ta bashi amsa.

"Yayi kyau a dage a maida hankali ayi karatu yanda na sanki dai kinji ko?"

Ta jinjina kai tana murmushi tace "Baka tambayi Immileey ba?"

Kafin yayi magana su Sighn suka shigo dakin da hayaniyar su,Ria ta matso tana cewa "Wow is that your sister?she is cute."

Sighn da Abdulraheem suka zauna can bayan sa basa iya hango Amnah amma ita na ganin su tayi dariya tana waving Ria tace "Hi."

Cike da jin dad'i Rian tace zauna tana cewa "Hi beautiful how are you?"

"Am good,how are you?" Amnah ta amsa tana dariya.

"Am good too,you are beautiful."

Tana dariya tare da d'an rufe fuskar ta tace "Thank you."

Itama dariya tayi tace "Okay you are welcome,Bye."

Amnah ta daga kai tare da fad'in "Bye."

Ta matsa ta koma wajen su Sighn shi kuma ya cigaba da wayar da ita.

Hira sosai sukayi sun dade sannan yace ta bashi Jannah itama suka d'an taba hira sannan sukayi sallama suka kashe.

Kamar hadin baki tana kashewa Immileey ta dawo d'akin,ta kalle ta tana murmushi tace "Naga ina fara waya kika gudu,ya akayi kuma kika san na gama ko labe kikayi ne?" Ta qarasa da son zolayar ta.

Dariya Immileey tayi tace "Amnah ina ruwana da wayar ki,kawai dai na danyi abune a qasa shiyasa amma ba wayar ce ta sa na fita ba." Ta qarasa tana ajiye kayan hannun ta sannan ta d'auki Baby Eve da ta rarrafo ta riqe qafar ta.

Jannah tace "Don gulma idan daga mu sai ke ne sai kiyi ta daukar ta amma idan da manya sai ki ta nuna wai kunya kike ji zan fara tona miki asiri Allah."

Dariya tayi tana gyarawa Baby Eve din sarqar wuyar ta er qarama ta azurfa wadda asalin ya Turajo ne ya siya ya ajiye tare da awarwaro da en kunnaye yace idan mace aka haifa zai saka mata shida kansa in namiji ne kuma zai haqura har sai an haifi macen,wannan zuwan da sukayi taga sarqar a kayanta da aka debo daga gidan su Turajon shine ta saka mata.

Jin batayi magana ta yasa Jannan ta sake cewa "Ya naji ana zancen ku da Hamma Mooha wai yaushe ma cinikin ya fada ne?"

Mooha dake tahowa ya tsaya cak jin Jannah na ambaton sunan sa,Immileey yaji tace "Ji min yarinyar nan sanda zai fada sai an gaya miki,ko an gaya miki mu d'in yara ne da zamu zauna announcement kowa sai yaji?"

Dariya su Amnah sukayi,yaji Amnahn tace "Ah ashe haka Hammana ya samu waje a zuciyar ki baki taba koda nuna mana ba?"

Dariya ta sake yi tace "Hmm waje kawai kika bashi?ni zuciyar duka na bashi don kiji."

Hab'a ya kama yana dariya qasa qasa,duk da zancen yayi kama da yarinta yarinta amma yayi masa mugun dadi.

Tana shirin sake magana ta yi gum,Amnah tace "Cigaba naga kamar magana zaki."

Da hannu tai maka alama da hancin ta alamun qamshi,Jannah tace "Ni tun dazu nake jin qamshin turaren nan amma ai kamar wajen Mummy ya wuce."

Jin haka ya sashi yi kamar daga wajen Mummyn yake Immileey data kasa nutsuwa ta taso da Baby Eve a hannun ta ta bude qofar shima ya kama handle din da niyyar budewa sukayi kacibis.

Da sauri tayi baya tana cewa "Subhanallahi bansan kana wajen ba yi haquri."

Dariya yayi yace "Bani ita." Ya miqa hannu ya karbe ta tana ta zillo da murnan ganinsa ya juya yana cewa zo kiji mana.

Juyowa tayi tana kallon su Jannah,suka yi mata dariya tace tana tab'e fuska kamar zata sa kuka "Don Allah Sis Jay kizo ki raka ni."

Zaro ido tayi tana cewa "Wa ni?noo bazan je ba kije kawai."

Marairaicewa tayi ta maida kallon ta kan Amnah kafin tai magana Amnan ta riga ta "Karma kice ni don kinsan bazan je ba."

Ba yanda zatayi ta ware mayafin doguwar rigar dake jikin ta ta yafa tabi bayan sa.

Yana harabar gidan saman wata kujera da aka gina ta siminti anyi mata rumfa,ta qarasa da sallama sai kuma ta tsaya tana kallon su,ya dago daga yiwa Baby Eve wasa yace "Ki zauna mana dogara."

Kauda kai tayi tana murmushi tace "Kai Hammah."

Shima dariyar yayi yace "Eh mana in ba dogarawa ba ko sojoji wake tsayawa a tsaye."

Bata kula shiba ta zauna nesa dasu tana kallon yanda Baby Eve ke qyalqyala dariya sosai da alama tana jin dadin wasan da yake mata ba kadan ba don koya ya dakata sai ita ta fara tsokanar sa tana jan rigarsa da gemun sa.

Murmushi tayi ta kauda kanta tana tuna Turajo,duk da dan fari ne yasha cin wannan burin akan bazai ji kunyar yin wasa da dan sa ba ko a gaban Yafendo ne don bai ga amfanin qin dan fari ba da akeyi sai ma illolin sa.

Takan yi dariya duk sanda ya fara tace "Ace maka mara kunya ai."

Shi kuma yakan maido mata da "Ba kaina farau ba kuma kaina qarau ba."





#ZahraArkel ce!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now