EPISODE 5

100 3 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

🌐 *RASHIN SIRRU*
            (Sharrin Abokai)

Alk'alamin
          JANNAH JAY
Wattpad  @jannahjay8

Marubuciyar
A dalilin su
Faccala tace
Kuduri ko Manufa
Namijin Kishi

Shafi na Biyar

Gaba d'aya ta shagala da wayar da take da 'yan gidansu " Umma     anya zan iya kaiwa wata uku ban ganki ba?" Umma tace " Zaki iya fiye da haka ma Zainab, banda abinki ku matan yanzu ai kunyi sa'a don ana barin ku fita da wuri, mu a zamanin mu ai sai ayi shekara wata bata je gidansu ba sai dai in mutuwa ce ta faru ko tsananin jinya" Zee tace " Gaskiya nikam bazan iya ba, gaba d'aya zaman shirun nan baya min dad'i, bana komai sai gyaran gida da girki" karb'ar wayar yayanta yayi suka gaisa sannan ya zolayeta a kan bazata zo gida kwana kusa ba har tana cuno baki tana cewa " Umma don Allah ki karb'i  wayar ni nayi fushi bazan k'ara magana dakai ba, harda wani sai nafi shekara zan zo, aikuwa  da ko bai bani dama ba zaku ganni na taho" da sallama ya shigo Falon ya zauna yana jin yanda take magana akan zuwa gida, murmushi yayi kawai lokacin ne tagama waya da 'yan gidan nasu tayi sallama da su sannan suka gaisa da  Hamza " Ga wannan d'azu Sulaiman ya k'irani yace na kawo miki" godiya ta masa sannan ta k'arba tace " Bari na kawo maka abun motsa baki" ta shige kitchen ta ajiye kifin titus ne dake tana sonshi, shikuma  Sulaiman baya gari shiyasa yace Hamza ya kawo mata, fitowa tayi hannun ta d'auke da plate me cup cake da meat pie a kai, ta ajiye sannan ta juya ta koma ta dawo da plate d'auke da cucumber juice da cup, ta ajiye masa, yaso ace ta sake komawa d'auko wani abun don ya sake kalleta, shi dai baisan meyasa baya gajiya da k'are mata kallo, bai bar gidan ba sai da ya d'auki kimanin awa biyu yana janta da hira, don sai da ya k'ira Sulaiman ma yake fad'a masa gashi yana masa gadin matarsa, bai bar gidan ba sai da aka fara kiran sallar Isha'i sannan ya fita, yana fita ta rufe gidan gaba d'aya sannan ta dawo tagama abunda zatayi ta kwanta.

      Ishaq yana wurin aiki wayarshi ta d'au k'ara ganin sunan matarshi akai yasa yayi gaggawar d'auka " Sweet Ish ya aiki?" yace " Lafiya lou Hayatie, ya gida? Ina fatan komai lafiya ko?" tace " Lafiya lou, dama na kirane inaso na fad'a  maka Anisa ce a kace ta k'one da ruwan zafi, shine nake so na shiga na duba ta" yace " Ayya Allah sarki, ki shiga ki dubata amma na sanki da hira karki dad'e sosai, don ina ga kafin la'asar zan shigo gida" dad'i sosai Fadila taji tace " Nagode miji na, bye" dama Already tayi wankanta kawai mayafi ta d'auka da wayarta sai Key d'inta ta d'auka ta rufo k'ofar falonta ta fito, tacewa mai gadi zata shiga mak'ota, tana shiga gidan Maman Anisa ta tarar da wasu matan mak'otan nasu sun shigo su biyu, ganin k'afar Anisa sai taji idonta ya fara tara ruwa " Allah sarki Anisa sannu" ta maida kallonta kan uwar tace " Garin ya haka kuwa? Ashe k'unar da yawa d'azu Abulkhairi ya shigo yake fad'amin" Maman Anisa tace " kinsan halin yara da karambani ina Anisa ina dafa ruwan tea, na shiga toilet zanyi wanka kawai ta jona kettle wai tana dafa shayi, ganin  kettle bata d'auka ba shine harda bud'ewa taga meye ciki shine garin hakan ta kwaro ruwan dake ciki, daman na zafi ne, kawai sai ihunta naji" Anisa da take shekara hud'u kuwa sai bacci take saboda ansha kuka an gaji kuma tasha magani, nan suka shiga hirar irin karambanin da yara suke, daga baya d'aya matar ta tashi ta tafi ya zamanto saura su uku, suka cigaba da hirarsu irin ta mata can Maman  Anisa tace " Fadila kune sabin amare, ni kuwa ko kinsan wata mai saida kayan bacci na yayi? Duk yawanci nawa sun tsufa kuma dai ina son kafin Abban Anisa ya dawo na sai wasu na ajiye saboda tarar sa" Fadila tace " Aikuwa a group d'inmu akwai me sayarwa, matsalar kince yanzu baki whatsapp da kinayi da kin gansu kala-kala, saboda zakiga a na turo abubuwa a group, komai kina iya saya online" Jalila tace " K'warai groups suna da amfani ta wannan wajan"

RASHIN SIRRU (sharrin abokai) Where stories live. Discover now