بسم الله الرحمن الرحيم🙏🏽
Assalamu alaikum wa Rahmatullah , readers ,, wannan shine littafina na biyu da fatan zamu ji dadin shi kuma mu amfana dashi , abunda nayi kuskure pls don't hesitate to correct me Ni er Adam ce kamar ku , ina kuskure... Inda nayi me kyau kuma ku yaba min ta hanyar vote da kuma comments dinku ..... Bissalam
Takuce Hibbat_ Jawad (UMMU_AMMAR)................
................
................... Iska me daɗi ne ke kadawa, kasancewar ruwan sama da aka kwana anayi, kwance take a lullube a dan qaramin bed dinta zuciyarta cikeda tunani iri iri....
Amrah! Amrah!! Amrah!!! Taji Ummynta na qira gami da qonqosa qofa.. ta amsa da Na'am Ummy gani nan zuwa , sauqowa tayi taje ta bude qofar , wata matashiyar mata na gani sanye da hijab har qasa hannunta riqe da counter ( Ummy knn) tace har an idar da sallah a masallaci Amrah baki tashi ba balle kiyi haraman yin alwala , shiru Amrah tayi kaman me tunani sai kuma tace period nakeyi Ummy, to kije ki tashi Er uwarki tayi sallahn sannan ku yi adhkar , idan kun gama ku fito ku mana break fast ku shirya ku tafi school kunsan dai 6:45Am kuke tafiya , tana kaiwa nan ta juya ta koma dakinta ...
Komawa ciki amrah tayi ta tashi Er uwarta kamar yadda Ummy ta umurta shiga Sukayi sukayi wanka sannan suka dauro alwala ita ta zauna tana adhkar qanwarta kuma tayi sallahn kana ta kwanta da niyyar komawa bacci , Ilham kita shi fa muje muyi aikin gabanmu kinsan yau monday Amrah ta fadi cike da muryarta me cike da nutsuwa kamar ko yaushe , tashi Ilham tayi tana quqquni " baki isa kiga mutun zai huta ba sai kin shiga rayuwarsa wai Ni Adda Amrah me na tare miki ne.." murmushi kawai tayi ta fita ba tare da ta tanka mata ba don tasan inta biye wa Ilham ita bata gajiya da surutu , fara aikin tayi ba ta jirata ta fito bah bayan kaman minti biyar ta fito suka yi aikin acikin 20 mins suka gama , Sandwich suka yi sai ruwan zafi da suka sa a flask suka tattara suka yi dakin Ummy da shi anan suka tarar da Ammar da Irfan shirye cikin Uniform din makaranta , Ammar ne ya fara gaishe su, sannan Irfan ma ya gaishesu kana ya daura da cewa kunsan 6 tayi ko kuma ko wanka bakuyi ba wlhhy zamuyi latti gwara ku ba'a dukan ku , Ajiyewa sukayi da sauri suka wuce dakinsu suka fara shirin saka Uniform dinsu Farin rigane sai navy blue din trousers, da kuma farin hijab , acikin minti qalilan suka gama shirin su suka ɗauki school bag dinsu suka wuce dakin mama.. .
sun tarar da babansu da kuma Ummy azaune gaishe su sukayi kafin kowa ya nemi guri ya zauna suka yi breakfast ten mins alokacin 6:20Am ya buga , Miqewa sukayi .. Baba yace Ammar ya dauko key ɗin mota a daki , da sauri ya dauko kasancewar sunsan insukayi latti duka zasu sha inka cire AMRAH DA ILHAM da suke Prefect Amrah itace Health prefect tana SS3 Ilham kuma itace Acting Head girl tana SS2 ....Fitowa sukayi Baba ya kaisu school kasan cewar Makarantar ba wani nisa da gidansu da qafa ma zaka iya zuwa acikin 5 minutes suka isa abakin gate baba ya ajiyesu tare da miqa ma Amrah #500 ku ɗauki dari da hamsin ke da Ilham kubawa Ammar 100 Irfan ma 100 godiya sukayi Dukansu suka fice daga motar suna daga ma Baba hannu ...
Alhamdulillah..!!! Ammar da Irfan suka faɗa atare alokacin da suka isa harabar makarantar sukaga ba'a fara taran latti ba , dariya Ilham tayi tace kunji asara wllhy maza daku sai tsoron bulala mtssww ..!! Allah ya sauwake , shareta suka yi kowa ya wuce ajinsa .....
Amrah na shiga ajinsu ta ajiye jakanta tabi matan ajin kowa ta miqa musu hannu suka yi musabaha cike da fara'a kowa ke amsa mata ... Don ta kasance very friendly hakan yasa matan ajin qaunar ta sosai saboda duk ya halinka yake ita zakuyi zaman mutunci ..
zama tayi a seat dinta , "seatmate" naji budurwan da ke gefenta ta qirata,,, na'am sitty ❤️ , YKK? Amrah ta faɗa tare da fadada fara'ar dake fiskanta Lfy lau wacce aka qira da sitty ta faɗa cike da fara'a itama , sannan ta haɗa da cewa kinyi assignment din Mahmud kuwa , zaro ido tayi waje tare da fadin wllhy bnyi ba , sannan ta daura da cewa mu da mun gama waec Neco zamu fara next week meye hadinshi da bamu assignment Ni Allah tsarin nan bai min ba , ke dai bari seatmate qawattata ta faɗa nima baimin amma ya zamuyi , se ya kusa wucewa yanxu dai ga assignment din na miki Alhamdulillah rubutun mu iri daya ne baza'a gane ba , rungume ta Amrah tayi tace Thank u so much sitty ❤️ , U r wlcm sitty tace .. ta ciro assignment din ta miqa mata ajaka ta saka .... sannan tayi shiru ta faɗa nazarin abinda ke damunta tun jiya ....
Ya zamuyi sitty..😔 ta faɗa da murya me nuna tana cikin damuwa ...
KARBAN QADDARA zamuyi seatmate karki damu Ni wllhy na cire komai araina komai kika gani ya faru haka Allah yaso...Kuma Allah baya daura wa wani rai abunda bazata iya dauka ba ...
Shiru suka yi sakamakon sallaman malamin biologynsu da sukayi............
GIDAN ALHAJI ANWAR ADEEL
ABUJA .............. Motoci ke ta fitowa da ga wani tan gamemen gate , da alamu biki ake , ko wani taro ko mutuwa...
Daga chan nesa na hango wani kyakkyawan , qaton mota, fara da tambarin Benz agaba abayan kuma an rubuta Mercedes Benz ,2019 Edition Driver ne ya gyara parking yaje ya buɗe qofar baya , Wani handsome , Fari , ga beard , ne ya fito fiskansa dauke da fara'a mutane ne dayawa suka yo inda yake fuskansu ɗauke da fara'a kowa burin shi abarshi ya qarasa
Inda yake amma jami'an tsaro sun hana ...
Wucewa ciki yayi zuciyar cike da zumudin son ganin mahaifiyar sa Yana shigowa ya sameta tsaye tana jiran shigowanshi, qarasa wa yayi cikin sassarfa ya rungumeta tare faɗin "Mommah"
I missed U so much , I missed U too my son "ADEEL" ta faɗa irinta cike tap da hawaye , No Mommah meye abun kuka ," i'm back " ya faɗa tare da samun guri ya zauna yana qarewa ko ina kallo kaman yau yafara ganin dakin komai sabone kuma mai tsada, da ɗaukar hankali fiye da tunanin me karatu , hakan yasa ya kalli mommahn sa yace Mommah komai sabone sai dai Exactly irin na Shekaru biyar da suka wuce ,,,
Shiru tayi na en second 20 sannan tace tabbass my son saboda kai ka zaɓi kayan dakin nan tun kana qarami nikuma bazan taba canza tsarin dakin nan ba muddin bakwai ka canza shi ba domin kullum tunamin yake dakai ta faɗa with a sad tune....Kamo hannunta yayi yace No more worries Mommah" let bygones be bygones" , jinjina kai tayi sannan ta kamo hannunsa don su wuce gyaran muryan da akayi ne ya sa su juyawa Daddy ne sai Qanwarsa Adeelah , wato ma mommahn ka kaɗai ka sani koh ADEEL , A'a ADEEL ya faɗa yana sosa goshinsa buɗe masa hannu yayi shima ya rungume shi ,,,, sun jima a haka kafin suka saki juna
ya juya ya kalli qanwarsa daketa ta faman cika ta na batsewa yace haba darling sis fushi ake da sweet broh kau da kai tayi gefe sai ji tayi an Daga ta sama anata juyi da ita dariya ta fara yi ba shiri sannan ya sauqe ta duk wucewa sukayi dinning suna cin abinci suna ta fara'a kowa ya kasa cewa komai saboda maganganun suna da yawa ...Bayan sun gama ci ne Daddy ya dubi ɗan nasa yace yau ka dawo qasar nan kuma mutane suna ta jiran gaisawa dakai ka daure kaje ku gaisa tunda kaga mommahn naka koh ,?? suna Hall suna jiranka , da toh ya amsa sannan ya miqe...
Yace Mommah I will be right back , tace toh son karka jima Adeelah dake gefenshi ta riqo hannunshi yaya muje tare 😣Toh dauko mayafinki murmushi tayi tashi ga daki da sauri ta dauko mayafinta suka fita atare da ka gansu kaga en uwa domin kuwa suna mugun kama ...
Binsu Mommah tayi da ido cike da qaunarsu ...........
AMRAH
....... Qarfe 1:30pm aka tashe su a makaranta suka fito don komawa gida suka tarar da Babansu ya zo daukunsu shiga sukayi suka tafi kowannensu ya gaishe da baban nasu da " ina yini Baba" lfy Lau , ya karatu ya amsa musu , Alhamdulillah suka faɗa a tare.....
Suna isa gidan ,,,, gidane dan daidai , mai dauke da part ɗaya, sai dakin su Amrah a kusa dashi sai dakinsu Ammar a ɗan gefe.. parlourn Ummy duk sukayi suka gaisheta cike da girmama wa , tambayar su tayi ya karatu suka amsa da Alhamdulillah.........
........UMMU_AMMAR
VOTE
COMMENT
AND SHAREya yan taken ne..???
Shin kunji daɗin page 1 ɗin meye ra'ayin ku akai ...??
Pls vote don inji ƙwarin gwiwan cigaba 😪😪
YOU ARE READING
★★KAR'BAN QADDARA..★★
RandomLabari ne da ya qunshi ; Soyayya😍, Yarda🤗, Friendship, Haquri , da kuma uwa uba KARBAN QADDARA a yanda tazo .. Hope we will all Enjoy it 😊