Washegari da safe jallal ya shirya bayan ya karya yaje dakin kakarsa “ ina kwana kaka”
kakarsa wanda ke kwance kan gado da alama tashiwanta kenan tace “ ka tashi lafia jallal”
“lafia lau kaka zan tafi wajen aiki, ina Noor take ne” kaka tace “yanxu ta shiga wanka, ka
karya ko” “eh kaka yanzu na sha tea” murmushi tayi tace “toh Allah bada saa Allah maka Albarka” Ameen yace sannan ya tashi ya fita kenan daidai lokacin noor ta fito dagawanka tace “ina kwana yaya” “lau baki tafi makaranta ba ” tace "eh yanzu zan shirya na
tafi muna ma da test"“ok Allah bada saa”
Mashin dinsa ya dauko yai hanyar office dinsa jidda ne ya tuno wayarsa ya ciro yayi dialing
numberta ringing biu yayi ta amsada “ Assalamu Alaikum” ta bangarensa yace “ wa alaikumul salam kin tashi lafia” sai wani“lafia lau ka tafi wajen aiki ne”
“ yanzu haka ina hanya nace yakamata na kiraki”
murmushi tayi“toh nagode yanzu ma na tashi daga bacci” “ok I will call you later” sannan yayi hang up
Jidda bayan ta gama waya da jallal sai wani murmushi takeyi azumi mai aikinsu ta shigo “ina
kwana Anty jidda”“lafia lau” ta amsadashi cikin far'anta “daman hajia ce tace in kiraki wai ki sauko kiyi breakfast”
“ok ina zuwa bari nayi wanka” a hankali ta fita tana mamakin yau jidda ta amsa gaisuwarta ba fada
Tashi jidda tayi ta shiga toilet tayi wanka saida ta dade a toilet tana wanka bayan ta fito tayi shafe
shafenta wardrobe dinta ta nufa wanda ke cike da kayayaki wani hollandis ta ciro mai tsadawanda yasha dinki ta saka tayi daurin turban batayi heavy makeup ba powder ta shafa da lip balm sannan tayi hanya parlour
Data sauka parlour hanyar dinning tayi wanda mum dinta already tana cin breakfast dinta
“ Good morning mum” mum wanda ke shirin kai irish bakinta tace “ morning my
daughter what took you so long haka tun dazu nasa azumi ta kiraki” zama tayi kujerar dakefacing mum cikin shagwabar murya tace “mum wanka fa nayi kema kinsani idan ina wanka ina
dadewa” girgiza kai mum tayi tace “jidda kenan kin fiya shagwaba oya ci abincin ki”Plate dinda aka rufe abincinta ta cire fork ta caka ta fara cin irish din mum ce tayi Magana
“jidda munyi waya da babanki yace zai shigo yau kuma ya tambayeni kan maganar haidar kuma na fada masa kunyi Magana” aje fork din tayi tace “why mum meyasa kika fada masa haka”
mum tace “bangane meyasa na fada masa ba karya kikeson na mashi toh, bari ma na tambayeki
bakison kiyi aure ne ko kuwa akwai wanda kikeso dakike wulakanta haidar” iska ta fuzar“mum bawai haka ba ni bai mun ba kuma kinga yanda yake kallon mutum ne am embarrassed jiya”
“ wannan kuma ke kika sani in babanki yadawo kwayi Magana”
“mum!” ta fada gabadaya abincin ya fita ranta.
Tashi tayi ta nufi dakinta girgiza kai mum tayi ‘yarinyar nan”
Bayan jallal yakai office ya gaida staffs din wajen sannan ya zauna a mazauninsa ya fara ayukansa
daya kamata sabon manager su ya shigo wato haidar suka gaida shi sannan kowa ya cigaba da
aikinsaLandline dinda ke kusada jallal yayi ringing yayi picking hello sir Wanda aka kirada hello sir yace
"kawomun green file dinnan" "ok sir" tashi yayi ya dauki file din yaje office din knocking yayi akace come in ya tadda sa yana magana a waya shidai jiyayi ance eh munyi magana da ita saida
jallal ya tsaya har ya gama waya sannan ya mika masa file din "thank you"
Juyawa yayi zai tafi haidar yace "ya sunanka" jallal yadanyi murmushi "sunana jallal sir"
"OK jallal thank you" juyawa yayi ya fita yana tunanin meyasa manager ke tambayar sunansa.
Bayan ya koma ya zauna ya cigaba da aikinsa vibration din wayarsa yaji daman a vibration ya saka ta dubawa yayi yaga unknown number "waye wannan" picking yayi yasa a Lynne
"Assalamu Alaikum" ta dayan bangaren aka amsada " Wa alaikumul salam jallal" daga jin muryan yasan waye Babansa ne shiru yayi saida baban yai magana yace "jallal ya kake dazu naje gda kaka tace mun ka tafi wurin aiki daman nazo ne dan na fada maka kanwarka zatayi sauka Qur'ani sati me zuwa" cikin rashin ganewa yace
"ai noor ta riga ta sauka" murmushi yayi yace "ow ban fada maka cewan inada wata 'ya ba ko itace ce zatayi sauka kuma anan garin Abuja zaayi ina fatan
zakazo" a ranshi ya fada lokacin da su sukayi sauka ko ganinsa basuyi shine zaizo yana fada masa wani saukar 'yar samaganar baban ne ya dawo dashi daga tunani "jallal kana jina kuwa" "Allah kaimu kawai yace"
sannan sukayi sallama bayan ya tashi daga office ya tafi gda yaje massalaci yayi sallah sannan ya je dakin kakarsa a
zaune ya ganta ita da noor yace "noor harkin dawo" "eh yaya" zama yayi kan tabarma kaka tace"noor dauko masa abincinsa" tashi tayi kaka tace "jallal dazu babanka yazo" jallal kansa a kasa yace "ya kirani a waya" ido kaka ta zaro "ya fada mun wai yarsa zatayi sauka nasan zakayi tunanin bazaka ba amma baidace ba komi lokaci ne" saida kaka tayi convincing dinsa har ya yarda zashi
daidai lokacin noor ta shigo da abincin sa jollof rice ce cokaci ya dauka ya fara ci cikin natsuwa
jidda na zaune a parlour tana chatting da maryam tana fada mata cewan sun shirya da jallal horn din mota taji tasan dad dinta ne tashi tayi ta tafi dakinta
bayan driver yayi parking dad ya fita ya shigo parlour ba kowa mum ce ta sauko daga stairs taci
kwalliya tace "sannu da zuwa ya gajiyan hanya" zama yayi kan kujera yace "gajiya akwai shi"
mai aiki ne ta dauko drink me sanyi da cooler abinci kala kala da aka girka bayan yaci ya koshi
yace "ina jidda ne" mum tace "tana daki" kwada ma azumi kira tayi da sauri ta zo "naam hajia"
"jeki kira jidda kice babanta na kira"
dakin jidda taje tayi sallama ta shiga "Anty Alhaji wai kije" ido ta zaro tace tohm ina zuwa gabanta ne ke faduwa tashi tayi ta tafi parlour
ganinsu tayi zaune iyayenta suna hira karasawa tayi ta gaida dad dinta yace "jidda kinji na dawo
amma bakizo kinmun sannu da zuwa ba" murmushi tayi tace "ina toilet ne shiyasa" sun zaune sunsha hira irinta family
all of a sudden dad yace "yawwa jidda kun sasanta da haidar ko" kaita fara sosawa "eh dad amma...." "amma me?"
"dad baimun bane" juyowa dad yayi rai bace
"ban gane bai maki ba daman abinda zan zaba maki sai ya maki, babansa abokina ne sosai kuma idan na hada ku yanzu
company na zaiyi benefiting sosai""kallon dad tayi idonta sun fara cika da kwalla tace dad bangane ba kana nufin akan business zaka hadamu that's not fare dad akwai wanda nakeso" bata San sanda bakinta Ya fadi last statement din ba.
kara kallonta yayi yace "koma waye you better remove him from your heart because bazan canza maganata ba juyawa yayi ya wuce
wani kuka ta saki tace "mum Kinyi shiru kima dad magana inada wanda nakeso" mum ta shiga lalashinta "wani guy ne haka kike maganar a kansa kiyi shiru i will talk to your dad"
"please mum kiyi masa magana" ta fada cikin kuka
"toh share hawayenki ki fada mun waye wannan guy din a ina kuka hadu "
"sunansa jallal a office din mu yake aiki" mum tace "
"To, da wuya dad dinki but zanyi trying karki damu jeki kwanta duk yadda mukayi da shi i will let you know " rugumar mum tayi "i love you mum" sannan ta tafi dakinta
YOU ARE READING
Jidda Da Jallal
RomanceJidda 'yar shekara 25, wacce ta fito daga gidan masu kudi. Abinda takeso shi takeyi ba'a mata abu ta kyale. Me zai faru da babanta ya sata a matsayin manager a company shi kuma tayi crossing part da Jallal, Daya daga cikin ma'aikatan company wanda b...