🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
🌴🌳 *OUM-DEEDAT*🌳🌴
🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞🌞
_Na_
_Amina Hassan_
_Oum-Deedat__Dedicated to_
_Hauwa'u Hassan_*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, ba labari na bane, haka kuma ba na wani bane, idan yaci karo da labarin wani yayi haƙuri, ajizanci ne irin na ɗan Adam. Sannan ban yarda a juya man labari ba, ta kowacce irin siga. Ngd*
*Pg 1*
♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️
Cikin takun tafiyar da kai tsaye zamu iya kiran ta da sassarfa, fuskar ta ɗauke da maɗaukakin murmushi take nufar motar da ta goga parking cikin harabar gidan.
"You are higly welcome dear" Ta furta, daidai lokacin da take rungumo shi zuwa cikin jikin ta.
Faɗaɗa murmushin shi yayi, cikin farin ciki, wanda ya kasa ɓoyuwa a saman ƴar kyakkyawar fuskar tashi, da zamu iya kiran shi kai tsaye kadaran kadahan.
Ɗan rungumar ta yayi shima yana faɗin "I really missed you Ummu na" sosai ta ƙanƙame shi cikin jikin nata. Idan ba ɓata tayi ba, tsawon shekaru uku kenan bata sanya ɗan gudalin ɗan nata a idanun ta ba. Ta sha mita wajen mahaifin shi, a cewar shi, ita ce ta hana shi dawowa. Wanda ita kuma tayi hakan ne domin ya tsaida hankalin shi waje guda, domin ganin ya samu nasarar kammala course ɗin da yaje yi ɗin.
"Good day Momma" Taji an furta daga bayan ta, cikin ɗan sauri ta waiga, jin sautin muryar mace na tashi, wacece ita ɗin kuma? Daga ina har ta shigo basu ganta ba? Kodayake, idanun su sun rufe ga murnan ganin juna ita da yaron nata.
Sakin fuskarta ta sake yi, wanda ko dama cen ita ɗin ba mai zafi bace sosai, a koda yaushe fuskar tata, ƙunshe take da fara'a mabayyaniya.
"Hey, how are you doing?" itama ta mayar mata, cikin salon maganar ta, wanda daga ji zaka san hutu da boko sun ratsa ta.
Saidai kallon da take mata, wanda yake cike da ma'anoni tambayoyi, na daga ina take? Ita ɗin wacece?
Hannun shi ya sanya duka, yana mai jawo ta zuwa ga jikin nashi, bata wani yi musu ba, ta kai kanta zuwa gareshi, tana mai sake ƙwaƙume shi sosai.
Cikin ɗan mamaki Ummun tashi ta shiga binshi da kallo, bata fahimci me ke shirin faruwa ba? To dama a tare suke ne? Daga mota guda suka fito kenan?
Bata kai ƙarshe a tambayoyin da zuciyar tata ke jera mata ba, taji sautin muryar shi, cikin wata irin kasala yana cewa; "Ummu na, Najma kenan, my fiance, and my future wife"
"Najmmmaaa" Ta amshe zancen bakin shi, cikin rawar muryar da bata ma san tayi ba. What? Ahmad Deedat ɗinta ne ya koma haka? When? As how?
"Yes Ummu na, and tare muka zo, zata ɗan yi mana hutu ne nan gidan, kafin ta wuce Abuja" Ya kuma furtawa kanshi tsaye, cikin son tabbatarwa, ba tare kuma da ya ga aibin hakan ba.
Ɗan baya kaɗan taja, cikin taku biyu, ba tare da tace mashi komai ba. Da hannu tayi ma mai gadin gidan nasu da yake tsaye gefe, alamun ya kwaso kayan Deedat ɗin zuwa ciki, wanda ya riga ya sauko da manyan luggage ɗin zuwa saman shimfiɗaɗɗen interlock ɗin dake gidan.
Bata kuma cewa komai ba, ta juya cikin takun ta mai cike da natsuwa, tana nufar plat ɗin gidan, wanda ya ƙawatu da manyan furanni da flowers masu ƙamshin daɗi.
Shima bai fahimci komai ba, daga wajen Ummun tashi, saidai yanda tayi ɗin ya bashi mamaki, sanin kanshi ne cewa duk abunda yazo ma Ummun shi dashi, ita ce ta farkon mai goya mashi baya, kafin ma Mahaifin nashi yaji.